Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ƙarin N40,000 muka gani a albashi mafi ƙaƙanta'
Yayin da gwamnatin Najeriya ke cewa ta fara biyan ma’aikatanta sabon albashi da aka gina kan mafi ƙanƙatar albashi na naira 70,000, ma’aikatan sun ce ba a bin da suka tsammata suka gani ba.
Wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya da BBC ta tattauna da su sun tabbatar da samun ƙarin, wanda gwamnati ta fara biya ne daga ranar Alhamis da ta gabata.
Wannan na zuwa ne wata bakwai bayan fara tattaunawa kan ƙarin albashin tsakanin gwamnati da ƙungiyar kwadago ta ma’aikata NLC, da kuma TUC ta ‘yankasuwa.
Tun a ranar 29 ga watan Yulin da ya gabata ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar ƙarin mafi ƙanƙantar albashi daga N30,000 zuwa N70,000 bayan tattaunawa mai tsawo da ƙungiyoyin.
“Duka m’aikatan da ake biya albashi ta tsarin IPPIS sun samu ƙarin,” kamar yadda kakakin ofishin babban akanta na ƙasa Bawa Salihu Makwa ya shaida wa BBC.
Sai dai ya ce ba lallai ne duka ma’aikatan su ga albashin ba a ranar Alhamis, abin da ya sa suka fara turawa da wuri kenan.
A ranar Laraba ita ma hukumar kula da yi wa ƙasa hidima ta NYSC ta sanar da ƙarin alawus ɗin da take bai wa matasan daga N33,000 zuwa N77,000, wanda ake aunawa da mafi ƙanƙantar albashin tsawon shekaru.
‘N40,000 muka gani’
Saɓanin abin da wasu ma’aikata suka yi tsammani, wasu sun yi iƙirarin cewa N40,000 aka ƙara wa kowa da kowa a yanzu.
Sai dai sun ce an faɗa musu cewa lissafin na iya sauyawa nan gaba idan ofishin tsara albashi na ƙasa ya fitar da lissafin abin da kowane ma’aikaci zai samu gwargwadon matakin aikinsa.
A gefe guda kuma, masana harkokin ƙwadago sun ce akan yi ƙarin ne gwargwadon matakin ma’aikaci, abin da ke nufin ba kowane ma’aikaci ne zai samu ƙarin N70,000 ba. Wanda ke da tabbas game da abin da zai samu shi ne ma’aikaci na mataki mafi ƙanƙanta, wanda a baya yake karɓar N30,000.
“Dukkan ma’aikata daga sama har ƙasa, N40,000 suka samu a matsayin ƙari. Sai dai fa idan kana da wani alawus da ake bai wa mutum sannan zai fi N40,000,” a cewar wani ma’aikaci da ya nemi a sakaya sunansa.
Shi ma wani ma’aikacin ya tabbatar da samun ƙarin N40,000, yana mai cewa akwai lissafin da suke jira.
“Sun ce akwai teburin da za a fitar nan da ƙarshen watan Oktoba da za mu shiga, kuma sai ya fito ne sannan albashin zai daidaita,” in ji shi.
Sai dai kakakin ofishin akanta Bawa Salihu ya ce idan aka haɗa da tsohon albashin lissafin zai yi daidai.
“Ai da ma mafi ƙanƙantar albashi ake magana wanda aka mayar da shi 70,000. To idan aka haɗa 30,000 da 40,000 ba ya zama 70,000 ba? To maganar kenan,” kamar yadda ya bayyana.
Cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya yi a ranar da ya karɓi mulki cikin watan Maris na shekara ta 2013, ya sanya farashin kayan masarufi ya nunnunka, lamarin da ya jefa al'ummar ƙasar cikin mummunan hali.
An shafe watanni ƙungiyar ƙwadago na ja'inja da gwamnati kan ƙarin albashi, kafin cimma matsaya kan N70,000 a matsayin mafi ƙanƙanta.
Tuni dai wasu jihohi suka ce sun fara biyan albashin mafi ƙanƙanta.