Hotunan tufafin kawa na Afirka da za a baje-kolinsu a London
Za a nuna matsayin kayan kawa na Afirka a duniya yayin da za a baje-kolinsu a wurin bikin kayan kawa da gidan adana kayan tarihi na Victoria and Albert (V&A) da ke London zai soma ranar Asabar.
Wata rigar siliki mai kyakkyali da haifaffen kasar Kamaru mai tsara kayan kawa, Imane Ayissi, ya zana ita ce take soma jan hankalin masu shiga zauren baje-kolin:

Asalin hoton, AFRICA FASHION AT THE V&A
Wadannan tufafi ne da suka ki bacewa.
Abu ne "da ke nuna cewa tufafin Afirka gagara gasa ne, fasahar yinsu ta musamman ce", a cewar wata babbar jami'a a gidan adana kayan tarihi na V&A Christine Checinska.
A matsayinta na wacce take lura da sashen tufafi na kayan tarihi na Afirka da kasashen duniya, tana kuma jagorantar wannan baje-kolin.
Ta yi amannar cewa nahiyar Afirka tana da "muhimmiyar rawa da za ta taka a fannin kayan kawa na duniya" kuma baje-kolinda za a yi na tufafi nau'i 250 ya zo "a kan gaba ta nuna muhimmancin irin wadannan kirkire-kirkire".
Za a burge 'yan kallo ta hanyar baje-koli nau'ukan tufafi, hotuna, zane-zane, finfinai da kuma tafiya mai ban sha'awa na asalin 'yan nahiyar.
Shade Thomas-Fahm, wadda ke cikin wannan hoton da aka dauka a Lagos a shekarun 1960, ana bayyana ta a matsayin "Mai sana'ar kayan kawa ta farko 'yar Najeriya":

Asalin hoton, AFRICA FASHION AT THE V&A
Ta yi fice wurin sanya tufafin da aka yi a Najeriya, inda take inganta tufafin gargajiya ta hanyar dinka su tare da wasu nau'ukan tufafin yadda za a gan su kamar na zamani, kamar yadda gidan adana kayan tarihi na V&A ya bayyana.
Wannan ita ce daya daga cikin atamfofin Thomas-Fahm take sanyawa inda ake hada ìró (atamfa), bùbá (riga) da gèlè (gyale) a dinka abin da ake kira aso-òkè, a harshen Yarabanci.

Asalin hoton, AFRICA FASHION AT THE V&A
A yayin da fafutukar neman 'yanci ta karade duniya a tsakiyar karni na 20, mutane sun "rika baje-kolin fasaharsu a fannin kayan kawa da wake-wake da zayyana", a cewar Dr Checinska. Hakan ya fito da "gagarumar fasaha da muradin neman 'yanci ". Wannan tufafin da aka yi auduga da farin karfe a 1988, da ke nuna tufafin kasar Congo mai suna kuba, wanda Alphadi ya dinka:

Asalin hoton, AFRICA FASHION AT THE V&A
An haifi Sidahmed Alphadi Seidnaly a Mali a shekarar 1957, ya girma a Jmhuriyar Nijar kuma ana bayyana shi a matsayin "mai fasaha daga yankn Sahara". Kazalika a yankin na Yammacin Afirka, dan kasar Mali da ke tsara kayan kawa, marigayi Chris Seydou ya yi aiki da shahararru kan kayan kawa irin su Yves Saint Laurent da Paco Rabanne a birnin Paris a shekarun 1970:

Asalin hoton, AFRICA FASHION AT THE V&A
Ya yi fice wajen tallata tufafin Afirka irin su bògòlanfini a fadin duniya, a cewar Dr Checinska. Sai dai a hoton da ke sama, ya yi amfani da tufafin wajen dinka wani tufafi na musamman.
Fitaccen mai tsara kayan kawa na kasar Ghana Kofi Ansah, wanda ya mutu a 2014, shi ma ya yi amfani da irin wadannan tufafin, inda ake rina su wajen yin kaya a Yammacin Afirka da wasu yankuna:

Asalin hoton, AFRICA FASHION AT THE V&A
Ya shahara a haniyar Turai, amma ya koma gida Ghana a shekarun 1990 inda ya kafa wani kamfani na tsare da zana tufafi.
Thomas-Fahm, Alphadi, Seydou da Ansah sun yi shuhura wajen baje-kolin tufafi, inda suke nuna yadda tsarin tufafin zamani na Afirka yake.
Haka kuma irin wannan baje-kolin yana nuna abin da Dr Checinska take kira "sabon tsarin tufafi".
Fitacciyar mai tallata kayan kawa 'yar Najeriya Nkwo Onwuka ta tsara abin da ta kira dakala wanda ke da nufin tattalin tufafi a masana'antar kawa:

Asalin hoton, AFRICA FASHION AT THE V&A










