Ko ƙasashen Musulmai za su iya kafa ƙawancen tsaro don tunkarar abokan gaba?

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Firaiministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani
    • Marubuci, संदीप राय
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, बीबीसी संवाददाता
  • Lokacin karatu: Minti 6

Bayan harin da Isra'ila ta kai kan jagororin Hamas a Doha, babban birnin Qatar, akwai alamun cewa wani yunƙuri tsakanin ƙasashen Larabawa na kafa ƙungiyar tsaro mai kama da NATO na ƙara samun goyon baya.

Ƙasashen sun kira wani taro na ministocin harkokin waje a birnin na Doha ranar Lahadi, sannan a ranar Litininshugabannin ƙasashen Larabawa, ciki har da na Iran Masoud Pezshkian da Firaiministan Iraq Muhammad Shia-al Sudani da da kuma shugaban hukumar mulkin Falasɗinawa Mahmoud Abbas.

Kuma a wannan lokaci shawarar da Masar ta bayar ta kafa dakarun hadin gwiwa ta haifar da muhawara.

Jaridar 'The National' ta ce Masar ta bayar da shawarar kafa wani ƙawancen tsaro mai kama da NATO, wanda za a riƙa karɓa-karɓar jagorancinsa tsakanin ƙasashen Larabawa 22, inda Masar ɗin za ta zama ta farko.

Kafar yaɗa labarai ta 'The New Arab Media' ta ce an fara bijiro da wannan shawara ce a shekara ta 2015 lokacin da yaƙin basasa ya ɓarke tsakanin dakarun Yemen da ƴan tawayen Houthi, waɗanda suka karɓe iko da birnin Sanaa.

A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra'ila ta kai a birnin Doha.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargadin cewa "Isra'ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Qatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala'i."

Mece ce shawarar da Masar ta bayar?

A ranar 9 ga watan Satumba ne Isra'ila ta kai hari kan wannan gini da ke birnin Doha na ƙasar Qatar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar 9 ga watan Satumba ne Isra'ila ta kai hari kan wannan gini da ke birnin Doha na ƙasar Qatar

Shawarar da Masar ta bayar ya ƙunshi samar da tsarin hade ayyukan sojin ƙasa da na sama da cibiyoyin tsaro, tare da haɗe cibiyoyin horaswa da ayyukan soji.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Haka nan kuma ƙasashen ne za su yanke hukunci kafin amfani da dakarun bayan tattaunawa a tsakaninsu.

Kafar yaɗa labarai ta Al Akhbar da ke Lebanon ta ce a ƙarƙashin tsarin, Masar ta ce za ta samar da dakaru 20,000, sannan Saudiyya za ta zamo ta biyu mafi bayar da gudumawa.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya tattauna da ƙasashe da dama a kan wannan batu, kuma akwai yiwuwar harin da Isra'ila ta kai a Doha zai iya farfaɗo da maganar.

An taɓa samun irin wannan ƙawance a lokuta daban-daban tsakanin ƙasashen yankin, kamar a lokacin yaƙin yankin Gulf da kuma yaƙe-yaƙen da aka yi a Isra'ila.

An taba kulla irin wannan kawancen tsaro a baya tsakanin kasashen Larabawa da na Musulmai - wadda ake kira Central Treaty Organisation, wadda aka yi wa lakabi da Yarjejeniyar Baghdad. Yarjejeniyar ta yi aiki daga shekara ta 1955 zuwa 1979.

Kasashen Larabawa sun yi mummunar suka kan harin da Isra’ila ta kai a Qatar

Firaiministan Iraqi Mohammed Shia al-Sudani ya kuma yi kira da a samu ‘kawancen soji na kasashen Musulmai’.

Kafar yada labarai ta Turkiyya, TRT World, ta ambato shi na cewa akwai bukatar daukar mataki na bai-daya kan abubuwan da Isra’ila ta aikata a Gaza da kuma Qatar a baya-bayan nan.

Al-Sudani ya ce harin da Isra’ila ta kai a Doha, wanda ya kashe mambobin Hamas biyar da wani babban jami’in tsaron Qatar “taka dokokin duniya ne mai matukar mamaki” kuma tunatarwa ce kan cewa abubuwan da Isra’ila ke aikatawa barazana ce ga tsaron daukacin yankin.

”Babu wani dalili da zai hana kasashen Musulmai hada kai domin samar da kawancen soji guda daya domin kare kansu,” kamar yadda ya shaida wa tashar talabijin ta Al Jazeera, inda ya bukaci kasashen Larabawa da na Musulmai su samar da hadaka ta siyasa da tsaro da kuma tattalin arziki.

