Abubuwan da ba ku sani ba kan sabon birni mafi tsayi da Saudiyya ke ginawa
Daga Merilyn Thomas da Vibeke Venema

Asalin hoton, NEOM.COM
Neom ƙasaitaccen birni ne kamar filin wasa
Sheƙin walwali a duhun gaƃar ruwa. Biliyoyin bishiyoyin da aka dasa a ƙasar da ke cike da Sahara.
Jiragen ƙasa masu lilo a iska. Watan bogi. Babu mota, wato babu iskar da ke baza sinadarin carbon a birnin da ke miƙe fiye da tsawon mil 100 a cikin sahara.
Waɗannan wasu ne kaɗan daga cikin fasalin birnin Neom mai managarcin muhallin halittu, a shirin Saudiyya na kafa birnin da zai zama jigon kyautata muhalli baibaiye da korayen tsirrai.
Shin yana da alfanu a kasance da haƙiƙanin gaskiya.
Neom nuni ne da ke fayyace, “fasalin makomar muhallin da al’umma za ta riƙa zama ba tare da illata lumanar lafiyar doron duniya ba.”
Aiki ne da zai ci kuɗi har Dalar Amurka biliyan 500 (daidai da Fam biliyan 366), a wani vangare na manufar Saudiyya na bunƙasa ƙasa nan da shekara ta 2030, inda ƙasar za ta daina dogaro da mai – fannin masana’antun da ya mayar da ita mai ɗimbin arziki.
Faɗin ƙasar da ake aikin ginin ya karaɗe sukwaya kilomita 26,500 – wurin ya fi girman kasar Kuwait ko Isra’ila – haka Neom zai kasance, a iƙirarin masu aikin gina birnin.
Domin kacokam ko ɗungurungum zai kasance ne a wajen ƙwaryar ko ƙarƙashin tsarin dokokin shari’ar da ake aiki da ita a Saudiyyar da ake ciki halin yanzu.
Wani tsarin mulki ne mai cin gashin kansa bisa dokokin da za a tsara wa masu zuba hannun jari.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ali Shihabi, tsohon ma’aikacin banki, wanda yanzu yana cikin hukumar gudanarwar da ke bayar da shawara kan aikin tsara birnin Neom, katafaren faɗin ƙasar zai haɗa da birni mai tsawon gaske, wanda aka yi wa laƙabin Labin layi miƙaƙƙe ‘The Line,’ Labin layin, wanda zai keta kaitsaye ta cikin sahara.
An kwatanta ginin da na birnin Barcelona, wanda babu cushewar tubAlan gini,” ya bayyana cewa.
kowace kusurwar sukwaya za ta wadatar da kanta da kayan more jin daɗin rayuwa, kamar shaguna da makarantu, ta yadda mutane za su iya kaiwa ko cimma buƙatarsu da tattaki ko kewayen minti biyar.
Matuƙar wannan na nuni da cewa, kamar wannan al’amari ba mai yiwuwa ba ne, Shihabi ya bayyana cewa, za a gina layin lawalin ne a mataki- mataki, tubali-tubali.”
Mutane dai na ganin cewa aikin na tattare da matuƙar ruɗani, inda zai laƙume maƙudan kuɗi masu yawan gaske, wato kimanin ƙima gazillion, amma dai za ai gini mai tsari fasali- fasali, ta yadda zai biya buƙatar da ake son cimmawa,” a cewarsa.
Da zarar an kammala aikin ginin, kai-kawo a birnin Lawalin Layi zai gudana ne a kan babban jirgin ƙasa, ta yadda doguwar tafiya duk ba za ta wuce fiye da mintuna 20 ba,” a cewar masu aikin ginin.
Dangane da ƙarin wasu saura al’amura a kai, Neom dai zai kasance mazaunin ruwan da ke toroƙon kai-kawon ƙasa da sama na tsawon kilomita bakwai, inda ake sa ran kasancewarsa ruwa mai toroƙon tasowa mafi girma a faɗin duniya.
Babban Jami’in gudanarwar Neom, Nadhmni al-Nasr, ya ce, tashar jiragen ruwan birnin za ta fara maraba, marhabin da kamfanonin ƙere-ƙere da za a kafa tun farkon shekarar 2022.

