Abu bakwai da shugaban Nijar ya faɗa kan matsalar tsaro

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya kai ziyarar kwanaki biyu a jihar Tillabery, wurin da hare-haren ƙungiyoyin masu da'awar jihadi ya daidaita.

Shugaban ya samu rakiyar wata babbar tawaga da suka haɗa da ƙaramin ministan ƙasar kuma ministan tsaron ƙasar Salifou Mody, da babban hafsan hafsoshin soji, Moussa Salao Barmou, da sauran membobin gwamnati da na majalisar CNSP da wasu shuwagabanin hukumomi da ma'aikatu na gwamnati.

A yayin ziyararsa, shugaban ya ziyarci dakarun tsaron ƙasar da ke aikin tsaron ƙasar da al'umma wani matakin da yan ƙasar suka yaba da shi.

Hakazalika, shugaban ya yi muhimman jawaban da suka shafi tsaro da hadin kan al'umma da kuma matsin lambar da ƙasarsa ke fuskanta.

Ga manyan batutuwan da ya jaddada:

Haɗin kai da Zaman Lafiya

Shugaban ya yi kira ga al'ummar ƙasar da su tashi tsaye domin samar da zaman lafiya, da tallafawa dakarun tsaro da kuma nuna jajircewa wajen tinkarar kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin da ma ƙasar baki ɗaya.

Ƙoƙarin jami'an tsaro

Shugaba Tchiani ya yaba da jajircewar dakarun tsaron ƙasar da ke fafutukar yakar 'yan bindiga da masu tada zaune tsaye. Ya ce kokarinsu ya zama abin koyi kuma ya cancanci goyon bayan al'umma baki ɗaya.

Zarge-zarge

Ya bayyana cewa akwai maƙiyan Nijar da ke ƙoƙarin tada zaune tsaye ta hanyar ba da horo da kuɗi da kuma kayan aiki ga ƙungiyoyin masu da'awar jihadi domin ƙara dagula lamarin tsaro a ƙasar.

Jama'a su tashi tsaye

Janar Tchiani ya buƙaci jama'a su tallafa wa jami'an tsaro ta hanyar addu'a, taimako na zahiri da kuma bayar da gudummawa ga asusu na musamman na hadin kai, wanda aka ƙaddamar domin karfafa kayan aikin sojoji wajen yaƙi da ta'addanci.

Takunkuman da aka saka wa Nijar

Shugaban ya yi ƙarin haske kan matakan da gwamnatin Nijar ta ɗauka don rage illar takunkumin ƙasashen waje. Ya jaddada cewa duk da wahalhalun da ake fuskanta, Nijar ta ci gaba da nuna turjiya saboda imanin al'umma da haɗin kan su.

Sauyin ɗabi'u

Shugaban ya kuma shawarci al'umma da kada su tsaya cak saboda ƙalubale, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum tare da sauya wasu dabi'un da ba su da amfani domin cigaban ƙasa.

Zargin Faransa da yaɗa labaran ƙarya

Janar Tchiani ya yi zargin cewa Faransa na kitsa wani shiri na musamman na yaɗa labaran ƙarya domin tada hankalin jama'a a ƙasashen AES (ƙungiyar ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar). Ya ce ana amfani da shafukan sada zumunta wajen yada waɗannan labaran don kawo ruɗani da rashin jituwa a tsakanin jama'a.

Ya ƙara da cewa, duk waɗannan ƙalubale za su ci tura ne idan al'ummar Nijar suka ci gaba da zama cikin jituwa, haɗin kai da kuma kishin ƙasa.