Ta yaya hare-hare a tekun Maliya za su shafi kasuwancin duniya?

.

Asalin hoton, Reuters

Kasuwancin duniya zai fuskancin mummunan tarnaki, sakamakon yadda manyan kamfanonin fiton kaya na duniya ke janyewa daga tekun Maliya.

Hare-hare da 'yan tawayen Houthi a Yemen ke kai wa jiragen 'yan kasuwa a makonnin baya-bayan nan, sun sanya manyan kamfanonin fiton kaya daukar matakin janyewa daga daya daga cikin manyan hanyoyin zirga-zirgar fiton kaya na duniya.

Kungiyar Houthi ta bayyana goyon bayanta ga Hamas, sannan kuma ta ce za ta rika kai hari kan duk wani jirgin ruwan da ke kan hanyar zuwa Isra'ila, duk da cewa ba a sani ba ko duka jiragen da kungiyar ta kai wa harin na kan hanyar zuwa Isra'ilan ne.

Mene ne ya faru?

Houthi ta fara zafafa hare-hare a tekun ne tun bayan fara yakin Isra'ila da Hamas a watan Oktoba.

Kungiyar - wadda ke samun goyon bayan Iran - na amfani da jirage marasa matuka da rokoki kan jiragen ruwa mallakin kasashen waje da ke jigilar kaya, a kan hanyar Bab al-Mandab, mai nisan mil 20 daga ruwan da ya raba kasashen Eritrea and Djibouti a bangaren Afirka da kuma Yeman daga bangaren yankin kasashen Larabawa.

Jiragen ruwan kan bi wannan hanyar daga kudu domin su isa yankin Suez na kasar Masar a arewaci.

Sakamakon hare-haren da kuma fargaba, manyan kamfanonin fiton kaya na duniya da dama, ciki har da kamfanin fiton kaya na tekun Mediterranean da kamfanin fiton kaya na Maersk, sun karkatar da akalar jiragensu wajen yin dogon zagaye ta hanyar biyowa da kudancin Afirka sannan su kewayo ta yammaci kafin shi shiga Turai don kauce wa hatsarin hare-haren.

.

Shi ma kamfanin fiton kaya na BP ya sanar da dakatar da jigilar danyen mai a tekun na Maliya, saboda ''tabarbarewar yanayin tsaro a tekun''

Dogon zagayen na kara wa jiragen tafiyar tsawon kwanaki akalla 10, lamarin da ke kara wa kamfanonin kashe miliyoyin daloli.

Me ya sa hanyar fiton ke da muhimmanci?

Duk jirgin da ke bi ta hanyar Suez Canal ko ta tekun Indiya dole ya bi ta hanyar Bab al-Mandab da tekun Maliya.

Hanyar Suez Canal ita ce hanya mafi saukin jigila tsakanin Asiya da Turai, kuma tana da matukar muhimmanci a jigilar mai da iskar gas tsakanin wadannan yankuna biyu.

A farkon shekarar 2023 akan yi jigilar gangar mai miliyan tara a kowace rana ta hanyar Suez Canal, kamar yadda kamfanin kididdiga na Vortexa ya bayyana.

.

Asalin hoton, EPA

Masu sharhi a kamfanin S&P mai sa ido kan kasuwanci sun ce kusan kashi 15 na kayayyakin da ake shiga da su Turai da Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, ana shigar da su ne daga Asiya da yankin Gulf ta hanyar Teku.

Wannan ya hadar da kashi 21.5 na tataccen man fetur da fiye da kashi 13 na danyen man.

To amma ba man fetur ne kadai ba. Akwai kwantenonin da ke dakon nau'ikan kayayyaki da ake iya gani a shaguna ciki har da akwatunan talbijin da tufafi da kayayyakin wasanni.

Ta ya matakin zai shafi masu saye?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babu makawa safarar kayayyaki zai fuskanci cikas sakamakon sauya akalar jiragen ruwa daga tekun na Maliya, to amma kayyakin da aka sarrafa domin amfani ''su ne matakin zai fi shafa kai-tsaye'', kamar yadda Chris Rogers, jagoran bincike a kamfanin S&P ya bayyana.

Za a samu jingirin kayayyaki zuwa shaguna, sakamakon karin lokacin zuwansu na akalla kwanaki 10, saboda sabuwar hanyar 'Cape of good Hope' da yanzu ake bi an samu karin kimanin kilomita 6,482.

Manyan kamfanonin kayyakin gidaje na Ikea da Next na Birtaniya duka sun yi gargadin cewar za a samu jinkiri a jigilar kayyakin aikinsa idan aka ci gaba da samun tsaiko wajen fiton kayyakin a tekun.

Zagayen zai kara wa kamfanonin kashe karin kudade. A makon da ya gabata an samu karin kashi hudu na kudin fiton kayyaki, kuma karin zai shafi masu saya ne.

Farashin ya kasance kasa da abin da ake biya a shekarar da ta gabata, haka kuma ya yi kasa sosai da farashin da aka gani a shekarar 2021, a lokacin annobar cutar corona.

Akwai kuma fargabar tsaikon zai iya haddasa karin farashin man fetur.

Karuwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, zai iya haddasa karuwarsa a gidajen mai, tare da haddasa karuwar farashin kayayyaki.

Shin jigilar kayyaki ta teku ne kawai mafita? Mista Rogers ya ce jigilar kayayyaki ta jirgin kasa na bukatar ''ratsawa ta kasar Rasha'', wadda ke karkashin takunkuman tattalin arziki sakamakon mamayar Ukraine.

Me aka yi don mayar da martani?

Hare-haren sun tilasta wa Amurka girke sojojin ruwa domin kare jiragen ruwa a tekun na Maliya, sannan kuma wasu kasashe irin Birtaniya da Canada da Faransa da Bahrain da Norway da Sifaniya su ma sun bi sahunta.

Sakaraten harkokin tsaron Amurka Lloyd Austin ya yi kira ga wasu karin kasashe da su tallafa wajen kare jiragen fiton kaya a yankin.

Tosai dai har yanzu kamfanonin fiton kaya na fargabar cigaba da amfani da hanyar, duk kuwa da irin karin tsaron da aka samu a yankin.

Kamfanin fiton kaya na Maersk ya koma amfani da hanyar bayan samuwar jami'ar tsaro a yankin, to sai dai ya dakatar da aiki a baya-bayan nan a tekun na Maliya bayan da aka kai hari kan wani jirginsu da ke dakon kwantainoni.