Abin da ya sa aka gaza warware rikicin Dangote da ƙungiyar NUPENG

Wasu motocin Dangote a matatarsa

Asalin hoton, Dangote

Lokacin karatu: Minti 6

Matatar mai ta Dangote ta sanar da cewa a ranar Litinin ne za ta fara rarraba mai daga matatar zuwa gidajen mai da ke faɗin Najeriya.

Dangoten ya yi alƙawarin sayo manyan motocin dakon mai masu amfani da CNG, kusan 10,000, inda ya zuwa yanzu ya sayo 4,000 daga ciki, inda ya yi alƙawarin ɗaukar man daga matatarsa zuwa gidajen man da suka sari man nasa a kyauta.

Matakin da bai yi wa ƙungiyar masu dakon man fetur da rarraba shi - zuwa gidajen man ƙasar, ta NUPENG - daɗi ba .

NUPENG na fargabar cewa matakin na Dangote zai zame wa sana'arsu barazana.

Inda ƙungiyar ta buƙaci duka sabbin direbobin Dangoten su zama mambobinta.

Lamarin da ya sa aka riƙa kai ruwa rana tsakanin ƙungiyar da matatar Dangoten , inda har a makon da ya gabata ministan ƙwadogon Najeriya da hukumar tsaron farin kaya ta DSS suka shiga lamarin tare da cimma yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, to sai dai ba a je ko ina ba yarjejeniyar ta wargaje. Ko me ya sa haka?

Mene ne buƙatun NUPENG?

Farfesa Ahmed Adamu ƙwararren masanin harkokin tattalin arzikin man fetur a jami'ar Nile da ke Abuja ya ce buƙatun ƙungiyar sun haɗa da:

  • Duka direbobin Dangote su shiga ƙungiyar Nupeng

Farfesa Adamu ya ce babbar buƙatar ƙungiyar ta Nigeria Union of Petroleum and Natural Gas Workers (NUPENG) ita ce dirobobin Dangote su zama mambobinta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Tana so ne duk wani mai dakon man fetur ya kasance mambanta kuma mai biyayya ga umarninta'', a cewar masanin harkokin na man fetur.

  • Motocin Dangote su riƙa bin layin lodi a matatarsa

Wani abu da ƙungiyar ke so, shi ne duka motocin Dangote su riƙa bin layi a wajen lodin mai a matatar, kamar yadda kowa ke bi, kafin a loda masa.

''Su suna ganin wasu kan yi kwanaki a kan layi, kafin lodi ya zo kansu, amma motocin Dangote idan sun zo sai kawai a loda musu ba tare da sun bi dogon layin da sauran motocin dako ke bi ba'', in ji masani harkokin man fetur ɗin.

Haka kuma ya ce ƙungiyar ta nuna damuwa kan matakin da direbobin gidan mai na MRS mai alaƙa da Dangote suka ɗauka na cire tambarin (sticker) ƙungiyar NUPENG daga jikin motocinsu.

  • Yin watsi da duk wata ƙungiya mai aiki irin nata

Haka kuma wata buƙatar ta ƙungiyar ita ce kada matatar Dangote ta amince da duka wata ƙungiyar da ta zama tamkar kishiya ga NUPENG.

''Akwai ƙungiyoyin da suke aiki irin na NUPENG don haka take ganin shiga wata ƙungiyar da ba ita ba, tamkar kishiya aka yi mata'', kamar yadda Farfesa Adamu ya bayyana.

  • Samun ƙarin kuɗin shiga

Farfesa Adamu ya ce ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ƙungiyar ke son hakan shi ne samun ƙarin kuɗin shiga daga sabbin mambobin.

''Idan aka samu ƙarin mambobi, dole ne ƙungiyar ta samu ƙarin kuɗin shiga, saboda ƙaruwar mambobin,'' in ji shi.

Me matatar Dangote ke buƙata?

Wasu motocin Dangote

Asalin hoton, Dangote

A nata ɓangare matatar Dangote na ganin kanta a matsayin kamfani mai zaman kansa ba gwamnati ba, bai kamata a tilasta mata yin abubuwan da ba su zame mata dole ba.

Wasu daga cikin buƙatun matatar kamar yadda Farfesa Ahmed Adamu ya bayyana sun haɗa da:

  • Cin gashin kai

Masanin tattalin arzikin na man fetur ya ce ita matatar Dangote gani take kasuwanci take yi, kuma idan ta ga dama sai ta ƙi sayar da man a Najeriya, babu mai hana ta, don haka take ganin babu wanda zai yi mata gadara.

