Amurka ta yi kuskuren kakkaɓo jirginta yayin luguden wuta kan ƴan Houthi

Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Amurka
Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar sojin Amurka ta ce ta kai hare-hare ta sama kan sansanonin mayakan Houthi a Sana'a babban birnin kasar Yemen da ke hannun 'ƴan tawayen.

Hakan na zuwa ne sa'o'i bayan da ƙungiyar ta Houthi ta harba wani makami mai linzami kan Isra'ila, wanda ya raunata gomman mutane

Babbar bataliyar rundunar sojin Amurka da ke sa ido kan ayyukan rundunar a gabas ta tsakiya, ta ce an kai hare haren ne kan wata cibiyar ajiyar makamai masu linzami da kuma wani wurin ba da umarni a babban birnin kasar Sanaa.

Ta kara da cewa a yayin farmakin sojojin na Amurka sun yi nasarar kakkabo jirage marasa matuka da dama na yan tawayen na Houthi da kuma lalata makamai masu linzamin da suke amfani da su wajen kai hare hare a tekun maliya.

Isra'ila ta ce mutane 16 ne suka jikkata a harin makami mai linzamin da 'yan Houthi suka kai kan Tel Aviv, wanda shi ne na baya-bayan nan da aka kai wa Isra'ila bayan fara yakin Gaza.

Kungiyar da Iran ke marawa baya ta ce tana jan zare da Isra'ilar ne, don mara baya ga Falasinawa.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce a shirye take ta shiga yaki daga nan har illa masha'allahu.

Amurkar dai ta yi kuskuren kakkabo wani jirginta yayin da take luguden wuta kan wuraren mayakan, abun da ya Hutsin suka bayyana da cewa kaikayi ne ya koma kan mashekiya.