Asalin hoton, NEOM.COM
Sannan gaƃar tekun Indiya da wannan masana’anta,’ ta Neom, ya yi nuni da aikin kula da tsirran ƙarƙashin ruwa.
A shafin sadarwarsa, wanda a wani lokaci ke wassafa sarƙaƙiyar ƙirƙirarren labarin kimiyya (sci-fi novel) da ke iƙirarin samar da katafaren muhallin da za a kammala gininsa nan da shekara ta 2025.
Wannan ita ce manufa ta hangen nesan inganta rayuwar al’umma. Haƙiƙanin gaskiyar lamari a halin yanzu, lamarin na da matuƙar ƙayatarwa.
Siffar tauraron ɗan Adam da ke nuni da halin da ake ciki yanzu, a kowace kusurwa an ginata a Sahara.
Sannan jerin gidaje na haɗe da wuraren iyon kurme na alfarma da filin wasan ƙwallon ƙafa Ali Shihabi ya ce, wannan wuri ne da aka keve wa ma’aikatan Neom, amma ba ma wurin ballantana mu tabbatar.

Asalin hoton, GOOGLE EARTH
Sai dai ya ake ganin yiwuwar ginin wannan ƙayataccen birni da zai kasance baibaiye da korayen tsirrai a tsakiyar Sahara?
Dokta Manaf Shihabi, ƙwararren masani a kan makamashi da ke Jami’ar Oxford cewa ya yi, wajen tantance yadda tsarin Neom zai ɗore, akwai al’amura da dama da ya kamata a yi la’akari da su.
Shin za a iya noma abinci ne a birnin ƙarƙashin tsarin da ba ya buƙatar amfani da na’urorin kayan aiki, ko kuwa za a dogara ne wajen shigo da shi daga waje?
Shafin sadarwar ya yi nuni da cewa, Neom zai kasance “birnin duniya mafi wadatar abinci.”
An yi hangen nesa wajen amfani da rumfunan noman zamani ta “wajen sabon salon da ƙasar ta ɗauka, wadda a halin yanzu take shigo da kashi 80 cikin 100 daga waje.
Akwai tambayoyi da dama kan ko shirin zai ɗore?
Kafar wayar da kan al’umma ta yi hasashen yadda rumfar noman zamani za ta wadata Neom da abinci.
Masu adawa na sukar lamiri da zargin Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman da jan ragamar aikin gina Neom da tsarin baibaye sahara da korayen tsirrai, inda ya yi cikakken alƙawarin inganta muhalli ta hanyar ɗaukar hankali daga haƙiƙanin abu mai yiwuwa.
Wannan “katafaren aiki” yana cikin hangen nesan Yarima mai jiran gado na baibaye Saudiyya da korayen tsirrai.
Mako guda kafin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi, mai laƙabin COP26, ya ƙaddamar da shirin na dasa korayen tsirrai, inda ya bayyana manufar kawar da gurvata yanayi nan da shekara ta 2060.
Da farko an kalli lamarin a matsayin babban yunƙurin kyautata muhallin al’umma, amma dai ba a binciki al’amarin da kyau ba, a cewar Dokta Joanna Depledge, wata ƙwararriyar masaniyar yarjejeniya kan sauyin yanayi a faɗin duniya, wadda ta fito daga Jami’ar Cambridge.
Ta yi nuni da cewa, don a taƙaita ɗumamar yanayi zuwa 1.50C, akwai buƙatar a rage haƙar man fetur da kashi 5 cikin 100 a shekara tun daga yanzu zuwa nan da shekara ta 2030.
Duk da haka Saudiyya ta yi alƙawarin ƙara yawan man da take haƙowa makonni kawai bayan kammala babban taron duniya kan sauyin yanayi na COP26.
Ministan makamashi, Yarima AbdulAziz bin Salman an ruwaito shi yana cewa, Saudiyya ba za ta daina fitar da mai ba: “Za mu kara tsara, ta yadda kowane ɗigo na sinadaran Hydrocarbon zai zubo.”

