Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Autan na Aisha ya ji jiki a dambe da Bahagon Autan Mamman
Autan na Aisha bai taba damben da ya sha wahala kamar wanda ya yi da Bahagon Autan Mamman ranar Lahadi a Marabar 'Nyanya a jihar Nasarawa, Najeriya.
Damben naira 100,000 ne tsakanin dan wasan Jamus da na Guramada, inda suka yi turmi uku ba kisa alkalin wasa, Anas Dandume ya raba su.
Tun daga turmin farko zuwa na uku Autan na Aisha gudu yake daga fili, wani lokacin ma a kan buhu yake tsayawa ya yi dambe.
Bayan da suka yi hutu a turmin farko magoya baya sun ba su kudi domin kara musu kwarin gwiwa.
Amma dai Arewatawa sun yi murna da damben, ganin yadda dan wasansu ya taka rawar gani.
Autan na Aisha, wanda sama da wata biyar bai fadi ba a gidan wasa na Idris Bambarewa, ya sha wahala ma a damben da ya yi da Rabe Bahagon Ebola.
Shi kuwa Rabe Shagon Ebola a turmin farko ya kashe Dan Yalon Arewa a damben gasa na naira 100,000 a damben safiyar Lahadi a Maraba.
Sa zare kuwa tsakanin Ilele da Bahagon Ali Kawoji an ji jiki, amma turmi uku suka yi ba kisa a damben naira 100,000 shima.
Damben da suka yi:
- Bahagon Ali Kansila Guramada ya buge Ushu Shagon Inda daga Jamus.
- Aljanin Nokiya daga Jamus ya yi nasara a kan Albaru Shagon Yalo daga Kugu.
- Dogon Mamman daga Arewa ya buge Shagon Basiru Guramada.
Wasannin da aka yi canjaras:
- Shagon Mada daga Kudu da Inda daga Arewa
- Shagon Basiru Guramada da Shagon Dunan ba ta jemu ba daga Kudu
- Dan Aliyu na Arewa da Dan Yalon Autan Sikido daga Kudu
- Dogon Mamman daga Arewa da Bahagon Yahaya Guramada
- Bahagon Ali Yaro Guramada da Dogo dan Maiduguri daga Jamus
- Shagon dan Yalo daga Kudu da Autan Sanin gidan dan Kande daga Jamus.