Ya kamata a hukunta Isra’ila - in ji Qatar

Ministan harkokin waje na Iran Abbas Araghchi ya gana da Firaiministan Qatar gabanin taron

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ministan harkokin waje na Iran Abbas Araghchi ya gana da Firaiministan Qatar gabanin taron

“Lokaci ya yi da duniya za ta kawo karshen baki biyu da ake yi sannan a hukunta Isra’ila kan laifukan da ta tafka,” in ji ministan harkokin waje na Qatar, gabanin taron da kasashen suka yi a ranar Litinin, kamar yadda sashen BBC Persia ya ruwaito.

Ya ce “Ya kamata Isra’ila ta sani cewa wannan yaki da take da ‘yan’uwanmu, Falasdinawa, da nufin korar su daga kasarsu, ba zai yi nasara ba.”

Qatar ta yi martani da kakkausan harshe bayan harin da Isra’ila ta kai mata ranar 9 ga watan Satumba, kuma ta jaddada cewa yanzu a shirye take kan ko ma mene ne zai faru.

Daya daga cikin manyan jami’an Hamas, Bassem Naim, ya ce kungiyar na fatan cewa za a samu “wani kwakkwaran mataki na bai-daya daga kasashen Larabawa da na Musulmai” kan Isra’ila.

Amurka na da sansanin sojin samanta mafi girma a fadin Gabas ta tsakiya ne a Qatar. Baya ga haka, Qatar ta taka muhimmiyar rawa wajen tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Masar da kuma Isra’ila da Hamas.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio wanda ya kai ziyara Isra’ila, ya nuna fushinsa kan harin da Isra’ila ta kai a Qatar, sai dai ya bayyana cewa wannan ba zai lalata kyakkyawar alakar da ke tsakanin Amurka da Isra’ila ba.

Dama dai akwai rudani kan abin da mai magana da yawun fadar shugaban Amurka ta White House, Caroline Levitt ta ce game da bayanin da aka yi wa Qatar kan harin. Fadar White House ta ce ‘an sanar da Qatar kafin kai harin’, sai dai Firaiminstan Qatar ya ce ya ‘samu bayanin ne minti 10 bayan kai harin’.

Shin abu ne mai yiwuwa kasashen Larabawa su kafa kawance kamar NATO?

Saudiyya tana jagorantar rundunar yaki da tsattsauran ra’ayin addini

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Saudiyya tana jagorantar rundunar yaki da tsattsauran ra’ayin addini

Batun kafa kawancen soji tsakanin kasashen Larabawa, mai kama da kawancen NATO, abu ne da ya dade, sai dai masana ba su da kwarin gwiwar cewa abu ne da zai yiwu.

Premanand Mishra, malami a cibiyar zaman lafiya da warware rikice-rikice ta Nelson Mandela a jami’ar Jamia Millia Islamia da ke Indiya, ya ce “An tana tattaunawa kan kafa kungiyar NATOn Larabawa, kuma Saudiyya ta bai wa batun muhimmanci sosai. Har ma an taba nada tsohon babban hafsan soji na Pakistan, Raheel Sharif a matsayin shugabanta. To amma sai batun ya gaza ci gaba.”

Ya ce “Muradun tsaro na dukkanin kasashen sun sha bamban ta yadda zai yi wahala a samu matsaya daya a tsakaninsu. Misali, Saudiyya da Iran za su iya watsi da bambance-bambancen da ke tsakaninsu? Domin idan har za a yi hadakar soji, to akwai bukatar yin musayar bayanan sirri.”

Duk da cewa akwai kokarin da aka yi a baya-bayan man na sulhuntawa tsakanin Saudiyya da Iran, babu tabbas kan ko an cimma wata matsaya mai kwari da za ta ita samar da kawance tsakanin kasashen yankin.

Premanand Mishra ya ce wannan shawara ta kawancen soji ta samo asali ne daga Masar, abin da ya rage shi ne a ga ko akwai kwakkwarar aniyar aiwatarwa. Sannan kuma ko kasashen Yamma, musamman Amurka da kawancenta na NATO za su bari a aiwatar da shawarar”

Ya ce tabbas akwai batun kafa NATOn Larabawa a baya, kuma za a ci gaba da samu irin wannan batu a nan gaba, amma akwai shakku kan ko za a iya aiwatarwa.

Dr Mudassir Qamar, karamin farfesa a Cibiyar nazarin yankin yammacin Asia a jami’ar Jawaharlal Nehru da ke birnin Delhi na Indiya, ya ce kasashen Larabawa na da kungiyoyi da dama da suka hadu a ciki, kamar kungiyar Arab League, da OIC da kuma GCC.

Bayan haka akwai dakarun yaki da ta’addanci da ke karkashin jagorancin Saudiyya, to amma matsalar ita ce yadda za a warware matsalolin da ke tsakanin kasashen na Larabawa.

Mudassir Qamar ya ce “zai yi matukar wahala Isra’ila - wadda yanzu ba ta shiri da kasashen Larabawa da dama - ta kawar da kai daga duk wani yunkuri na samar da irin wannan kawance.”