Dalilai biyar da suka sa duniya ta damu da juyin mulkin Nijar

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Yusuf Akinpelu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Lagos
Juyin mulkin sojin Nijar ya haifar da rashin jituwa tsakanin ƙasashen Afirka makwabta, musamman yadda ƙungiyar Ecowas ta ƙaƙaba jerin takunkumai kan ƙasar wadda ke yankin Sahel.
Nijar ce ƙasa ta baya-bayan nan a yankin yammacin Afirka da sojoji suka ƙwace mulki, bayan Burkina Faso da Mali, cikin shekara uku da suka gabata.
Yanayin da Nijar din ke ciki na ci gaba da damun yankin Sahel da ma duniya baki ɗaya.
Ƙaruwar tawaye
Nijar ta kasance cikin ƙasashen da aka bari a baya ta fuskar dimokuradiyya a yankin Sahel.
Ƙasashen Yamma na yi mata kallon gidan zaman lafiya a yankin - wanda ke fama da ƙaruwar tashe-tashen hankuli da hare-haren 'yan tawaye a baya-bayan nan.
Amma a yanzu da sojoji suka ƙwace mulki a ƙasar, akwai fargaba game da zaman lafiya a ƙasar.
Akwai sansanin sojin Amurka da na Faransa a Nijar, waɗanda ke taimaka wa wajen yaƙar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da ISIS.
Kawo yanzu dai ba a san makomar sojojin na ƙasashen Yamma ba.
Juyin mulkin da aka samu a Mali da Burkina Faso sun haifar da ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi.
Akwai kuma fargabar cewa ire-iren waɗannan hare-hare za su ɓulla a Nijar.
Ƙaruwar ɗabi'ar juyin mulki
Juyin mulkin na Nijar na nufin cewa daga ƙasar Mali a yamma zuwa Sudan a gabashi, ilahirin wani zirin ƙasashe a Afirka na ƙarkashin ikon mulkin sojoji.
Ƙaruwar mulkin sojoji a yankin Sahel wani koma-baya ne ga dimokuradiyyar yankin.
Juyin mulkin zai kuma iya ingiza sojoji a wasu ƙasashen domin ƙwace mulki.
Wannan fargabar ce ta sanya ƙungiyar Ecowas sanya jerin takunkumai kan sojojin da suka kifar da gwamnatin, tare da barazanar amfani da ƙarfin soji matuƙar sojojin ba su mayar da Bazoum kan mulki ba.
Wannan matakin ya samu goyon bayan Amurka da tarayyar Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙaruwar tasirin Rasha
Bayan da suka gudanar da juyin mulki, sojojin Burkina Faso da Mali sun ƙulla ƙawance da Rasha. Haka su ma sojojin na Nijar sun bayyana cewa a shirye suke wajen ƙulla irin wannan ƙawance.
Babu wata hujja da ke nuna cewa da hannun Rasha a juyin mulkin Nijar.
Mai magana da yawun fadar gwamnatin Rasha ya yi kira da a saki Shugaba Bazoum domin kauce wa rikici a ƙasar.
Amma masu goyon bayan gwamnatin Rasha sun yaba da juyin mulkin a kafar yaɗa labaran ƙasar da shafukan Telegram.
Masu goyon bayan juyin mulkin sun yi ta ɗaga tutar Rasha tare da yin tofin-Allah-tsine ga Faransa- wadda ta yi wa Nijar mulkin mallaka.
Akwai kuma fargabar cewa ƙungiyar sojojin hayar Rasha ta Wagner za ta faɗaɗa ayyukanta zuwa Nijar ɗin.
Idan Nijar ta bi sawun maƙwabtanta wajen ƙulla ƙawance da Rasha, musamman ƙungiyar Wagner, hakan zai haddasa ƙaruwar hare-hare, da take haƙƙin ɗan Adama tare da sace ma'adinai.
'Makamashin uranium a hannun ɓata-gari'
Nijar ce ke samar da kashi biyar na Uranium a duniya - sinadarin da ake amfani da shi wajen haɗa makamashin nukiliya.
Ta kasance ƙasa ta biyu a duniya da ta fitar da makamashin zuwa Turai a shekarar da ta gabata, kamar yaddaa cibiyar makamashi ta Tarayyar Turai (Euratom) ta bayyana.
Ƙasar kan sayar da kashi 15 cikin 100 na makamashin nata ga ƙasar Faransa.
Euratom ta ce babu wata barazana da Tarayyar Turai za ta samu idan Nijar ta daina fitar da makamashin na Uranium, saboda a cewar cibiyar akwai wadataccen makamashin da zai ishi ƙasashen Turan na kusan aƙalla shekara uku, a rumbunan ajiyar makamashin da ke Turai.
Duk da wannan, Ecowas ko ƙawayenta na ƙasashen Yamma ba za su so makamashin ya faɗa hannun ɓata-gari a yankin da masu iƙirarin jihadi ke cin karensu babu babbaka ba, sannan kuma Rasha da Wagner ke ƙara faɗaɗa tasirinsu a ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Matsalar 'yan ci-rani
Gwamnatin Shugaba Bazoum a baya ta ƙulla ƙawance da ƙasashen Turai wajen hana tuɗaɗar 'yan ci-rani da ke bi ta tekun Baharrum, tare da amincewa da mayar da ɗaruruwan 'yan ci-ranin da ake tsare da su a cibiyoyin tsare 'yan ci-ranin da ke Libya.
Ya kuma kawar da batun safarar ɗan Adam a ƙasar wadda ta zama wata cibiya ta safarar mutane tsakanin ƙasashen Afirka ta Yamma da na Arewacin Afirka.
A ƙarƙashin mulkin soji wannan yunƙuri ka iya samun cikas, musamman bayan wasu ƙasashen Turai kamar Faransa da Birtaniya sun ce za su daina bayar da tallafi ga Nijar ɗin.
Abin da kuma ka iya ta'azzara tuɗaɗar 'yan ci-rani zuwa Turai.










