Hotunan sabon masallaci mafi girma a Afirka da aka buɗe a Aljeriya

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya ƙaddamar da masallaci mafi girma a Afirka a birnin Algiers
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shi ne masallaci na uku mafi girma a duniya bayan masallatai masu tsarki na birnin Makkah da Madina
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gina katafaren masallacin mai suna 'The Great Mosque of Algiers' kan kadada saba'in kuma masu ibada dubu ɗari da ashirin za su iya sallah a cikin sa lokaci guda
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gina masallacin cikin shekara bakwai inda kuma aka kashe sama da dala miliyan 8000 wajen gina shi
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana sa ran za a riƙa gudanar da salloli a lokacin watan Ramadan da ake shirin farawa nan da mako biyu masu zuwa
..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masallacin wani aiki ne na tsohon shugaba Abdelaziz Bouteflika wanda ya sauka daga kan mulki a 2019 bayan yunƙurinsa na neman wa'adi na biyar ya janyo gagarumar zanga-zanga