Ƙirƙirarriyar basira ta AI za ta iya tunani kamar ɗan'adam?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Pallab Ghosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science correspondent
- Lokacin karatu: Minti 6
Shin zan iya zama butum-butumi nan gaba kuma zan iya sanin haka? Sannan zan iya tsallake gwajin?
Masu bincike da ke ƙoƙarin gano me yadda ɗan'adam ke tunani sun tabbatar min cewa binciken bai tsaya nan ba.
Wata na'ura da ake kira "Dreamachine" an ƙirƙiro ta ne domin sanin yadda ƙwaƙwalwar ɗan'adam ke sanin abin da ke faruwa da kuma masaniyar abu.
Na'urar na fito da yadda ƙwakwalwar ɗan'adam take tuna abu ta hanyar haska tocila, a ƙoƙarin gano yadda mutane ke yin tunani.

Hotuna da nake gani suna da kyau, a cewar masu binciken. Sun yi imanin cewa wannan hanyar za ta yi ƙarin haske kan yadda ƙwaƙwalwar ɗan'adam ke sanin abin da ke faruwa.
Sun ji na yi raɗa: "Abu mai kyau ne, gaskiya yana da kyau. Kamar ina watayawa cikin zuciyata!"
Na'urar wadda ke cibiyar sanin abin da ke faruwa a jami'ar Sussex, na ɗaya daga cikin sabbin ayyukan bincike da dama a faɗin duniya da ake gudanarwa, don sanin yadda ɗan'adam ke yin tunani ko sanin abin da ke faruwa: kama daga abin da zuciyarmu ke raɗa mana, da tunani da kuma jin abu har ma da ɗaukar matakai na ƙashin-kai kan duniya.
Ta hanyar sanin haka, masu binciken na fatan ƙara fahimtar abin da ke faruwa da ƙwakwalwar ƙirƙirarriyar basira ta AI. Wasu sun yi imanin cewa na'urorin AI za su zama suna sanin abin da ke faruwa da kashin kansu nan ba da jimawa ba, idan ma a ce ba su fara yanzu ba.
Sai dai me ake nufi da sanin abin da ke faruwa ko kuma tunani, kuma AI ya kusa zuwa matakin ne? Shin imanin da aka yi cewa AI zai zama mai sanin abubuwan da ke faruwa a duniya zai iya sauya ɗan'adam a shekaru masu zuwa?
Duniyar kimiyya zuwa rayuwar zahiri
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɓangaren kimiyya ya ɗauki lokaci yana bincike kan yadda ƙwakwalwar ɗan'adam ke tunani.
An fara bincike kan fargabar da na'urorin zamani ke yi wa yadda ɗan'adam ke tunani ne tun a cikin wani fim a shekarar 1968 zuwa 2001: A fim ɗin mai suna Space Odyssey, an ga yadda aka yi ƙoƙarin kashe ƴan sama jannati a cikin kumbonsu.
Haka ma a fim ɗin Mission Impossible, wani ɓangare da aka fitar a baya-bayan nan, ya nuna yadda AI ke yi wa duniya barazana, wanda aka kwatanta cewa "tunaninsa ba zai misaltu ba, ya san abin da ke faruwa da sauransu".
Sai dai a baya-bayan nan, an fara yin nazari kan yadda na'urori ke sanin abin da ke faruwa cikin sauri, har wasu ma na nuna damuwar cewa ba a san da irin abin ba saboda ya zarce sanin kimiyya.
Hakan ya biyo sauyawa ko kuma nasara da wasu na'urorin harsuna suka samu, waɗanda ake iya saka su a kan wayoyi irinsu Gemini da kuma ChatGPT. Waɗanda suka samar da waɗannan na'urori sun fara yin mamaki kan yadda na'urorin ke sarrafa rubutu da zance.
Mutane da dama na ganin cewa yayin da AI yake ƙara zama mai basira sosai, hasken da ke cikinsu zai ƙaru cikin na'urorin kuma za su fara sanin abubuwan da ke faruwa a duniya.
Wasu, kamar farfesa Anil Seth wanda ke jagorantar tawagar binciken na jami'ar Sussex, bai aminta da zancen ba.
"Muna alaƙanta sanin abin da ke faruwa da ɓangaren ilimi da kuma harshe saboda suna tafiya tare a wajen ɗan'adam. Sai dai duk da cewa suna tafiya kafaɗa da kafaɗa a wajen mu, ba ya nufin cewa a ko'ina haka suke, musamman a wajen dabbobi."
Don haka me ake nufi da sanin abin da ke faruwa?
Amsa a takaice shi ne babu wanda ya sani. Wannan yana cikin muhawara da tawagar Farfesa Seth mai ɗauke ƙwararru kan na'urorin AI suka yi, ciki har da masana kwamfuta da sauransu - waɗanda ke ƙoƙarin amsa babbar tambaya a ɓangaren kimiyya da kuma tunani.
Yayin da aka samu mabambantan ra'ayoyi a cibiyar binciken, tsarin masana kimiyyar ɗaya yake: Ƙoƙarin warware wannan babbar matsala zuwa karama a cikin jerin ayyukan bincike, wanda ya kunshi na'urar Dreamachine.

