Ƴanbindiga sun tayar da wasu garuruwan Katsina

Ƴanbindiga masu satar mutane sun tilasta wa al'ummar wasu garuruwa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya yin gudun hijira.

Yanbindigar sun abka ne garin Wurma da ke ƙaramar hukumar Kurfi inda suka bude wuta, lamarin da ya tilasta wa mutanen yankin gudun hijira domin tsira da ransu zuwa makwabta.

"Babu kowa a garin duka an fito," kamar yadda wani mazauni garin Wurma ya shaida wa BBC

Gwamnatin jihar Katsina da ta tabbatar da al'amarin ta ce matsalar ta kuma shafi garuruwan Lambo da Guda da ke yankin na Kurfi.

Kwamishinan tsaron jihar Katsina Dakta Nasir Baangida Ma'azu ya ce ƴanbindigar sun matsawa yankin.

"Shiga ta farko sun bi gida-gida, shiga ta biyu kuma suka ƙone sansanin ƴansanda, dalilin da ya sa mutane suka gudo," a cewar Kwamishinan.

A ranar Juma'a wasu al'ummar yankunann na karamar hukumar Kurfi sun gudanar da zanga-zanga kan kan ƙamarin matsalar tsaron da ke addabarsu.

Sun ce an kashe mutane da sace da dama sakamakon yawaitar hare-haren na ƴanbindiga baya ga asarar dimbin dukiya.

"Da magariba suka kawo mana hari, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, sun kashe akalla mutane biyar, dukkansu magidanta."

Sun kwashi dukiya mai yawa wannan abin ya bai wa mutane haushi, don haka duka aka fito daga garin Wurma aka yi bore saboda mutanenmu na ganin ita ce hanyar da za ta tilasta wa gwamnati ɗaukar mataki,'' in ji wani mazauni yankin.

Ya kuma ce an gudanar da irin wannan zanga-zanga a garin Birchi da ke cikin karamar hukumar Kufin, da su ma ke fama da matsalar ta ɓarayin daji masu satar mutane domin neman kudin fansa.

Mutane na gudun hijira

Wata matsalar da suke fama da ita ita ce ta kwararar 'yan gudun hijira daga garuruwa makwabta da hare-haren ƴanbindigar suka tilasta wa barin muhallansu.

Wani mazaunin garin Birchi ya shaidawa BBC garin ya cika makil da 'yan gudun hijira, ya ce a tashar mota da daddare za ka iske mutane sama da 50 a nan suke kwana saboda rashin inda za su nufa.

Kwamishinan tsaro na jihar Katsina Dakta Nasir Baba Mu'azu, ya ce gwamnati na sane da halin da ake ciki da shan alwashin magance matsalar tsaron da ta addabi mazauna garuruwa da kauyukan jihar.

Ya ce gwamna ya kai ziyarar gani da ido garin Birchi domin jajantawa al'ummar yankin.

"Gwamnati na iya bakin kokarinta domin ganin an shawo kan matsalar tsaron nan," in ji shi.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro ta barayin daji masu satar mutane domin neman kudin fansa da kashe-kashen jama'a.

A baya-bayan nan gamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da rundunar 'yan sintiri da ta yi wa lakabi da Community Watch Corps domin magance matsalar tsaro a sassan jihar.

Sabuwar rundunar 'yan sintiri ta jihar Katsina wadda aka ƙaddamar tana da jami’ai 1,500 waɗanda za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro wajen wanzar da tsaron, musamman a garuruwan da ake fama da harin 'yanbindiga a Katsina.

Sai dai duk da ƙoƙarin gwamnatin ta Katsina da kuma hukumomin tsaro, amma al'ummar yankin na ci gaba da fuskantar hare-hare.