Mece ce alaƙar takin zamani da farashin kayan abinci?

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da farashin kayan abinci ya karye sannan kuma gwamnatin Najeriya take ƙara karya farashin domin sauƙaƙawa 'yan ƙasa, manoma da masana ke ta nuna damuwa dangane da yadda farashin abincin ke faɗuwa amma kuma a gefe guda farashin takin zamani ke ƙara hauhawa.
A ranar Litinin ne Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya ta fitar da alƙaluma da suka nuna farashin kayan abinci ya faɗo da kaso 1.76 cikin ɗari daga watan Yuli zuwa Agusta, al'amarin da masu saye suka tabbatar.
Yayin da wasu ke murnar ci gaba da saukar farashin abincin, wasu kuwa musamman manoma da masana na cewa al'amarin ba zai yi kyau ba a nan gaba, bisa la'akari da hauhawar farashin takin zamani.
To, ko mece ce alaƙar takin zamani da farashin kayan abinci?
Domin samun wannan amsar ne BBC Hausa ta tuntuɓi Alhaji Lawal Garba Kurfi, masani kan harkar noma kuma shugaban manoman masara na ƙasa a jihar Katsina.
Alaƙar takin zamani da farashin abinci

Asalin hoton, Getty Images
"Idan farashin takin zamani ya tashi, kuma manomi ya yi amfani da shi wajen noma, farashin kayan abinci zai tashi. Idan kuwa farashin takin zamani ya yi rahusa, manomi zai iya yin noma cikin sauƙi kuma ya sayar a farashi mai sauƙi, har ya samu riba." In ji Alhaji Lawal Garba Kurfi, masani kan harkar noma kuma shugaban manoman masara na ƙasa a jihar Katsina.
Sai dai a halin yanzu, ya ce; "amma a halin da muke ciki, takin zamani na tsada kuma farashin kayan abinci na ƙasa, toh a wannan yananin ne manomi ke noma kuma ba ya samun riba."
Bisa binciken da BBC ta yi, farashin takin zamani ya ɗaga naira 30,000 zuwa har kusan naira 60,000 ya danganci wane irin takin ne mutum zai siya.
Shin dole ne a yi noma da takin zamani?

Asalin hoton, Getty Images
Masanin ya ce "ba dole ba ne sai da takin zamani za a iya yin noma, domin akwai hanyoyi na gargajiya da ake iya amfani da su. Misali, a da, iyayenmu sun yi amfani da takin dabbobi da na kwatoci da juji wajen yin noma, kuma sun samu amfanin gona mai kyau." in ji shi.
Amma ya ƙara da cewa, a yanzu saboda yawan buƙatun abinci, musamman ga manyan manoma masu noma hectoci da yawa, ya zama dole a yi amfani da takin zamanin.
Dangane kuma da abubuwan da ake nomawa ba tare da takin zamani ba, Alhaji Kurfi ya ce tabbas, akwai wasu kayan abinci da ake nomawa ba tare da taki ba musamman gonakin da ke da ƙwari sosai.
"Muddin idan wurin na da ƙwari, za a iya noma kayan abincin kamar su dawa da gero da dauro da wake da kuma gyaɗa ba tare da amfani da taki ba.
Kuma idan aka noma su ba takin, za a iya samun inganci da amfanin gona da ɗan yawa." in ji shi.
Yaushe aka fara amfani da takin zamani?

Alhaji Kurfi ya ce an fara amfani da takin zamani a Arewacin Najeriya ne kusan shekaru 50 da suka wuce lokacin da Bankin Duniya ya buɗe ADP ta Funtua a shekarar 1975.
"A wannan lokacin ne manoma suka karɓi amfani da takin zamani kusan ko'ina a faɗin wasu jihohin Arewa." in ji shi.
Muryoyin manoma daga jihohi daban-daban

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
BBC ta kuma tuntuɓi manoma daga jihohi daban-daban domin jin ta bakinsu.
Malam Usman Adamu, manomin shinkafa ne daga Kano kuma ya ce;
"Ni ina noma a yankin Kura, kuma shinkafa ce babbar sana'ata. A da buhun taki ana siya a kan naira 5,000 zuwa N7,000. Yanzu kuwa sama da N45,000 ake siya." in ji shi.
Malam Usman ya ƙara da cewa ba ya iya sayen takin da yawa saboda tsada wadda hakan ke saka abin da nake nomawa ba sa fitowa da ywa kamar da ba.
"Wannan matsalar ta sa duk da cewa farashin abinci yana sauka yanzu, nan gaba shinkafa za ta ƙara tsada saboda mu manoma ba za mu iya girbar shinkafar da yawa ba."
Wata manomiyar masara da wake daga jihar Benue, Esther ta shaida wa BBC cewa a yankinsu yawancin mata sun fi noma masara da wake amma matsalar tsadar taki tana hana su girbar amfanin gona da yawa.
"Idan muka samu taki da sauƙi ko arha, za mu iya ciyar da Najeriya baki ɗaya. Amma yanzu ko da gwamnati ta ce a karya farashin abinci, mu a gonaki muna fuskantar ƙalubale saboda kayan da muke amfani da su sun yi tsada." in ji Esther.
Shi ma Bulama Goni, manomi daga Borno da ke noman dawa da alkama ya ce matsalar tsaro da tsadar taki su ne manyan matsalolinsu
"Sau da yawa sai mun je cikin Maiduguri kafin mu samo taki, kuma kudinsa ya ninka zuwa naira 47,000 abin da muke siya a da kan naira 12,000."
Idan gwamnati ba ta kawo mana sauƙi ba, nan gaba kayan abinci za su ƙara tsada fiye da yadda mutane suke tsammani." in ji shi.
Mece ce mafita?

Asalin hoton, Getty Images
Alhaji Lawal Garba Kurfi ya ce idan har ana son Najeriya ta zama ta samu cikakken natsuwa akan batun abinci ba tare da sai mun nemo shi daga ƙasashen waje ba , to ya kamata gwamnati ta wadatar da takin.
"A halin yanzu, kasancewar Najeriya tana da yawan mutane kuma akwai babbar buƙatuwar abinci, ya kamata gwamnati ta samar da takin zamani cikin rahusa da sauƙi ga manoma."
Ya ce idan babu takin zamani ko kuma yana da tsada, noma ba zai yi inganci ba, kuma ba za a samu abin da ake buƙata ba, a saboda haka idan an har gwamnati na son manoma su samar da abincin da ƙasar ke buƙata to dole ne ta samar da taki a farashi mai rahusa.