Asalin hoton, YOUTUBE/NEOM
Bayanan wayar da kai na nuni da cewa, “makamashin da ba ya ƙarewa” za a iya samar da shi daga ɗimbin fallen alkinta hasken rana
“Ina jin cewa, lamarin na da tayar da hankali ganin Saudiyya na ganin za ta ci gaba da haƙo mai a irin wannan yanayi a halin yanzu,” in ji Dokta Depledge.
Hayaƙin sinadaran da ƙasar ke fitarwa sama duk daga man fetur ɗin da take ƙonawa ne, fiye da man da take haƙowa.
Saboda haka idan har ƙasa kamar Saudiyya da ke haƙo miliyoyin gangar man fetur a shekara, ta yi dakon su a jiragen ruwa zuwa ƙasar waje zuwa sauran ƙasashe, wannan masarauta ba ta kamata ta yi la’akari da su ba.
Har cikin ƙasar, Saudiyya na da sauran aiki – kodayake manufar da take son cimmawa a halin yanzu, kashi 50 cikin 100 na lantarki a samar da shi daga sabuwar dabarar samar da makamashi nan da shekara ta 2030, kawai kimanin kashi 0.1 cikin 100 ne na lantarkin aka samar ta wannan hanya a shekarar 2019.
Mahangar tunani ta daban
Masu kare Neom sun ce ya zama dole a sake lale, a gina ƙayataccen birni, bisa tsari mai ɗorewa da za a riƙa samar masa da makamashin iska da hasken rana, tare da ruwa da ke bubbugowa ta hanyar tace sinadarin carbon da gishiri.
“Saudiyya na buƙatar wata dabarar mahangar tunani ta daban, saboda Gabas ta tsakiya za ta yi fama da ƙarancin ruwa,” a cewar Ali Shihabi na Hukumar gudanarwar bayar da shawara kan aikin Neom.
Saudiyya tundurƙin tsandaurin ƙasa ce, kuma fiye da rabin ruwan da take samarwa ta hanyar tace sinadarin carbon da gishiri – na’urorin masana’anta da ke tace gishiri daga ruwa- kuma tana amfani da makamashin man fetur ne, wata hanya da ake kashe kuɗi masu yawan gaske.
sannan abubuwan da aka tato sinadarai ne masu guba, waɗanda ake zubarwa a baƙin teku, al’amarin da ke da illa ga halittun ruwa.
Hayaƙin da ke tashi a masana’antar tace gishiri daga ruwan teku a Saudiyya
Tsarin tsaftace ruwa daga gishiri a Neom za a samar masa da makamashi ne ta dabarun sabunta makamashi da gishirin ruwan teku, maimakon a sake jibge shi a cikin teku, za a yi amfani da shi a mastsayin sinadarin sarrafawa a masana’anta.
Akwai dai cikas guda wajen amfani da sabunta makamashi a na’urorin tace gishiri daga ruwa, don ba a tava yin nasarar hakan ba.
Amma dai ƙwararru a harkar kula da muhalli na nuna damuwa kan dogaro da dabarar ƙere-ƙeren kimiyya da ba a samu nasarar gwajin su ba.
Waɗanda za su iya kawo koma-baya wajen inganta yanayi, ballantana a kai ga ɗaukar ƙwaƙƙwaran matakin shawo kan illar sauyin yanayi.
A wasu lokutan dai ƙwarin guiwar tasirin fasahar ƙere-ƙere ake da shi.
Kuma akwai babbar tambaya kan ko saboda wane ne (rukunin mutane) aka gina Neom?

Asalin hoton, YOUTUBE/NEOM
Yankin da ba kowa a tsakanin gaƃar tekun Indiya da tsaunukan da ke kan iyakar ƙasar Jordan, ta yiwu ya zama wuri mafi kyawun dacen gina ƙaramar ƙasa.
Kodayake dai tuni mutane na zaune a wurin, wato ’yan asalin ƙabilar Larabawan karkara, makiyaya da ake kira Huwaitat.
Aikin ya ba da tabbacin samar da ayyukan yi, tare da dukiyar hada-hada a wannan yanki da babu ci gaban zamani, amma a halin yanzu al’ummar karkarar ba su ci gajiyar wata fa’ida ba.
Masu fafutikar kare haƙƙin ɗan Adam sun ce, garuruwa biyu an rusa su, sannan ’yan ƙabilar Huwaitat mutum 20,000 an kore su daga yankin, ba tare da wata cikikkiyar diyya ba, don kawai a gina wannan hamshaƙin ƙasaitaccen birni.
“Yunƙurin da aka yi na tursasa ’yan asalin wurin su bar yankin keta haddi ne da keta dokar kare haƙƙin ɗan Adam ta duniya,” a cewar Sarah Lea Whitson, Babbar Daraktar tabbatar da muradun dimokuraɗiyya a ƙasashen Larabawa

Asalin hoton, Getty Images
An halaka mutum guda cikin Afirilun 2020, Abdulrahim al-Huwaiti, wanda ya ƙi ficewa daga gidansa da ke Tabuk, kuma ya riƙa baza hotunan bidiyo a shafukan intanet.
Kwanaki kaɗan daga bisani rundunar jami’an tsaron Saudiyya suka harbe shi, tamkar dai yadda ya yi hasashen kasancewar hakan.
AbdulRahim al-Huwaiti ya baza hotunan bidiyo a shafukan intanet, inda ya ce, yana sa ran za a kashe shi
Mai magana da yawun ofishin Jakadancin Saudiyya a Washington DC, Fahad Nazer, ya musanta zargin cewa, an tursasa wa Huwaitat, kodayake bai musanta kisan da aka yi wa Mista al-Huwaitat ba, inda ya yi watsi da lamarin a matsayin “ƙaramin abin da ya faru.”
’Yan yawon buɗe ido da attajirai

