'Rashin albashi ya sanya mun cire yaranmu daga makaranta'

Zamfara State Governor

Asalin hoton, DAUDA LAWAN DARE

A Najeriya, wasu ma'aikatan jihar Zamfara fiye da dari sun koka kan yadda aka ki mayar da su bakin aiki, bayan da suka jingine ayyukansu, suka rike wasu mukaman siyasa a lokacin gwamnatin jihar da ta gabata.

Ma'aikatan sun ce, an kafa kwamitoci fiye da uku da suka tantance su, kuma suka bayar da shawarar a mayar da su bakin aikinsu, amma abin ya ci tura.

Yanzu haka kuma sun kwashe wata goma sha biyar ba albashi, har al'amarin ya jefa rayuwarsu da na iyalinsu cikin mawuyacin hali.

Ma'aikatan su dari da ashirin da biyu, sun ce sun bi doka da ka'idar jingine aiki, yayin da gwamnatin jihar Zamfara da ta gabata ta ba su riko wasu mukamai na siyasa.

Sai dai bayan karewar wa'adin mukaman, sun nemi komawa bakin ayyukansu na asali, amma abin ya gamu da tsaikon da ba su zata ba, a cewar daya daga cikinsu, Jamilu Haruna Kalale, iyan Dan Sadau:

"Duk da an yi kwamitoci har uku amman har yanzu ba a mayar da mu ba " in ji shi

Jamilu Haruna Kalale, wanda ya rike mukamin babban darakta a hukumar kula da harkokin wasanni ta jihar Zamfarar, ya ce wannan ba shi ne farau ba domin ko a baya ya rike irin wannan mukami na siyasa kuma yana gamawa ya koma bakin aikinsa.

Tsaikon da aka samu wajan mayar da wadannan ma'aikata kan ayyukansu da rashin biyan su albashi na tsawon wata goma sha biyar, duk sun jefa rayuwarsu da ta iyalansu cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Kwamared Sani Garba Gusau ya ce da su da iyalansu suna cikin wahala da tashin hankali :

"Wanda ke da albashi ya ya ƙare bare mu, yaro na ya yi rashin lafiya saboda rashin kudin magani 8,500 na koma da shi gida, matsalar ta sanya har yaranmu mun cire daga makaranta."

"Muna kira ga mai girma gwamna da ya taimaka ya mayar da mu bakin aikin mu" cewar Kwamared Sani

Kwamishinan watsa labarai na jihar Zamfarar, Mannir Haidara, ya ce gwamnatin jihar tana sane da wadannan ma'aikata da korafe-korafensu kuma za a mayar da su bakin aikin su za kuma a biya su hakkokinsu.