Kompany yana cikin kociyan da Bayern Munich ke son dauka

Kociyan Burnley, Vincent Kompany yana cikin masu horar da tamaula da ake cewa watakila Bayern Munich ta dauka a matakin sabon wanda zai ja ragamar ƙungiyar.

Kompany da Bayern Munich sun tattauna a tsakaninsu a baya, amma ba a fayyace inda suka tsaya ba, sansan ba a san ko za su kai ga cimma kwantiragi ba.

Ƙungiyar dake buga Bundesliga na neman wanda zai maye gurbin Thomas Tuchel, wanda cikin Fabrairu ya sanar da zai ajiye aikin da zarar an kammala kakar nan.

Kociyan Bayer Leverkusen, Xabi Alonso da na tawagar Jamus, Julian Nagelsmann da na Austria, Ralf Rangnick duk sun ki amincewa da tayin da aka yi musu.

Haka kuma an kasa rarrashin Tuchel ya sauya shawara, amma hakan bai yiwuba, hakan ya sa ƙungiyar take ta neman kociyan da ya kamata ta dauka.

Kompany ya taka rawar gani a lokacin da ya horar a Anderlecht da kuma Burnley, wadda ya kai gasar Premier League a bara daga Championship a kakar farko.

Ko da yake ta kasa taka rawar gani a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana, wadda ta kare a mataki na biyun karshe, ke nan za ta koma buga Championship a badi.

Haka kuma ƙungiyar dake buga Bundesliga na tuna rawar da ɗan kwallon ya taka a Hamburg lokacin da yake taka leda, sannan yana jin harshen Jamus.

Idan har lallai Bayern na son ɗaukar Kompany, tana bukatar gabatar da yarjejeniya mai tsoka, bayan da ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyar a Burnley a 2023.

Kociyan bai fayyace makomarsa a Burnley ba lokacin da ƴan jarida suka yi masa tambaya ranar Lahadi bayan tashi a wasan karshe da Nottingham Forest.

Bayern Munich ta karkare kakar bana ba tare da lashe kofi ba karkashin Tuchel da yin ta uku a teburin Bundesliga da Leverkusen ta lashe, Stuttgard ta yi ta biyu.