Asalin hoton, Neom
Neom dabarar ƙayatarwa ce da ɗaukar hankalin mutane, a wani yunƙurin jawo masu yawon buɗe ido su shiga hada-hadar juya akalar tattalin arzikin Saudiyya- shi ma dai an buɗe masa babin sukar lamiri.
An yi ƙayatacciyar tallar nuna katafaren birni mai ƙawa , tare da dokokinsa da jami’an tsaronsa, a wani yanki mai cin gashin kansa, savanin jami’an tsaron da aka sani a Saudiyya a da, tare da ƙa’idojinsu.
Sai dai masu adawa na cewa, aikin an yi ne don biyan buƙatun manyan attajirai. An gina fadoji ga ’ya’yan sarautar ƙasar kamar yadda aka ruwaito.
Siffar tauraron ɗan Adam na nuna wajen saukar ƙaramin jirgin sama da wajen wasan ƙwallon golf, a gine-gine farko na aikin.
Ali Shihabi ya yi iƙirarin cewa, birnin ya tanadi gidaje ga kowa-da-kowa “tun daga kan leburori zuwa hamshaƙan masu kuɗi,” kodayake dai ya fadi cewa, ba dai yadda ake tsammani ba.
“Ina ganin cewa, matsalar Neom ta nuna gazawa a dabarun isar da saƙo,” in ji shi. “Mutane na ganin cewa, kawai birni ne na holewar masu kuɗi.”
Mawuyacin zabi
“Farkon shirin komawa tafarkin baibaye ƙasa da korayen tsirrai ba abu ne mai sauƙi ba, amma ba za mu kauce wa mawuyacin zavi ba,” a cewar Muhammad Bin Salman. “Mun yi watsi da tsarin ƙarya na zavi tsakanin kare tattalin arziki da kare muhalli
Neom ƙarara a bayyane yake yana cikin hangen nesa mai manufa. Amma dai a halin yanzu ’yan Saudiyya suna kauce wa mawuyacin zavi gaba ɗaya- wajen kauce wa haƙar man fetur.
Kulle famfuna na da wahala, a cewar Manal Shehabi, ƙwararren masanin makamashi daga Jami’ar Oxford. “Ina ganin lamarin na da matuƙar wuyar sha’ani, ta fuskar tattalin arziki, a sa ran kowace ƙasa da ta dogara ƙwarai da gaske kan fetur da iskar gas, kwatsam ta dakatar, ta daina haƙar albarkatun da take da su.”
Saudiyya na cewa, tana biyan buƙatun duniya ne na makamashi. “Gaskiyar lamari ita ce, har yanzu a faɗin duniya ana buƙatar sinadaran hydrocarbon,” a cewar mai magana da yawun Ofishin Jakadancin Saudiyya, Fahad Nazer.N

Asalin hoton, Neom
A fakaice Saudiyya da sauran ƙasashen da ke dogaro da arzikin man fetur a kodayaushe sukan yayyafa wa duk ƙurar da ta so kan abin da ya danganci jajircewa kan yanayi a faɗin duniya, a cewar Dokta Depledge
Haka lamarin ya ci gaba a taron sauyin yanayi na COP26. Saudiyya ta shiga tsakani, inda kaitsaye ta yi ƙoƙarin nuna rashin tabbaci da yawan kuɗi da illa ga muhalli, don rage hanzarin da ake yi wajen shawo kan matsalar da ke tattare da sauyin yanayi,” in ji Dokta Depledge, wadda ta bi kadin yarjejeniyar da aka ƙulla a Glasgow kaitsaye.
“Wannan kawai wani salon ce-ce-ku-ce ne da yaren da Saudiyya ke sauyawa tun da aka fara yarjejeniyar kan sauyin yanayi.”
Sai dai Fahad Nazer, mai magana da yawun gwamnati, ya musanta zarge-zargen kauce wa tsarin korantar da muhalli, inda ya jajirce kan cewa Saudiyya na ƙoƙarin baibaye muhallinta da korayen tsirrai ne nan gaba.
Duk da haka dai har yanzu akwai tambayoyi kan ko Neom za ta ɗore yadda aka tsara, Ali Shihabi ya nemi mu zuba ido mu gani yadda za a riƙa biyan kuɗin, “kafin wani ya yi wani abu.











