Yaz Plus: Afirka ta Kudu ta janye wani maganin tazarar haihuwa daga kasuwa

    • Marubuci, Smitha Mundasad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health reporter
  • Lokacin karatu: Minti 3

Hukumomin kula da ingancin magunguna a Afirka ta Kudu sun bayar da umarnin janye fitaccen maganin tazarar haihuwar nan mai suna Yaz Plus bayan an samu kuskure wajen shirya ƙwayoyin maganin a cikin fakiti, wanda hakan ke nufin za a iya samun raguwar ƙarfin aikin maganin.

Kamfanin haɗa maganin, Bayer Ltd, ya ce mata da suke amfani da magangunan da aka fitar a ɗan tsakanin nan, su daina, kuma su je wajen likitoci domin neman shawarwari.

Kuskuren jera ƙwayoyin maganin ya sa an samu fakiti mai ƙwayoyi 24 waɗanda ba sa yin aiki, maimakon guda 24 masu aiki.

Matsalar ta shafi wasu ƙayyadaddun fakiti ne, waɗanda suke da lambar sana'antawa ta WEW96J, kuma za su daina aiki a Maris na 2026.

Kamfanin Bayer ne ya janye maganin, bayan tattaunawa da hukumar kula da ingancin kayan kiwon lafiya, inda kamfanin ya ce an gano "musabbabin" kuskuren, kuma an magance matsalar.

Asalin fakitin Yaz Plus na tazarar haihuwa yana ƙunshe ne da ƙwayoyi 24 masu aiki waɗanda suke ɗauke da sinadaran da suka dace, kuma suna da kalar ruwan hoda ne, sai wasu guda huɗu waɗanda ba sa aiki, kuma suke da kalar ruwan lemu.

Amma a waɗanda aka janye daga kasuwa, sai aka samu wasu daga fakitin suna ɗauke da waɗanda ba sa aiki guda 24, da masu aikin ƙwara huɗu.

Fargabar ita ce mata za su iya ɗaukar ciki bayan sun yi amfani da maganin saboda sun sha ƙwayoyi ne waɗanda ba sa aiki da tunanin masu aikin suke sha.

A sanarwar janye maganin da kamfanin Bayer Ltd ya fitar, ya ce, "duk da cewa wasu ƙayyadaddun fakiti ne kuskuren ya shafa, amma saboda tabbatar da kariya, kada a yi amfani da kowane fakiti har sai an tattauna da likita ko wani ma'aikacin asibiti, domin ba dole ba ne su bayar da kariyar da ake buƙata wajen hana ɗaukar ciki."

Duk wanda ya sayi fakitin ƙwayoyin a ɗan wannan tsakankanin, an buƙaci ya mayar da shi kantin sayar da maganin da ya saya domin a musanya masa ko a mayar masa da kuɗinsa.

Ma'aikatan jinya da asibitoci da kantunan sayar da magunguna da likitoci da dillalan magunguna da suke da fakitin maganin duk an buƙaci su mayar da shi.

A wata sanarwa, kamfanin Bayer Ltd ya ce, "an gano musabbabin kuskuren da aka samu wajen jera ƙwayoyin a cikin fakiti, sannan tuni an ɗauki wasu matakai domin hana sauke aukuwar hakan."

Sai dai kamfanin ya ƙara da cewa matsalar ta shafi wasu ƙayyadaddun fakitin magungunan ne, ba duka ba.

Kuma kamfanin ya fitar da wasu lambobin waya ga duk wanda yake buƙatar ƙarin bayani.