Mayaƙan Houthi sun yi iƙirarin nitsar da jirgin ruwan Birtaniya

...

Asalin hoton, EPA

Mayaƙan Houthi na Yemen sun ce jirgin ruwan Birtaniya da suka kai wa hari a ranar Lahadi ya nitse a kogi.

Babu dai wani bincike mai zaman kansa da ya tabbatar da iƙirarin ƙungiyar mai samun goyon bayan Iran.

Amma gwamnatin Birtaniya an ceto mutum 24 da ke cikin jirgin ruwan.

Mayaƙan Houthin sun kuma ce sun kai wasu ƙarin hare-haren a kan wani jirgin jigalar kaya mallakin Amurka, bayan sun hari na Birtaniyan mai ɗauke da takin zamani.

Ƙungiyar dai ta ce tana kai hare-hare a kan jiragen ruwa masu jigilar kaya ne, domin nuna goyon bayanta ga Falaɗinawan Gaza.

Kakakin mayaƙan Houthi, Yahya Serea ya yi bayani kan harin, a wani saƙon da aka yaɗa ta talabijin.

Ya ce: "An kai hare-haren ne da manyan makaman sojin ruwa da suka dace, kuma alhamdulillah an yi nasara. A cikin sa’oi 24 mayaƙan mu sun kai hari kan wurare daban-daban har guda huɗu..")

Dakarun Amurka da na Birtaniya ma sun ce sun mayar da martani, ta hanyar yin lugude a sansanin Houthi a Yemen.

Sun kuma ce ba zasu gaji ba sai sun ga bayan mayaƙan da ma masu tallafa masu.