''Matatar na ɗaukar kanta a matsayin kamfani don haka za ta ci gashin kanta ne'', in ji shi

Ya ƙara da cewa ''Ita ƙungiyar NUPENG a baya ta saba harka da NNPCL, wadda ita kuma ta gwamnati ce don haka za su iya nuna gadara kasancewarsu ƴanƙasa suna da haƙƙi''.

  • Sayar da mai kai-tsaye ga duk mai gidan mai

Haka ma matatar Dangoten na ganin za ta iya sayar da man kai tsaye ga kowane gidan mai ba tare da shigar dillalai ko wasu ƴan tsakiya ba, da za su sa man ya ƙara tsada, kamar yadda Farfesa Adamu ya yi ƙarin haske.

''Abin da Dangote ke buƙata shi ne duk wani mai gidan mai da ke son man fetur ya yi wa matatarsa magana kai-tsaye domin sayar masa tare da kai masa shi a duk inda gidan man yake'', in ji shi.

Masanin tattalin arzikin ya kuma ce yana ganin Dangote ba ya buƙatar direbobinsa su shiga ƙungiyar NUPENG saboda matatarsa kamfani ne mai zaman kansa ba a ƙarƙashin wani suke ba.

  • Kada a ƙayyade ƙungiyar da direbobinsu za su shiga

Sannan matatar Dangoten tana ganin bai kamata a ƙayyade wata ƙungiya ɗaya tilo da direbobinta za su shiga ba.

''Kasancewa ita NUPENG a yanzu tana da kishiya, don haka direbobinta na da damar zaɓar ƙungiyar da za su shiga'', in ji Farfesa Adamu.

Ya ci gaba da cewa ''Ita Matatar Dangote na ganin cewa idan ta fara amfani da motocinta, to za ta iya samar da mai da araha, fiye da direbobin NUPENG'', in ji a Farfesa Adamu.

Me aka cimma a yarjejeniyar farko?

Wasu daga cikin wakilan da suka yi zaman

Asalin hoton, Federal Ministry of Labour/X

Bayanan hoto, Wasu daga cikin wakilan da suka yi zaman

A ranar 9 ga watan Satumba ne wakilan matatar Dangote da na ƙungiyar NUPENG da na ƙungiyar Ƙwadago ta NLC da TUC da NMDPRA da ma'aikatar Ƙwadagon ƙasar suka yi zama tare da amincewa da wasu yarjejeniyoyi da suka ƙunshi:

  • Ma'aikatan Matatar Dangote na da damar shiga ƙungiya idan suna buƙatar hakan.
  • An kuma amince cewa ma'aikatan matatar za su kammala shiga ƙungiya tsakanin 9 zuwa 22 ga watan Satumba.
  • Haramta wa ma'aikatan matatar shiga wata ƙungiyar da Dangote ke iko da ita.
  • Sannan ba za a musguna musu ba idan suka shiga yajin aiki ko suka mara wa ƙungiyar da suke ciki baya.
  • Daga ƙarshe yarjejeniyar ta buƙaci duka ɓangarorin biyu su sanar wa ministan ƙwadagon ƙasar kammala aiwatar da yarjejeniyar bayan mako guda.

Me ya janyo wargajewar yarjejeniyar?

Farfesa Adamu ya ce abin da ya janyo wargewar yarjejeniyar shi ne kwanaki bayan cimma yarjejeniyar sai NUPENG ta zargi matatar Dangote da saɓa wa abubuwan da aka cimma, musamman kan batun shiga ƙungiya.

Haka ma ƙungiyar ta zargi matatar Dangote da hannu a cire tambarin NUPENG daga motocin dakon mai na MRS mai ƙawance da matatar.

''Wannan abu bai yi wa NUPENG daɗi ba, lamarin da ya sa suka ce an karya yarjejeniyar da aka cimma a makon da ya gabata'', in ji shi.

Sai dai a wata sanarwa da Matatar Dangoten ta fitar a ranar 11 ga watan Satumba ta musanta zargin na NUPENG, musamman kan batun shiga ƙungiyar.

Matatar ta ce ta yadda ma'aikatanta na da damar shiga ƙungiya bisa raɗin kansu, amma ba tilasta musu ba, bisa dokokin Najeriya da dokokin ƙwadago na duniya.

Matatar ta kuma ce tana da kyakkyawar alaƙa da duka wata ƙungiya da ke harkar man fetur ciki har da NUPENG, tana mai iƙirarin cewa zuwanta ya taimaka wajen haɓaka kuɗaɗen shigar ƙungiyoyin.

Matatar ta kuma ce duk da cewa tana son wanzar da kyakkyawar hulɗa da kowa ta hanyar lalama, ba za ta lamunci ɓata-suna ko cin dunduniya ko tilasta mata yin abin da bai zama dole a gare ta ba da sunan ƙungiyanci.