An tashi baram-baram a taron sulhu da kungiyar NUPENG

Asalin hoton, NNPCL/X
An tashi baram-baram a wajen taron tattunawar sulhu da aka yi tsakanin kunyiyoyin kwadago na NLC da TUC da kuma wakillan kamfanin Dangote a Najeriya.
Kungiyar ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas ta NUPENG ce ta yi barazanar shiga yajin aiki sakamakon matakin da kamfanin mai na Dangote ya dauka na fara jigilar mai zuwa gidajen mai.
Ministocin kwadago na Najeriya biyu ne suka shiga tsakani domin ganin an samu warware matsalar da ta taso tsakanin bangarorin to amma kuma ba a samu galaba ba.
Kwamared Nuhu Abbayo Toro, shi ne babban magatakar na kungiyar kwadago ta TUC a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa babu wani da aka cimma a wajen taron sulhun.
Ya ce " Tun da magana ce ta hakkin ma'aikata da kamfanin Dangote ke kokarin tauyewa, mun iya bakin kokarinmu don a samu masalaha amma ba a yi galaba ba."
Kwamared Toro, ya ce" A don haka mu yanzu muna kan bakarmu ma'aikata zamu ci gaba da zaman ko ta kwana har illa masha Allahu."
"Ina so na sanar da mutane abu guda wato ba gudu ba já da baya domin akan hakkin ma'akaci guda sai yadda karfin kungiyoyin kwadago ya kare." In ji shi.
Kwamared Nuhu Abbayo Toro, ya ce,"Batun tsunduma yajin aiki a sanya ido aga abin da zai biyo baya."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga bangaren wakilan kamfanin mai na Dangote kuwa sun ce babu abin da za su ce daga nasu bangaren.
A ranar Litinin 8 ga watan Satumbar 2025, ne kungiyar ƙwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas a Najeriya, NUPENG, ta yi barazanar tsunduma yajin aiki domin adawa da matakin da matatar mai ta Ɗangote ta dauka na fara kai man fetur zuwa gidajen mai da ke fadin ƙasar.
Kungiyar ta NUPENG, ta ce muddin matatar mai ta Dangote ta fara jigilar mai zuwa gidajen man da ke jihohi, to dubban ma'aikatan da ke aiki a depo-depo da kuma direbobin da ke tuka manyan motoci sama da dubu 30, za su rasa aikinsu.
Ita ma kungiyar masu gidajen mai da isakar gasa NOGASA, ta nuna goyon bayanta a kan matakin da NUPENG din ta ce zata dauka na shiga yajin aiki.
To sai dai kuma kungiyar masu gidajen mai da iskar gas ta arewacin Najeriya wato AROGMA ta ce tana maraba da matakin da matatar Ɗangote ta ɗauka na yin dakon mai zuwa gidajen man a faɗin ƙasar.
Akwai dai rahotanni da ke cewa ma'aikatan kungiyar ta NUPENG sun fara rufe wasu gidajen mai a arewacin Najeriya a matsayin martani ga kamfanin na Dangote.











