Dalilai shida da ke haddasa fasa gidajen yari a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 7

A farkon makon nan ne aka samu wani hari kan gidan yarin Keffi da ke jihar Nasarawa a Najeriya, lamarin ya sa fursunoni 16 suka arce, kodayake daga baya hukumomi sun ce sun kama bakwai daga ciki.

Cikin wata sanarwa da hukumar kula da gidajen yarin ƙasar ta fitar, ta ce harin ya yi sanadiyyar raunata jami'an kula da gidan aƙalla biyar, inda biyu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

Sanarwar ta ce ɗaurarrun sun ci ƙarfin maʼaikatan da ke tsaron gidan yarin ne, lamarin da ya bai wa wasu daga ciki damar guduwa nan take.

A makon da ya gabata ne shugaban hukumar kula da gidajen yarin Najeriya, Sylvester Ndidi Nwakuche ya ce akwai ɗaurarru fiye da 81,000 a faɗin gidajen yarin ƙasar, kuma kusan kashi 66 daga cikinsu na zaman jiran shari'a ne.

Fasa gidajen yari wani al'amari da ke neman gararar kundila a Najeriya, inda a wasu lokuta ake samun rahotannin tserewar ɗaurarru, duk kuwa da iƙirarin da gwamnatin ƙasar ke yi na cewa suna ƙoƙarin magance matsalar.

A shekarar 2024 ne Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga shugaban ƙasar ya kafa kwamitin binciken gano abubuwan da ke haddasa yawaitar fasa gidajen yarin ƙasar.

Cikin ƙudirin da majalisar da gabatar ta koka da yawaitar matsalar, tana mai cewa an samu tserewar fursunoni fiye da 7,000 daga gidajen yarin ƙasar daga 2015 zuwa 2023.

Wasu lokuta da aka fasa gidajen yari a Najeriya

  • Koton Karfe - 2025

A watan Maris ɗin 2025, wasu mahara suka far wa gidan yarin Koton Ƙarfe a jihar Kogi mai matsakaicin tsaro.

Maharan sun kashe ɗaya daga cikin jami'an kula da gidajen yarin tare da raunata wasu, lamarin da ya sa fursunoni 12 suka arce, kamar yadda jaridun ƙasar suka ambato a lokacin.

  • Suleja - 2024

Haka ma a watan Afrilun 2024 fiye da fursunoni 100 suka tsere daga gidan yarin Suleje a jihar Neja, bayan da mamakon ruwan sama.

Ruwan saman da aka ɗauki sa'ao masu yawa ana sheƙawa ya kayar da katangar gidan yarin, lamarin da ya bai wa ɗaurarrun damar tserewa.

  • Kuje - 2022

Sannan kuma a watan Yulin 2022, kimanin fursunoni 879 ne suka arce gidan gidan yarin Kuje mai matsakaicin tsaro a Abuja, babban birnin ƙasar.

Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin harin tare da kuɓutar da mambobinta da dama da ke tsare a ciki.

  • Imo - 2021

Sai kuma a watan Afrilun 2021, wasu mahara ɗauke da makamai suka far wa gidan yarin Owerri, babban birnin jihar Imo, inda suka kuɓutar da fursunoni fiye da 1,800.

Rundunar ƴansandan ƙasar ta alaƙanta harin da ƴan ƙungiyar awaren ESN mai alaƙa da IPOB da nufin kuɓutar da mambobinta

  • Kogi - 2021

Kazalika a watan Satumban 2021, aka samu wani mummunan hari kan gidan yarin Kabba da ke jihar Kogi.

A lokacin harin maharan ɗauke da makamai sun kuɓutar da fursunoni 240 daga cikin 294 da ke tsare a gidan.

  • Benin - 2020

Sannan a watan Oktoban 2020, masu zanga-zangar #EndSARS suka far wa gidajen yari Benin da Oko a jihar Edo da ke kudu maso kudancin ƙasar.

A lokacin masu zanga-zangar sun kuɓutar da fursunoni kusan 2,000, waɗanda hukumar kula da gidajen yarin ƙasar ta ce galibinsu an same su da aikata manyan laifuka, ciki har da wadanda ke jiran hukuncin kisa.

  • Ondo - 2020

Haka nan a watan Oktoban 2020, masu zanga-zangar ta #EndSARS sun fasa gidan harin Okitipupa da ke jihar Ondo a kudu maso yammacin ƙasar.

A lokacin fasa gidan yarin masu zanga-zangar sun saki fursunoni aƙalla 58.

Me ke haifar da matsalar?

Barrista Audu Bulama Bukarti, ƙwararren lauya kuma mai bincike kan al'amuran tsaro a ƙasashen Afirka ya bayyana dalilan da ke hadasa matsalar fasa gidajen yari a Najeriya.

Masanin tsaron ya lissafo dalilai biyar da ke haifar da matsalar da suka haɗa da:

Ƙarancin ma'aikatan kula da gidajen

Barista Bukarti ya ce matsala ta farko da ke haifar da fasa gidajen yarin shi ne ƙarancin jami'an da ke kula da fursunonin.

