Me ya sa aka fi tsangwamar mata a intanet, ta yaya za su kare kansu?

Lokacin karatu: Minti 5

Zalunci a shafukan sada zumunta na ɗaya daga cikin abubuwan da ke korar mata daga intanet gaba ɗaya. Miliyoyin mata na fuskantar tsangwama duk shekara saboda sa-ido da tsokana.

Akwai kusan mutum biliyan shida da ke amfani da intanet a duniya, kuma akwai maza miliyan 280 fiye da mata da suke amfani da ita a shekarar nan, a cewar cibiyar International Telecommunication Union mai alaƙa da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

Mata da 'yanmata da waɗanda ba su yarda da jinsi ba sun fi shiga haɗari kuma sun fi samun matsala ta tsawon lokaci saboda jinsinsu, in ji MDD.

Bincike ya gano cewa akwai kusan kashi 58 cikin 100 na mata da 'yanmata da ake kai wa hari a intanet, a cewar sashen harkokin mata na MDD.

Nau'i biyar na tsangwama da aka fi yi ta intanet

1. Tsokana (Trolling)

Tsokana ko kuma trolling a Turance, shi ne wallafa abubuwan tsokana da gangan a intanet da zimmar ɓata wa wani rai, ko tunzura shi, ko haddasa fitina.

Akwai manyan nau'o'in tsokana biyu, kamar yadda cibiyar Centre for Countering Digital Hate (CCDH) mai mazauni a Birtaniya da Amurka ta bayyana.

  • Tsakona kan shahararrun mutane masu mabiya da yawa a dandalin sada zumunta
  • Tsokana ta hanyar yin murna da abin cutarwa da ya faru da wani

Akwai dalilai da yawa da ke jawo tsokana a intanet, kuma yanayin tsokanar kan sha bamban da saura.

Masu tsokanar na samun biyan buƙata ne idan ran wanda suke kai wa hari ya ɓaci, saboda haka idan ya mayar da martani sai su ƙara samun ƙwarin gwiwa.

Tsokana irin wannan kan haifar da damuwa mai tsanani da kuma tunanin ƙasƙanci a zukatan mutanen da aka yi wa.

2. Fallasa

Fallasa ko kuma doxing a Turance na nufin fallasa wasu bayanai game da mutum a intanet da zimmar ɓata masa suna da gangan.

Yakan jawo matsaloli ga rayuwar mutum a fili. A 2021, marubuciyar littafin Harry Potter, JK Rowling, an aikata mata hakan - bayan wallafa wani hoto a intanet da aka ɗauka a ƙofar gidanta ɗauke da adireshinta.

Amma 'yansanda sun ce babu wani mataki da za a ɗauka kan waɗanda suka aikata hakan.

Tun daga Afrilun 2022, Facebook da Instagram - mallakar kamfanin Meta - sun haramta yaɗa adireshin gida na wani mutum daban ko da kuwa akwai shi a fili ko a labarai. Kowane mutum zai iya wallafa adireshinsa amma an hana wani ya yaɗa na wani.

3. Hotuna da bidiyon ƙarya

Ana yawan yaɗa hotuna da bidiyo da sauti masu kama da na gaske da ake ƙirƙira da wasu manhajoji, waɗanda ake kira deepfake.

Akan yi amfani da su saboda nishaɗi, ko wani binciken kimiyya. Amma wani zubin akan yi amfani da su wajen yin sojan gona da wasu mutane kamar 'yansiyasa, da shugabannin duniya domin juya tunanin mutane da gangan.

Akan yi kuma amfani da su wajen ƙirƙirar bidiyo da hotunan batsa na wasu shahararru ko kuma game-garin mutane.

Yaɗawa ko kuma yi wa mutum barazanar fitar da hotunansa na batsa ba tare da amincewarsa ba laifi ne a Birtaniya. Akan hukunta mai laifin ƙarƙashin dokar Online Safety Act 2023, wadda ta ƙunshi hotuna da bidiyon da aka jirkita, ciki har da deepfake.

4. Yaudara

Akan kai wa yara da 'yanmata hari ta hanyar rainonsu kafin daga baya a yaudare su ta intanet. Miyagun kan yi amfani da shafukan zumunta domin neman yarda da amincewar yaro ko yarinya domin yaudarar su daga baya.

Tsangwamar kan faru ta intanet, ko kuma azzalumin ya shirya haɗuwa da yaran da zimmar cutar da su. Zai kuma iya ɗaukar hoto ko bidiyo nasu domin ya wallafa a intanet.

Ko a fili ko kuma a intanet, idan lamarin ya faru, abin kan haifar da matsala ta tsawon lokaci a tunanin yaro, inda wasu kan kashe kansu daga baya.

5. Tsangwama

Tsangwama ta intanet na faruwa ne lokacin da wasu ke uzura masa a shafukan sada zumunta, ko dandalin aika saƙonni, ko na wasan game.

Akan tsangwami mutum a fili ko a intanet a lokaci guda, kuma wani lokacin mai tsangwamar sananne ne ga wanda aka tsangwama.

Abu ne mai sauƙi kuma mutum ya fuskanci tsangwama daga mutanen da bai taɓa gani ba ma.

Wani lokacin kuma, mai tsangwamar kan ɓoye kansa kwatakwata.

Yadda za ku kare kai

Ga wasu matakai da za su taimaka wajen rage haɗurran faɗawa tarkon miyagu, kamar yadda MDD ta zayyana:

  • Ku yi tunani da kyau kafin wallafa duk wani abu a intanet - zai iya zama har abada kuma za a iya yin amfani da shi domin a cutar da ku nan gaba
  • Ku rage yawan bayanan da kuke sakawa a intanet, musamman bayanan da suka shafi kanku da kanku kamar adireshi, da lambar waya
  • Ku gargaɗi abokai da 'yan'uwanku da kada su wallafa bayananku
  • Ku nazarci tsarin kiyaye bayanan sirri na dandalin zumuntar da kuke amfani da shi, ciki har da wane ne zai iya ganin bayananku da yadda za ku iya ɓoye bayanan bayan wallafa su
  • Kashe zaɓin gane wurin da kuke wato geo-location
  • Kai rahoton mutanen da kuke zargin suna da haɗari