Gasar Kofin Duniya : Shugaban Liberia ya harzuka 'yan kasarsa

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Liberia na nuna ɓacin rai da rashin yarda bayan da Shugaban kasar George Weah ya shirya wani bulaguro na shafe kwana 9 don halartar Gasar Cin Kofin Duniya ta kwallon kafa a Qatar.
Za a fara gasar ne ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba 2022 a kuma kare, ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba 2022.
Shugaban wanda tsohon ɗan ƙwallon ƙafa ne, ya bar Liberiya a cikin makon jiya don ziyarar ƙasashen waje, inda daga bisani zai tafi kallon gasar ta duniya a Qatar, ko da yake ba a bayyana duk wuraren da zai ziyarta ba.
Labarin shirye-shiryen ziyarar da Shugaban ya fara a ƙasashen wajen, ya fusata 'yan kasarsa masu yawa, inda wasu suka shiga sukar lamirinsa a kafofin sada zumunta da muhawara gidajen rediyon ƙasar.
Wasu na cewa, rashin tausayi ne ga Shugaba Weah ya sa ƙafa ya fice daga ƙasar zuwa kallon Gasar cin Kofin Duniya a daidai lokacin da mutane da yawa ke fama da matsalar tsadar kayan abinci da kuma rashin tabbas kan aikin ƙidayar jama'ar ƙasar da aka sha ɗagawa.
Karo na shida ke nan da George Weah ya jingine aikin a baya-bayan nan.
Ɗan George Weah mai suna Timothy wanda Ba'amurke ne, yana cikin 'yan wasan tawagar Amurka da za ta je Gasar Kofin Duniyar.
Tsohon gwarzon ɗan ƙwallon ya taɓa buga wa manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turai ciki har da AC Milan da Chelsea.
A shekara ta 2017 ne aka zaɓe shi matsayin Shugaban Liberiya bayan ya canza sana'a inda ya shiga siyasa.
Kafin ya zama shugaban kasa a 2018, dan majaliar dattawa ne mai wakiltar mazabar Montserrado County.
Jami'an gwamnatin Weah dai waɗanda ba su amsa tambayoyi game da kuɗin da shugaban zai kashe a lokacin wannan ziyara ba, sun mayar da martani a kan masu sukar lamirinsa.
Sun ce ziyarar shugaban ƙasar a ƙasashen waje za ta haifar wa Liberiya ɗumbin alheri.