''A yanzu haka akwai kimanin fursunoni 80,000 a gidajen yarin Najeriya, amam abin da zai ba ka mamaki adadin ma'aikatan da ke kula da waɗannan fursunoni ba su fi 20,000'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa cikin wannan adadi na ma'aikata akwai masu aiki a shalkwatar hukumar, akwai masu aiki a ofisoshi, akwai kuma waɗanda suka tafi ƙarin karatu.

''Haka kuma akwai rashin ƙwarewa daga wasu da dama cikin ma'aikatan, musamman ƙananansu'', a cewar Bukarti.

Cunkuson gidajen yari

Cunkuson gidajen yarin Najeriya abu ne da aka jima ana kokawa da shi a Najeriya, inda ake ƙorafi kan yadda gidajen yarin suka cika da mutanen da ke jiran shari'a.

Barista Bukarti ya ce a yanzu kusan kowane gidan yarin Najeriya na ɗauke da dukkan fursunonin da suka zarta adadin da ya kamata a ajiye a cikinsa.

''Ita kanta hukuma ta na maganar cewa kowane gidan kurkukun ƙasar na ɗauke da fursunoni kimanin kashi 130 cikin 100 da ya kamata ya ɗauka'', in ji Dakta Bukarti.

Rashin sabunta gine-ginen gidajen

Rashin sabunta gine-ginen gidajen gidajen yarin na daga cikinmatsalolin da ke haifar da matsalar fasa gidajen yarin Najeriya.

''Da yawa cikin gidajen yarin Najeriya za ka ga an gina su ne tun gomman shekaru da suka gabata, kuma za ka da dama cikin ba a taba zuwa aka yi musu wani gyaran kirki ba'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa hakan ya sa da dama cikin ɗakunan ɗaurarrun sun lalace, ƙarfin bangon gidajen duka sun ragu.

Ƙarancin kayan aiki na zamani

Gidajen yari wuri ne da ya kamata a riƙa sabunta kayan aikinsa sakamakon irin mutane masu cike da hatsari da ake tsare da su a gidajen.

Sai dai Barista Bukarti ya ce ba ahaka batun yake ba a gidajen yarin Najeriya, domin kuwa ba su da irin waɗannan kayan aiki na zamani.

''Ya kamata ace an girke kyamarorin tsaro na zamani wato CCTV Camerars a kowane ɗaki da kan katanga da da hasumiyar tsaro ta zamani da kuma kuma na'urar ankararwa idan akwai wata barazana'', in ji shi.

Cin hanci da rashawa

Wata matsalar da ke haddasa matsalar kuma ita ce ta cin hanci da rashawa a ayyukan hukumar.

Barista Bukarti ya ce ɗaya daga cikin zarge-zargen da aka yi lokacin da aka fasa gidan yarin Kuje shi ne an hada baki da wasu daga cikin ma'aikatan gidan yarin wajen kai harin.

''Misali a gidan yarin Kuje na san lokacin da fursunonin Kuje da aka tsare saboda zargin Boko Haram - ke yin waya da na waje'', in ji shi.

Bukarti ya ƙara da cewa akwai zargin shiga da ƙwayoyi da sauran kayan da doka ba ta amince a shiga da su kurkuku ba.

''Kuma za ka ji duk fashe-fashen gidajen yarin da aka samu a Najeriya ba inda ka ji an kama wani an bincike shi balle a hukunta shi'', in ji shi.

Rashin kula da walwalar ma'aikatan

Wata matsalar kuma da ke haifar da yawaitar fasa gidajen yari a najeriya ita ce rashin kula da walwalar ma'aikatan gidajen yarin.

Barister Bukarti ya ce ƙarancin albashin ma'aikatan ya sa ba sa mayar da hanakali kan aikinsu na kula da ɗaurarrun.

''Za ka tarar a wasu lokuta wasu ma'aikatan sun shagala da nema wa iyalansu abinci kamar zuwa kasuwanni da gonaki d saboda ƙarancin albashin da gwamnati ke biyansu'', in ji shi.

Me ya kamata a yi don magance matsalar?

Barister Bukarti ya ce abin da ya kamata a yi gwamnati ta mayar da hankali wajen tabbatar da rage cunkoson gidanjen ta hanyar bibiyar shari'ar da ake yi waɗanda ke zaman jiran shari'a domin kammala, waɗanda za a saki a sake su.

''Sannan kuma yana da kyau gwamnati ta zuba kudi wajen saye tare da girke kayan aiki na zamani a gidajen yarin'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa yana da kyau kowane ɗaki na ɗaurarrun a saka kyamarar CCTV sannan a saka a jikin katanga, a kuma amar da na'urar ankararwa da hasumiya mai inganci ta zamani.

''A gyara kowane bango da kofofin shiga domin tsaurara tsaro a ciki'', in ji shi.

Masanin tsaron ya kuma ya kamata gwamnati ta ƙara yawan ama'aikatan gidajen yarin tare da inganta musu albashinsu, ta yadda za su ji dadin yin aikin.

Daga ƙarshe Bukarti ya ce sai kuma a yaƙi cin hanci da rashawa da ake samu tsakanin ma'aikatan gidajen yarin.

''Akwai ma'aikatan da ke karkatar da kuɗaɗen da gwamnati ke ware wa gidajen yarin, yana da kyau a zurfafa bincike a kansu a kuma hukunta su domin ya zama izina ga wasu'', in ji shi.