Murnar ficewar Nijar daga Ecowas da ƙarancin ruwan sha a Goma cikin hotunan Afirka

    • Marubuci, Natasha Booty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afrika da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.

Wani mutum rike da karamin yaro ɗauke da tutar Burkina Faso da ta Nijar.

Asalin hoton, ISSIFOU DJIBO / EPA

Bayanan hoto, A ranar Talata a Jamhuriyar Nijar, magoya bayan gwamnatin mulkin sojan ƙasar sun yaba da matakin da gwamnatin ta ɗauka na ƙulla ƙawancen ƙasashen yankin Sahel da ke ƙarƙashin mulkin soji.Da kuma matakin ficewa daga ƙungiyar Ecowas ta ƙasashen yankin yammacin Afirka
Masu zane-zanen bango suna zana hotuna da saƙonnin nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

Asalin hoton, CEM OZDEL / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Lahadin da ta gabata a Dakar babban birnin ƙasar Senegal, masu zane-zanen bango suna zana hotuna da saƙonnin nuna goyon baya ga Falasɗinawa.
A large sheep appears to pucker up to a man. Its teeth are protruding comically from its mouth.

Asalin hoton, CEM OZDEL / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Kwanaki kaɗan bayan hakan a birnin na Dakar, manoma suka baje-kolin dabbobinsu a wani bikin baje-kolin dabbobi na duniya. Hankali ya karkata kan Ladoum – nau'in rago mafi tsada a duniya.
A man walks down a catwalk dressed in black and smiles at seated spectators. Behind him are models dressed in this clothing.

Asalin hoton, THIERRY CHESNOT / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, An karrama mai sarrafa kayan sawa ɗan ƙasar Kamaru Imane Ayissi a lokacin bikin baje kolin kayayyakinsa a birnin Paris na Faransa ranar Litinin.
A tall woman in a lilac tweed shorts-suit waves at photographers as she walks.

Asalin hoton, JULIE SEBADELHA / AFP

Bayanan hoto, A cikin birnin na Paris a ranar da ta gabata, daraktar fina-finai a Faransa, ƴar ƙasar Senegal Ramata-Toulaye Sy ta ɗaga wa mutane hannu yayin da take barin bikin baje kolin kaya na Chanel Spring.
A man dressed in combat fatigues holds his gun. He is partly hidden by foliage.

Asalin hoton, MOISE NIYONZIMA / EPA

Bayanan hoto, A ranar Laraba a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo wani mayakin ƙungiyar ƴanawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda, da ta ƙwace akasarin sassan birnin Goma, ya tsaya a kan iyaka...
Residents swim while carrying their jerry cans as they gather to collect water.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Galibin mazauna birnin Goma na fama da rashin tsaftataccen ruwan sha, kuma ba su da zaɓi sai dai su nemi cika jarkoki a tafkin Kivu.
A woman gestures towards a powerful waterfall.

Asalin hoton, DANIEL BELOUMOU OLOMO / AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar, ɗiyar ɗan gwagwarmayar neman ƴancin kai na Kamaru Jacob Fossi da aka kashe, Noël Louise Mekah Fossi, mai shekaru 71, ta tsaya a daidai inda aka kashe shi a Metche Falls. Ta kasance babbar mai sukar manufofin Faransa game da ƙasar da ta yi wa mulkin mallaka.
Four people stand in a row at a photocall, holding up the Sudanese flag.

Asalin hoton, CINDY ORD / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A Amurka ranar Litinin, Ibrahim Snoopy Ahmad da Rawia Alhag da Anas Saeed da Timeea Mohamed Ahmed sun halarci inda aka nuna wani fim mai suna 'Khartoum' a bikin Fina-finai na Sundance.
A man poses with his thumbs up. Next to him a woman waves the Kenyan flag.

Asalin hoton, PAUL KANE / GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Kwana ɗaya kafin nan, ɗan wasan Rugby na Kenya Denis Abukuse ya ɗauki hotuna tare da magoya bayansa bayan wasansu da New Zealand a Australia
A woman stands outside the capitol building wearing a dress modelled after the Liberian flag.

Asalin hoton, MATTHEW JACOBS / AFP

Bayanan hoto, Wannan matar ta ɗaga tutar ƙasar Liberia gabanin jawabin da shugaba Joseph Boakai ya yi a Monrovia ranar Litinin.
People sit at a cafe that has high ceilings and domed blue doors.

Asalin hoton, KHALED DESOUKI / AFP

Bayanan hoto, A ranar Talata a birnin Alƙahira na ƙasar Masar, jama'a na zaune a gidan cin abinci na Umm Kulthum, wanda aka sanya wa sunan marigayiya mawaƙiya, marubuciya kuma jarumar fina-finai ta ƙasar Masar.
Three men in chef's hats and gowns work on intricate pasty dishes.

Asalin hoton, JEFF PACHOUD / AFP

Bayanan hoto, Masu dafa abinci ƴan ƙasar Morrocco Mohamed El Yazidi (hagu) da Omar Eddie (dama) sun fafata a gasar gashe-gashe ta Bocuse d'Or a Faransa ranar Juma'a.
A man immerses himself in a round pool.

Asalin hoton, FETHI BELAID / AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar, wasu wanka sun shaƙata cikin kududdufin ruwan ɗumi a yankin arewa maso gabashin ƙasar Tunisia
A man waves the flags of Kenya and South Africa on Cape Town's waterfront. People hold him up in the air and celebrate with him.

Asalin hoton, RODGER BOSCH / AFP

Bayanan hoto, Kuma a ranar Lahadi, ɗan tseren Japan, "Gump" Suzuki na murnar gudun da ya yi na tsawon watanni shida daga Kenya zuwa Afirka ta Kudu.