Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda karatun addinin ya zamo zaɓi ɗaya tilo ga matan Afghanistan
- Marubuci, Mahjooba Nowrouzi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan Service, Kabul
- Lokacin karatu: Minti 6
Amina ba za ta taba mantawa da lokacin da yaruntarta ta canza ba. Tana 'yar shekara 12 kacal, aka shaida hana ta zuwa makaranta akasin sauran ‘yan’uwanta yara maza.
Sabuwar shekarar karatu a Afghanistan ta fara ne ranar Asabar, 22 ga watan Maris, amma shekaru hudu a jere ke nan, da hana 'yanmatan da suka haura shekaru 12 zuwa makaranta.
"Burina na rayuwa ya watse'' in ji ta cikin murya mai sanyi.
Amina, yanzu tana da shekaru 15, tana son zama likita. Tun tana karama, ta yi fama da ciwon zuciya kuma an yi mata tiyata tana da shekara takwas. Likitar da ta ceci rayuwarta mace ce, har yanzu tana tunawa da ita, kuma ta karfafa mata gwiwa wajen daukar karatunta da muhimmanci.
Amma a shekarar 202, lokacin da Taliban ta sake karbe mulki a Afghanistan, ba zato ba tsammani burinta ya tsaya cik. Sabuwar gwamnatin ta haramta wa 'yanmatan da suka haura shekaru 12 zuwa makarantu, lamarin da ya sauya rayuwar dubban mutane irin ta.
"Lokacin da mahaifina ya gaya mani cewa an rufe makarantun, na yi baƙin ciki sosai. Wannan mummunan yanayi ne," in ji ta a hankali. "Na so in yi karatu domin in zama likita."
Na hadu da Amina a wani wuri da babu haske sosai a wata Islamiyya da ake koyar da Hadisi, a Kabul, sabuwar makaranta ce da aka samar ga kimanin mata 280 masu mabanbantan shekaru.
Akwai sanyi sosai a wajen, bayan mun yi magana kamar ta tsawon dakika goma haka, gaba daya sai sanyi ya addabi kafafuwanmu.
Wani dan‘uwan Amina, Hamid ne ya samar da Islamiyyar shekara daya da ta gabata cikin ɗimbin haske na madrassa Al-Hadith a Kabul, sabuwar cibiyar koyar da ilimin addini mai zaman kanta ga ɗalibai mata kusan 280 masu shekaru daban-daban.
An kafa makarantar ta Al-Hadith shekara guda da ta gabata a hannun dan‘uwan Amina, Hamid, wanda a ransa, ya ji dole ya dauki wannan mataki bayan ya ga irin illar da haramcin ilimi ya yi mata.
"Lokacin da aka hana 'yanmata karatu, sai burin 'yar'uwata na zama likitar zuciya ya rushe, wanda hakan ya shafi lafiyarta sosai," in ji shi.
Ya kara da cewa "Samun damar komawa makaranta, da kuma koyon aikin ungozoma da taimakon gaggawa, ya sa ta ji dadi game da makomarta."
A Afganistan, makarantun Islamiyya da cibiyoyin addini na mayar da hankali kan koyarwar Musulunci, sun zama hanya ɗaya tilo ga mata da 'yanmata matasa za su iya samun kowane nau'i na ilimi.
Takunkumin da kungiyar Taliban ta kakaba, ya shafi 'yanmata sama da miliyan daya, a cewar asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef.
Afganistan ta kasance kasa daya tilo a duniya da aka sanya irin wannan haramcin.
Lokacin da Taliban ta karbi mulki a shekarar 2021, sun ba da shawarar haramta karatun 'ya'ya mata na wucin gadi ne, har sai an cika wasu sharudda.
Duk da haka, ba a sami wani ci gaba na sake buɗe makarantun manyan 'yan mata ba a cikin shekarun da suka gabata.
Kafin komawar Taliban, an yi imanin adadin makarantun da aka yi wa rajista ya kai kusan 5,000.
Yayin da makarantun firamare ke ba da ilimin addini, tun bayan hana manyan makarantu, wasu sun ce sun faɗaɗa koyar da darussa kamar harsuna da kimiyya.
Hamid ya ce ya himmatu wajen samar da ilimi wanda ya hada da na addini da sauran darussa na ilimi ga 'yanmatan da suka isa karatun makarantar sakandare.
"Yin hulɗa da wasu 'yanmata ya sa 'yar'uwata ta fi farin ciki," in ji shi cikin murmushi, yana alfahari da juriyar 'yar uwarsa.
Sai dai karatun ilimin likitancin da 'yar uwata ke yi wata shidda kawai ya dauka, kafin Taliban ta sanar da daukar wannan mataki. Yanzu, mafarkin Amina ya ruguje.
Damarmakin da mata ke da su na yin karatu na ci gaba da wargajewa a Afghanistan. Wasu makarantu kudinsu ya yi tsada, don haka irin wadannan makarantu ne suke zama zabinsu.
BBC ta ziyarci wasu makarantu na mata biyu masu zaman kansu a Kabul.
Wata Islamiyya ta Shaikh Abdul Qadr Jilani da ke birnin Kabul tana koyar da 'yanmata sama da 1,800 daga shekaru biyar zuwa 45. Ana gudanar da azuzuwan ne ta hanyar karfin basirar dalibai maimakon shekaru. Mun samu damar ziyartar makarantar ƙarƙashin kulawar tsaro mai tsauri.
