Wane tasiri ƙudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan tsagaita wuta a Gaza zai yi?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, By Ethar Shalaby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
A karon farko tun bayan da Hamas ta kai hari kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, abin da ya assasa yaki a Gaza, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya samu nasarar zartar da wani kuduri da ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a tsakanin bangarori biyu da ke rikici da juna.
Me ya faru yayin kada kuri'ar da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kira a ranar Litinin 25 ga watan Maris 2024?
Kudurin da aka amince da shi ya ce dole a gaggauta tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da 'yan gwagwarmayar Falasdinawa saboda watan Ramadan da ake ciki, abin da ake fargabar ko matakin zai dore baki daya.
Kudurin mai lamba 2728, ya kuma bukaci a gaggauta sakin dukkan wadanda aka yi garkuwa da su sannan a tabbatar da kayan agaji na isa Gaza.

Asalin hoton, EPA
Su waye suka kaɗa ƙuri'a a kan ƙudurin?
Kasashe 14 mambobin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ne suka kaɗa ƙuri'a a kan ƙudurin, kuma cikinsu babu wadda ta ki amincewa da shi, to amma Amurka ta ƙauracewa zaman kwamitin.
A baya Amurka ta yi watsi da ƙudurori uku sannan ta kauracewa biyu, a lokuta da dama ta na cewa kudurorin ba za su taimaka wajen sakin mutanen da aka yi garkuwa da su ba ko kuma ta ce kudurorin ba sa alawadai da harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Kuduri na baya bayannan, mambobin 10 da ba na na dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ne suka bullo da shi a karkashin jagorancin Mozambique.

Asalin hoton, Reuters
Wanne martani Isra'ila ta yi a game da kauracewar Amurka a wajen kada kuri'a?
Matakin Amurkan ya haifar da zaman dar dar tsakaninta da kawarta Isra'ila a kan hare haren da ake kai wa.
Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan, ya ce"Abin takaici, a yau ma kwamitin ya ki yin alawadai da harin 7 ga watan Oktoba."
To amma duk da haka ya fahimci cewa kudurin ya tabo batun Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su.
Cikin kudurin, "Kwamitin ya yi alawadai da matakin Hamas na garkuwa da Isra'ilawa inda ya ce hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa." Idan aka zo batun dawo da wadanda aka yi garkuwa da su gida, ya kamata kwamitin ya dauki matakin da ya ce."
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya soke yin wata tafiya da ya yi niyyar yi zuwa Washington.
To amma, mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka John Kirby, ya ce ganawar da aka tsara yi tsakanin ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant da mai ba da sha'awara kan harkokin tsaron Amura Jake Sullivan, ba fashi.
Daga karshe dai Gallant da Blinken ne suka gana a ranar Talata.

Asalin hoton, Reuters
" Mu na so mu tabbatar wa ministan tsaron Isra'ila cewa Amurka za ta ci gaba da goyon bayan Isra'ila a yayin da ta ke yaki da Hamas" in ji Kirby a wani taron manema labarai a ranar Litinin.
Ya ce, matakin Amurka na kauracewa kada kuri'a a kudurin, ba yana nufin ta janye a kan manufofinta ba ne, ya ce Amurka ta kauracewa kada kuri'arta ne saboda kwamitin ya gaza yin alawadai a kan Hamas.
Kirby ya ce," Babu abin da ya canza a kan manufofinmu ko kadan"
Cikin wata sanarwa da ofishin Netanyahu ya fitar, ya ce Amurka ta manta da matsayinta na baya wanda ke da alaka da sanarwar tsagaita wuta da kuma batun sakin wadanda aka yi garkuwa da su.

Asalin hoton, EPA
Me ya sa wasu kasashe suka yi watsi da kudurin na Gaza?
Rasha da China ma na cikin kasashen da suka yi watsi da kudurori biyu da Amurka ta fitar a kan rikicin Isra'ila.
A ranar Jumma'a, jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vassily Nebenzia, ya ce Amurka ta jagoranci wani kuduri, to gaskiya siyasa ce kawai.
Ya ce hakan wata alama ce ga Isra'ila a kan ta ci gaba da kai hare hare Rafah.
Ya ce hakan zai kara ba wa Isra'ila dama ta rinka yin abubuwan da ta ga dama a Gaza, sannan su kuma al'ummar Gazan za su ci gaba da fuskantar barna da kalubale iri-iri.

Asalin hoton, Reuters
Jakadan China a Majalisar Dinkin Duniya, Zhang Jun, ya ce Amurka ta gaza bayyana ainihin abin da ta ke nufi a kan manufarta kan hare haren da Isra'ila ke kai wa Rafah.

Asalin hoton, EPA
Kodayake jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, ta ce kudurin hadaka tsakanin Rasha da China, ya gaza cimma abubuwan da ake bukata.
" A wannan yanayi da ake ciki, kudurin ya gaza samar da kyakkyawar diplomasiyya a yankin, a maimakon haka abubuwa sai kara muni suke, kuma hakan da sannu a hankali zai iya sa Hamas ta fice daga tattaunawar da ake" in ji ta.

Asalin hoton, Reuters
Ko kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2728 zai dore?
Mataimakin mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya, Farhan Hag, ya ce kudurin kwamitin tsaron doka ce ta kasa da kasa don haka ya zama doka kawai.

Asalin hoton, EPA
Ko zai iya yiwuwa a mayar da kudurin na dindindin a karkashin sashe na 7 na kundin Majalisar Dinkin Duniya?

Asalin hoton, Getty Images
A 2006, sashen ya haramtawa Iran samar da makamai ga wata kasa abin da ya janyo aka sanya mata takunkumi.
Wani mai sanya idanu daga bangaren Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, ya bukaci ayi amfani da wannan sashe.
Ya ce,"Mun zo taron kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, an shaida mana cewa kudurin ba mai dorewa ba ne, mu ba mu amince da hakan ba."
Ya ce, idan har isra'ila ta yi niyyar yin wani abu da bai dace ba, to alhakin kwamitin ne ya yi amfani da wannan sashe wajen daukar matakan da suka dace a kan Isra'ilan.

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, EPA
Ko wannan kuduri zai yi tasiri a kan tattaunawar da Doha ke yi?
A ranar Talata, Qatar ta ce kudurin ba shi da wani tasiri a kan tattaunawar tsagaita wuta da ake a Doha.
Kasar ta jima ta na gudanar da tattauna a kan batun tsagaita wuta a Gaza.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkikin wajen Qatar, Majed Al- Ansari, ya ce," Ba mu ga wani sakamako a tattaunawar da ake ba.A kullum jiya a yau ake."
Tun da farko kafar yada labaran Isra'ila ta rawaito cewa tawagar Isra'ila da ta je Qatar kwana takwas ta bar kasar, bayan da Hamas ta yi watsi da batun sakin wadanda ta yi garkuwa da su a tattaunawar da ake Doha.






