Gwamnonin Najeriya biyar da kotu ta wanke bayan zargin rashawa

Asalin hoton, FB/Multiple
Babbar Kotu a Legas ta wanke tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a shari'ar halasta kuɗaɗen haram da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar da shi a gaban kotu
A ranar 16 ga Yuli, 2025, kotu ta bayyana cewa Fayose bai aikata laifin da ake zargin sa da shi ba, na sama da faɗi da kuɗi haram har naira biliyan biyu.
Fayose ya shafe shekaru yana fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa lokacin da yake gwamna, amma kotu ta yanke hukunci cewa babu isassun hujjoji da ke tabbatar da laifinsa.

Asalin hoton, Ayodele Fayose
Alƙali ya bayyana cewa "binciken da masu gabatar da ƙara suka yi bai nuna alaƙar da ke tsakanin wanda ake tuhuma da laifukan da ake zarginsa da su ba, ta yadda kotu za ta ga dacewar kiran sa domin ya ba da bahadi."
Tun da farko, kotun ta ba wa Fayose izinin fita ƙasar waje domin jinya bayan ya roƙi hakan.
Amma kuma, Fayose ba shi ne gwamna na farko da ya fuskanci shari'a kan zargin cin hanci a Najeriya ba inda kuma kotu ko dai ta wanke su ko kuma ta bayyana su a matsayin marasa laifi.
Baya ga Fayose, ga wasu gwamnonin Najeriya da aka gurfanar da su bisa zargin cin hanci da rashawa amma suka kauce wa hukunci ba tare da an same su da laifi ba.
Rashidi Ladoja – Tsohon gwamnan jihar Oyo

Asalin hoton, @Omojuwa
Shari'ar da EFCC ta shigar kan tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, dangane da halasta kuɗaɗen haram, ta ɗauki shekaru goma sha ɗaya kafin kotu ta wanke shi.
A shekarar 2008, EFCC ta zargi Ladoja da kwamishinansa na Kuɗi, Waheed Akanbi, da karkatar da sama da naira biliyan biyar.
A lokacin sauraron shari'ar, kotu ta bayyana cewa EFCC ta kasa gabatar da hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da laifin Ladoja da Akanbi.
Alƙali ya ce bayanan da shaidu shida na EFCC suka bayar duk da cewa ba su halarci kotu ba — sun saɓawa juna.
Ya ƙara da cewa zarge-zargen da ake yi wa Ladoja ba su da tushe, kuma ya kamata a gudanar da bincike sosai kafin a tuhumi wani da cin hanci.
Sule Lamido – Tsohon gwamnar jihar Jigawa

Asalin hoton, Sule Lamido
Sule Lamido ya kasance gwamnan jihar Jigawa, ɗaya daga cikin jihohi da suka fi talauci a jihohin Najeriya, daga shekarar 2007 zuwa 2015.
Daga cikin zarge-zargen da aka yi masa har da karɓar cin hanci daga wasu kamfanoni kafin ya aiwatar musu da ayyukan gwamnati.
A shekarar 2015, EFCC ta gurfanar da shi tare da 'ya'yansa biyu — Aminu da Mustapha — bisa tuhume-tuhume 37 da suka kai kimanin naira biliyan 1.35.
Bayan shekara takwas ana sauraron shari'ar tare da yawan ɗage ta, kotu ta yi watsi da ƙarar a shekarar 2023 bisa hujjar cewa ya kamata a saurari shari'ar ne a jihar Jigawa, ba a Abuja ba.
A maimakon kotu ta mayar da shari'ar zuwa Jigawa, sai ta yi watsi da ƙarar gaba ɗaya kawai, kuma duk ƙoƙarin EFCC na sake ɗaukaka ƙara ya ci tura.
Danjuma Goje – Tsohon gwamnan jihar Gombe

Asalin hoton, Danjuma Goje
Danjuma Goje ya kasance gwamnan jihar Gombe daga shekarar 2003 zuwa 2011, kuma an zarge shi da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai naira biliyan 25.
EFCC ta fara tuhumarsa ne a shekarar 2012, duk da cewa ɗalibai sun yi kira da a yi watsi da ƙarar bisa dalilai na doka.
Amma a shekarar 2019, bayan Goje ya janye daga neman kujerar shugaban majalisar dattawa domin mara wa marigayi Muhammadu Buhari baya, EFCC ta shigar da ƙara a gaban babban alƙalin Najeriya.
Ba da daɗewa ba, babban alkalin ya yi amfani da ikon doka wajen watsi da ƙarar, duk da cewa EFCC ta kira shaidu 25.
Kuma har zuwa yau, wannan shari'ar ta zama tarihi kawai.
Orji Uzor Kalu – Tsohon gwamnan jihar Abia

Asalin hoton, @DailyPostNGR
Orji Uzor Kalu ya yi mulkin Jihar Abia daga shekarar 1999 zuwa 2007. A shekarar 2007 ne EFCC ta ƙwace kuɗi kusan naira biliyan bakwai daga hannunsa.
Bayan shari'ar da ta ɗauki shekaru goma sha biyu, kotu ta yanke masa hukuncin dauri na shekaru goma sha biyu a 2019. Amma a 2020, Kotun Koli ta soke hukuncin, bisa hujjar cewa alƙalin da ya yanke hukuncin ya samu ƙarin girma kafin yanke hukuncin, don haka ba shi da hurumin ci gaba da sauraron shari'ar.
Hukumar EFCC ta ƙoƙarta domin sake buɗe shari'ar, amma duk ƙoƙarinta ya ci tura sakamakon rashin wasu muhimman takardu da gwamnatin tarayya ta gaza samarwa.
Yanzu haka, Orji Uzor Kalu na zaune a majalisar dattawa a matsayin ɗaya daga cikin 'yan majalisar dokokin Najeriya.
Peter Odili – Tsohon gwamnan jihar Rivers

Asalin hoton, @Real_AmakaIke
Peter Odili ya gwamnaci jihar Rivers daga shekarar 1999 zuwa 2007, inda sunansa ya shahara har sai lokacin da EFCC ta kama shi bisa zargin satar ɗaruruwan miliyoyin naira.
Duk da girman zarge-zargen, har yanzu ba a fara shari'a a kansa ba.
Wannan yana faruwa ne duk da hukuncin da kotu ta yanke a shekarar 2007 cewa EFCC ba ta da ikon bincike ko gurfanar da shi.