Kamar Islamiyyar nan ta Al-hadath, nan ma da sanyi sosai. Ginin mai hawa uku ba shi da wata matsala, wasu ajujuwa kuma babu kofofi da tagogi.
A wani katon daki, ana koyar da karatun Kur'ani, sannan a kuma a koyar da dinki daga bisani, yayin da wasu gungun 'yanmata sanye da hijabi da abun rufe fuska suka yi zaman dirshan a kan kafet.
Makarantar Shaikh Abdul Qadr Jilani ta kasu kashi biyu. Bangaren da ake koyar da darussan na yau da kullum, da kuma bangaren Islamiyya da ake koyar da karatun addini, da sana'o’in dogaro da kai.
Hadiya mai shekaru 20 a duniya kwanan nan ta kammala karatunta a makarantar, inda ta karanci darussa da dama ciki har da Lissafi, da Physics, da Chemistry, da Geography.
Ta yi magana sosai game da sanadarai da physics. "Ina son kimiyya. Musaman ilimin da ya shafi kwayoyin halitta da kuma yadda kimiyya ta shafi duniyar da ke kewaye da ni," in ji ta.
A yanzu Hadiya tana karantar da kur'ani a makarantar, kamar yadda ta shaida min.
Safiya, kuma mai shekaru 20, tana koyar da yaren Pashto a makarantar Al-Hadith. Ta yi imanin cewa ya kamata 'yanmata a cibiyoyin addini su inganta abin da ta bayyana a matsayin ci gaban kansu.
Ta mayar da hankali kan Fiqhu, tsarin shari'ar Musulunci mai mahimmanci ga ayyukan Musulmi na yau da kullun.
"Ba a shigar da Fiqhu a manyan makarantu ko jami'o'i. A matsayinta ta mace musulma, karatun Fiqhu yana da matukar muhimmanci ga ci gaban mata," in ji ta.
Duk da haka, ta kara da cewa irin wadannan makarantu "ba za su iya zama madadin manyan makarantu da jami'o'i ba".
"Cibiyoyin ilimi, ciki har da manyan makarantu da jami'o'i, suna da matuƙar mahimmanci ga al'ummarmu. Rufe waɗannan cibiyoyin zai haifar da raguwar ilimi a hankali a cikin Afghanistan," in ji ta.
Tawqa, mai shekaru 13, shiru-shiru ce, ba ta fiye yawan magana ba, kuma tana karatu a makarantar Shaikh Abdul Qadr Jilani. Ta fito ne daga dangin mutane masu addini, tana zuwa makaranta tare da yayarta.
"Na fi son darussan addini" in ji ta. "Ina son koyon irin hijabin da ya kamata mace ta sanya, da yadda za ta rika mu'amala da danginta, da yadda za ta kyautata wa dan‘uwanta da mijinta, kada a yi musu rashin kunya."
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kare hakkin dan’adam a kasar Afghanistan, Richard Bennett, ya nuna matukar damuwa game da matakin da kungiyar Taliban ta dauka na takura wa tsarin ilimi.
Ya kuma jaddada bukatar dawo da guraben karatu ga 'yanmata da suka wuce aji shida da kuma mata masu zuwa manyan makarantu.
Mista Bennett ya yi gargadin cewa wannan takaitaccen ilimi, hade da rashin aikin yi da talauci, "zai iya haifar da akidu masu tsattsauran ra'ayi da kuma kara hadarin ta'addanci a cikin gida, da barazana ga zaman lafiyar yankin da na duniya baki daya".
Ma'aikatar ilimi ta Taliban ta yi iƙirarin cewa kusan ɗalibai miliyan uku a Afganistan suna shiga cikin waɗannan cibiyoyin koyar da addini.
Sai dai wani rahoto da aka fitar a watan Janairun 2025 na Kungiyar kare hakkin bil’adama na Afghanistan ya nuna cewa akwai yiwuwar yawan zai iya zarta haka.
Kuma ya bayyana cewa ana amfani da wadannan makarantun Islamiyya wajen yada akidojin Taliban.
Rahoton ya kuma yi zargin cewa an sanya “akidojin tsattsauran ra’ayi” a cikin manhajar wadannan makarantu.
Afghanistan a yanzu ta kasance kasa daya tilo inda aka haramta wa mata da ‘yanmata zuwa makarantun sakandare da kuma na gaba da sakandare.
Kungiyar Taliban ta yi alkawarin sake bude makarantun boko na mata amma bisa wasu sharudda, kamar sanya manhajar karatun addinin “Islama”, to amma har yanzu ba ta cika wannan alkawari ba.
Cibiyar kare hakkin bil’adama ta Afghanistan ta bayyana haramcin ilimin matan a matsayin “wani tsararren karan-tsaye” ga ‘yancin yara mata na samun ingantaccen ilimi.
Duk kalubalen da Amina ta fuskanta - na abin da ya shafi lafiyarta da haramcin karatun boko - har yanzu tana da kwarin gwiwa.
“Ina da yakinin cewa wata rana Taliban za ta sake bude mana kofofin shiga makarantu da jami’o’i,” in ji ta. “Kuma zan cimma burina na zama likitar zuciya.”