Ɗanwasan bayan Chelsea Fofana ba zai sake buga wasa ba a kakar bana

    • Marubuci, Sam Drury
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Chelsea Enzo Maresca ya tabbatar cewa raunin da ɗanwasan bayansa Wesley Fofana ya ji raunin da ba zai bar shi ya sake buga wasa ba a kakar bana.

A ranar Asabar ne kulob ɗin ya tabbatar an yi wa Fofana mai shekara 24 ɗan Faransa tiyata "cikin nasara".

Yayin da Chelsea za ta ƙarasa kakar ba tare da Fofana ba, Maresca ya ce yana da ƙarin gwiwar ɗanwasan tsakiya Romeo Lavia da ɗanwasan gaba Marc Guiu za su dawo taka leda kafin ƙarshen kakar ta bana.

"Abin takaici, Fofana ba zai sake buga wasa ba a kakar nan," in ji kocin kafin wasan da za su buga da Legia Warsaw a kakar Euefa Conference League ranar Alhamis.

"Amma muna fatan dawowar Romeo nan gaba kaɗan. Ban sani ba ko zai iya buga wasa mai zuwa amma dai yana samun cigaba sosai.

"Akwai buƙatar mu taimaka musu sai kuma mu ga abin da zai faru nan da ƙrshen kaka.

"Akwai labari mai daɗi kan Marc. Ya ji garau yau sosai, kuma zai iya dawowa kafin ƙarshen kaka."

Lavia mai shekara 21, shi ma na fama da rauni.