Rashin yarda, da sauran abubuwan da ke haifar da saɓani tsakanin Nijar da Benin

Asalin hoton, Getty Images/CNSP
A ranar Litinin ne gwamnatin Jamhuriyar Benin da ke Yammacin Afirka ta sanar da rufe ofishin jakadancinta da ke Yamai na Jamhuriyar Nijar, a wani abu da masana ke bayyanawa da taɓarɓarewar alaƙa tsakanin ƙasasashen biyu.
A cewar hukumomin ƙasar ta Benin, sun ɗauki matakin ne bayan wasu lamurra da suka fi ƙarfinsu, kodayake ba ta fitar da wani ƙarin bayani a hukumance kan lamarin ba.
A nata ɓangare ita ma Jamhuriyar Nijar ta mayar da martani kan wannan mataki, in da ta umarci jami'in diflomasiyyar Benin ya saka hannu kan takardar dakatar da aiki, sannan ya bar ƙasar cikin sa'o'i 48.
Lamarin ya faro ne tun bayan da hukumomin Benin suka ɗauki matakin korar shugaban hukumar leƙen asirin Nijar da ke birnin Cotonou da kwamishiniyar ƴansanda da ke ofishin jakadancin Nijar a Cotonou bisa zargin aikata zagon ƙasa.
Inda a ranar 1 ga watan Janairu ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta ayyana Seidou Imourana, babban jami'in diplomasiyyar ofishin jakadancin Benin a matsayin wanda ba a buƙatar zamansa a ƙasar, tare da umartarsa da ficewa daga ƙasar.
Ba wannan ne karo na farko da ƙasashen biyu maƙwabtan juna ke samun tsamin dangantar diplomasiyya tsakaninsu ba.
Ko a shekarar 2024 Jamhuriyar Benin ta yi yunƙurin dakatar da wani shirin Nijar na shimfiɗa bututun mai zuwa ƙasashen waje, lamarin da ya sa gwamnatin Nijar ta ce za ta karkatar da aikin domin bi da ƙasar Chadi.
Ƙasashen biyu dai na zargin juna da aikata zagon-ƙasa, makonni bayan yunƙurin juyin mulki a Benin da bai yi nasara ba, inda wasu kafafon yaɗa labaran Benin suka zargi Nijar da hannu a kitsa juyin mulkin, kodayake babu tartibiyar hujjar da ta tabbatar da hakan.
Tun bayan juyin mulkin Nijar na watan Yulin 2023, aka riƙa samun saɓani tsakanin ƙasashen biyu, masu kusanci da juna.
Me ya janyo taƙaddamar?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mutane da dama kan yi mamakin yadda ƙasashen biyu makusantan juna ke takun-saƙa tsakaninsu, kasancewarsu al'umma iri ɗaya masu al'adu iri ɗaya, to amma me ya janyo musu wannan taƙaddama?
Alkasoum Abdourahmane masanin siyasa da al'amuran yau da kullum a yankin Afirka ta Yamma da ƙasashen Sahel ya ce matsalar ta samo asali ne tun bayan juyin mulkin da aka samu a Jamhuriyar Nijar a 2023.
Masanin diflomasiyyar ya ce matsayar da Benin ta ɗauka na rashin goyon bayan juyin mulkin Nijar na daga cikin abubuwan da suka assasa matsalar.
''Bayan juyin mulkin NIjar ta yanke duk wata hulda da ƙasashen Yamma, to amma ita Benin sai ma ta ƙara ƙarfafa alaƙar kawancenta da ƙasashen musamman Faransa, wani abu da Nijar ke kallo a matsayin barazana gareta'', in ji shi.
Alkasoum Abdourahmane ya ƙara da cewa yadda Benin ta haɗa kai da Ecowas wajen yi wa Nijar barazana da yunƙurin kai mata hari, shi ma ya taimaka wajen taɓarɓarewar alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.
Wace illar taɓarɓarwar alaƙar ke janyo musu?

Asalin hoton, Getty Images
Alkassoum Abdourahmane ya ce rashin kyawun alaƙa tsakanin ƙasashen biyu na haifar musu mummunar illa, da ya ce tuni ta samu.
Masanin ya ce ta fuskar kasuwanci da tattalin arziki taɓarɓarewar alaƙar na haifar wa ƙasashen biyu mummunart asara.
''Kusan a iya cewa Jamhuriyar Benin ba ta da wata ƙasa abokiyar kasuwanci da take amfani da tasoshin jiragen ruwanta kamar Nijar, kuma akwai wasu ƙasashen Afirka kamar Najeriya da Chadi da ma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadanda duka ta NIjar kayayyakinsu ke biyowa''.
Ya ƙara da cewa sakamakon taɓarɓarewar alaƙar kasashen biyu an daina sauke wa Nijar kaya a tashar ruwan ta Benin.
''Kuma hakan ya haifar wa ƙasashen biyu asarar maƙudan kuɗaɗen shiga'', in ji shi.
Haka ma wasu masanan na ganin cewa rashin kyawun alaƙa tsakanin ƙasashen biyu na shafar yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin masu aikata laifuka a cikin ƙasashen biyu da ke maƙwabtaka da juna.
''Kuma wannan na daga cikin manyan illolin da wannan takun saƙa zai haifar wa ƙasashen biyu'', a cewar Alkassoum.
Ya ƙara da cewa akwai iyakokin ƙasashe uku zuwa huɗu a kan iyakar ƙasashen.
''Akwai iyakar Nijar da Benin da kuma Najeriya, haka ma akwai iyakar Benin da NIjar da kuma Burkina Faso, kuma rashin haɗin kan ƙasashen zai shafi aikin tsaron haɗin gwiwa a kan iyakokin'', kamar yadda ya bayyana.
Me ya kamata ƙasashen biyu su yi?
Abdollay Mustafa masanin harkokin diplosamiiya a jamhuriyar Nijar ya ce abinda ya kamata ƙasashen biyu su yi shi ne shugabannin su zauna wuri guda domin warware matsalar.
''Ya kamata shugabannin ƙasshen biyu su zauna su fahimci juna tsakaninsu da Allah, idan ana batun diplomasiyya sai an kawo batun yarda da juan an kuma kawar da zargi'', in ji shi.
Ahmadou Danƙware mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Nijar ya kuma shaida wa BBC cewa ya kamata shugabannin ƙasashen biyu su kalli al'umomin da ke wahala a cikin wannan al'amari.
''Yana da kyau shugabannin biyu su fahimci cewa duka al'umominsu na cikin wani ƙangi na wahala sakamakon wannan matsala, domin warware matsalar, tun da ai ko yaƙi ma ana yin sulhu'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Alkassoum Abdurrahman ya ce babu wata hanya da ta fi da lalama wajen warware matsaloli.
''Ya kamata ƙasashen biyu su zauna su cire mummunan zato da zargi tsakaninsu, domin magance wannan matsalar da ke janyo musu asara ta fuskar tattalin arziki da tsaro'', in ji shi.










