Watakila Rooney ya koma Plymouth

Ana sa ran za a tabbatar da Wayne Rooney a matsayin kocin Plymouth a ranar Asabar ɗin nan bayan tattaunawa a kan ofishin.

Rooney mai shekara 38 dai ya zaƙu ya sake farfaɗo da ƙimarsa tun bayan faɗuwar warwas ɗin da ta yi a kakar da ta gabata a Birmingham a lokacin da ya rasa wasanni tara daga cikin 15 ɗin da aka taka.

Kulob ɗin Plymouth dai na neman sabon koci tun bayan korar Ian Foster a ƙarshen kakar wasannin da ta gabata.

Darekta Neil Dewsnip tare da kocin kulob ɗin Kevin Nancekiviel ne suka yi riƙon ƙwarya har zuwa ƙarshen lokacin da ya rage, inda suka kai Plymouth ɗin ga tudun mun tsira.

Shi Dewsnip ya san Rooney tun lokacin yana koci a Everton.

Rooney ya taka leda sau 763 a matsayin ɗan wasa lokacin zamansa a Everton da manchester United da MLS club da DR United da kuma Derby.

Daga nan ne ya zama ƙaramin koci tare a Derby County ɗin a watan Nuwamban 2020 sannan kuma ya sanar da ajiye aiki watanni biyu bayan nan, sakamakon ayyana shi a matsayin manaja mai cikakken iko.

Rooney wanda tsohon ɗan wasan gaban Ingila ne ya jagoranci wasanni 85 a kulob din na Derby kafin ya koma Amurka ya zama manaja a kulob ɗin DR United.

A naɗa shi a matsayin manaja a Birmingham a watan Oktoban 2023, sai dai kuma an tsige shi a ƙasa da watanni uku da fara aiki.