Waiwaye: Fara kwasar 'yan Najeriya daga Sudan da cikar 'Yar'adu'a shekara 13 da rasuwa

b

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata

Tafiyar Buhari Landan bikin naɗin Sarkin Ingila

c

Asalin hoton, Nigerian Presidency

A ranar Laraba ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin Landan domin halartar bikin naɗin sabon Sarkin Ingila Charles lll.

A ranar Asabar ne aka gudanar da bikin naɗin a Cocin Westminster Abbey da ke birnin Landan.

Firaministan Birtaniya Rishi Sunak da sauran tsofaffin Firaiministocin ƙasar bakwai duka sun halarci bikin.

Manyan mutane daga faɗin duniya ne suka halarci bikin naɗin Sarki Charles III, waɗanda suka haɗar da shugaban Faransa Emmanuel Macron da matar Shugaban Amurka Jill Biden.

An fara mayar da 'yan Najeriya daga Sudan

n

A daren Alhamis ne rukunin farko na ɗaliban Najeriya da suka maƙale a Sudan bayan ɓarkewar rikici a ƙasar, suka sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, bayan shafe sama da mako guda a kan hanya.

Yawancin ɗaliban dai sun sauka a gajiye kuma da ganin su sun ƙosa su isa gida.

Yawancin ɗaliban da BBC ta tattauna da su, sun ce sun shiga hali na tashin hankali a tsawon lokacin da suka kwashe suna ƙoƙarin barin ƙasar ta Sudan.

Ɗaliban waɗanda suka sauka da misalin ƙarfe 11:30 na dare a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja na daga cikin kason farko da suka samu ficewa daga Sudan ta ƙasar Masar.

'Yan sanda sun kama matashin da ake zargi da kashe mahaifiyarsa a Kano

.

Asalin hoton, Kano police

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta sanar da kama matashin nan Ibrahim Musa da ake zargi ya kashe mahaifiyarsa a Kano.

Cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an kama matashin ne a maɓoyarsa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar ta Kano.

Abdullahi ya ce matashin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda kuma ya ce yana tu'ammali da ƙwayoyi masu sa maye.

A yanzu dai za a tura shi zuwa kotu bayan kammala bincike.

A cikin makon da ya gabatan ne aka ruwaito cewa matashin ya caccaka wa mahaifiyarsa mai shekara 50 wuƙa a kanta da ƙirjinta da kuma sauran sassan jiki, inda ya tsere bayan aikata laifin.

Cikar 'Yar'adu'a Shekara 13 da rasuwa

g

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Juma'ar da ta gabata ne tsohon Shugaban Najeriya Umaru Musa 'Yar’adu'a ya cika shekara 13 da rasuwa.

Tsohon shugaban ya rasu ne a kan karagar mulki bayan shafe dogon lokaci yana fama da jinya.

'Yan ƙasar da dama sun bayyana kewarsu ga tsohon shugaban wanda ya rasu a ranar 5 ga watan Mayun 2010.

Tsohon mataimakin 'Yar'adu'a wanda kuma aka rantsar a matsayin shugaban ƙasar bayan rasuwar 'Yar'aduan, Goodluck Jonathan ya bayyana tsohon maigidan nasa a matsayin shugaba maras son zuciya.

Jonathan ya kasance mataimakin Umaru Musa Yar’adu'a daga shekara ta 2007 zuwa 2010

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Juma'a, Jonathan ya rubuta cewa, “A wannan rana shekara 13 da ta wuce, ƙasarmu ta yi rashin jajirtaccen shugaba maras son zuciya, Shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.

Mutum ne mai son zaman lafiya da adalci da kuma kamanta gaskiya.

Matsayar gwamnatin Najeriya kan ce-ce-ku-cen haramta cin 'Indomie'

g

Asalin hoton, Getty Images

A makon da ya gabatan ne kuma hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta ce za a iya cin taliyar indomie a ƙasar saboda ba ta ɗauke da sinadarin haddasa cutar kansa.

Shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana haka yayin tattaunawa da BBC, inda ta ce taliyar ta indomie da ta sahale a ci, a ƙasar ake samar da ita.

An yi ta samun rahotanni mabanbanta cewa taliyar indomie mai ɗanɗanon kaza da Taiwan da Malaysia ke samarwa, tana ɗauke da sinadarin Ethylene Oxide da ke haddasa cutar kansa.

Sai dai, NAFDAC ta ce indomie da ake samarwa a cikin ƙasar ba ta da wata alaƙa da ta Taiwan da kuma Malaysia.

Legas ta soma wallafa sunaye da hotunan masu fyaɗe a jihar

g

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta wallafa sunayen wasu mutum uku da aka samu da laifukan fyaɗe a jihar.

Hukumar Yaƙi da Laifukan cin Zarafi ta jihar ce ta wallafa sunayen mutanen uku a shafinta na Tuwita

Hukumar ta wallafa sunaye da hotunan mutanen tare da irin nau'in laifukan da suka aikata da irin hukuncin da kotu ta yanke musu.

A watan Mayun shekarar 2022 ne hukumar ta bayyana aniyarta ta fara wallafa sunaye da hotunan masu aikata laifukan cin zarafi a shafukanta.