Masu binciken na fatan gano yadda ɓangarorin kwakwalwa ke aiki - don sanin yadda take gane abin da ke faruwa, kamar sauye-sauye a hanyoyin gudanar jini zuwa sassan jiki. Burin su shi ne ba wai duba dangantaka tsakanin yadda kwakwalwa ke aiki da kuma sanin abin da ke faruwa kaɗai ba, suna kuma son samar da bayanai kan ɓangarorinsa.
Shin AI ya fara sanin abin da ke faruwa ko'ina?
Wasu a ɓangaren fasaha waɗanda suka yi imanin cewa AI da ke cikin kwamfutocinmu da kuma wayoyinmu tuni watakila sun fara sanin abubuwan da ke faruwa, kuma ya kamata mu ɗauke su a haka.
Google ta dakatar da wani masanin na'urori injiniya Blake Lemoine a 2022, bayan da ya kalubalanci cewa AI na iya jin abubuwa kuma za iya fuskantar cikas.
A watan Nuwamban 2024, wani jami'in AI Kyle Fish, ya shiga cikin waɗanda suka wallafa rahoton da ke cewa da gaske ne ƙirƙirarriyar basira za ta iya sanin da ke faruwa da kuma tunani kamar ɗan'adam a nan gaba.
A baya-bayan nan ya faɗa wa jaridar New York Times cewa ya yi imanin cewa akwai dama kaɗan (kashi 15) cewa na'urorin sun riga da sanin abin da ke faruwa.
Dalili ɗaya da ya bayyana cewa hakan zai iya faruwa shi ne, babu wani mutun ko da waɗanda suka kirkiro da waɗannan na'urori, da suka san yadda suke aiki. Hakan abin damuwa ne, in ji Farfesa Murray Shanahan, babban masanin kimiyya a kwalejin Imperial da ke birnin Landan.
"Ba mu san hakikanin yadda waɗanda na'urori ke aiki ta cikinsu ba, kuma hakan abin damuwa ne," kamar yadda ya faɗa wa BBC.
A cewar Farfesa Shanahan, yana da muhimmanci ga kamfanonin fasaha su san hakikanin irin na'urorin da suke kirkirowa - masu bincike na yin duba kan haka a matsayin abin gaggawa.
"Muna cikin wani yanayi na kirkirar abubuwa masu wuyar sha'ani, inda ta kai ba musan yadda suke samar da mafitar da suke nunawa ba ko yadda suke same shi," in ji shi. "Don haka fahimtar ainihin yadda suke aiki zai ba mu damar karkato su ta hanyar da muke so da kuma tabbatar da cewa ba su da haɗari."
'Babi na gaba a wanzuwar ɗan'adam'
Kallon da ɓangaren fasaha ke yi shi ne waɗananan na'urori ba su kai ga fara sanin abin da ke faruwa ba ko kuma yadda muke kallon duniya. Sai dai wannan abu ne da wasu Farfesoshi ma'aurata a jami'ar Carnegir Mellon a Pittsburg, Farfesa Lenore da Mauel Blum ke ganin zai sauya, nan ba da jimawa ba.
A cewar Blum, hakan zai sauya ne ganin cewa AI da wasu na'urori suna da abubuwa a cikinsu, ta hanyar saka musu kyamarori da abin tunani. Suna kuma kirkiro da wani harshe a cikin kwamfutoci, a ƙoƙarin kwaikwayo irin na kwakwalwar ɗan'adam.

Asalin hoton, Getty Images
"Muna tunanin cewa hakan zai sauya matsalar sanin abin da ke faruwa kamar yadda muka san shi," in ji Lenore. "AI za su fara sanin abin da ke faruwa nan ba da jimawa ba a fahimtata."
Manuel chips in enthusiastically with an impish grin, saying that the new systems that he too firmly believes will emerge will be the "next stage in humanity's evolution".
Butum-butumi na cikin dangoginsu. Irin waɗannan na'urori za su kasance na tsawon lokaci a doron duniya watakila har da wasu duniyoyi lokacin da ba mu nan".
Masanin Falsafa a jami'ar New York David Chalmers - ya ba da amsar abin da ya sani kan sanin abin da ke faruwa a zahiri da kuma baɗini a wani taro a birnin Arizona a 1994.
Ya zayyano "babbar matsala" kan yadda kwakwalwa ke aiki da kuma tunanin abin da ke faruwa, kamar mayar da martani kan wani abin jimami.
Farfesa Chalmers ya ce yana da zimmar ganin an kawo karshen wannan matsala.
"Abin da zai fi dacewa shi ne ɗan'adam ya raba wannan sabon ilimi kyauta," kamar yadda ya faɗa wa BBC. "Watakila girman ƙwaƙwalenmu ya fi na AI."











