Yamal ya ce yana son wannan ƙarnin ya zama na Barcelona ne

Asalin hoton, Getty Images
Lamine Yamal ya sanar cewar yana fatan wannan ƙarnin ya zama na Barcelona ne a fannin taka leda a duniya.
Matashin ɗan wasan ya faɗi haka ne lokacin da ya gana da ƴan jarida kan wasan Champions League da Inter Milan zagayen daf da karshe.
Ranar Laraba, Barcelona za ta kece raini da Inter Milan a Estadi Olimpic a wasan farko zagayen daf da karshe a gasar ta zakarun Turai.
Matashin ɗan wasan cikin murmushi ya ce ''Muna murna domin yawancin mu wannan shi ne karon farko da za mu buga daf da karshe a Champions League.
''Muna mutakar son mu kai karawar karshe a gasar zakarun Turai, kuma a shirye muke mu sa dukkan kwazon da ya kamata.''
An tambayi Yalam kan ingancin ƙungiyar Inter Milan sai ya ce ''Kowa ya san Inter babbar ƙungiya ce, kuma suna da fitattun masu tsaron baya. Suna da ƙyau a gurbin kai hare-hare, da zarar sun samu ƙwallo sun iya kai matsi, sannan suna komawa baya gabaki ɗayansu.''
''To sai dai muma muna da kyau, za kuma mu yi dukkan abin da ya kamata na taka leda kan yadda muka saba, domin mu samu nasara. Gasar Champions League kuma karawar daf da karshe, za kuma yi wasan neman zuwa karawar karshe - kowa zai yi kokarin da kuma sa ƙwazo.''
An tambayi Yamal cewar ta yaya mai shekara 17 yake fuskantar kalubale a wasannin da yake da manyan kungiyoyi, sai ya ce: Yanayi a wasan da muka lashe Copa del Rey abin mamaki ne, zan so na sake samun yadda na ji a karawar nan gaba.
''An kara min kwarin gwiwa kafin wasan, koda yake da farko na yi ta fargaba kafin karawar, amma ban fuskanci kalubale ba, kawai ina son taka leda na kuma sa ƙwazo a wasan. Na cire dukkan wani tsoro a zuciya ta.''
Dalilin da Yamal ke samun ci gaba a fannin taka leda, saboda shi matashi ne, sannan dukkan ƴan wasa sun rungume shi, wanda ya fara daga La Masia.
''Muna sa kwazo da zarar mun sa rigar Barcelona, saboda mun fara tun daga makarantar ƙungiyar, mun kuma san mahimmacin hakan.
Bana fatan wannan ƙarnin ya zama na Lamine Yamal ne kawai, ya kamata ya zama na Barcelona ne, in ji matashin ɗan wasan tawagar Sifaniya.











