A shirye nake na zaune da 'yan hamayya don ceton Zamfara
Gwamnan Zamfara Dr Dauda Lawan Dare ya yi kira ga abokan hamayyarsa su zo a sa Zamfara gaba domin ciyar da ita gaba bayan hukuncin kotun koli da ya tabbatar da nasararsa ta gwamna.
Gwamna Dauda ya ce a shirye yake ya zauna da abokin hamayyarsa tsohon gwamna kuma karamin ministan tsaro Dr Bello Muhammad Matawalle kan matsalar tsaron da ta addabi jihar.
A hirarsu da BBC Gwamna Dauda ya ce bai taba shakkun rashin nasara ba a kotun koli domin a cewarsa sahihin zabe aka gudanar, amma ya fara da bayyana farin cikinsa game da hukuncin.








