Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Nicolas Maduro shugaban Venezuela da Amurka ta kama?
- Marubuci, André Rhoden-Paul
- Lokacin karatu: Minti 5
Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta kama shugaban Venezuela Nicolas Maduro bayan harin da Amurka ta kai ƙasar da ke kudancin Amurka.
Trump ya ce an fitar da shugaban Venezuelan mai ra'ayin riƙau da matarsa daga ƙasar a wani samamen soji da haɗin gwiwar jami'an tsaron Amurka.
Wannan na zuwa ne bayan rahoton jin ƙarar fashewar wasu abubuwa a Caracas babban birnin ƙasar da tsakar daren Asabar, ciki harda wanɗanda suka tashi a barikin soji.
Tuni gwamnatin Venezuela ta buƙaci samun shaidar cewa Maduro yana nan a raye, tare da ƙaddamar da dokar ta ɓaci, da jibge dakarunta.
Kama Maduro ya zo ne a daidai lokacin da fargaba ta ƙaru tsakanin ƙasashen biyu, bayan Washington ta kai hare-hare kan jiragen ruwa a tekun Karebiya, inda ta yi zargin ana safarar miyagun ƙwayoyi.
Amurka ta zargi shugaban Venezuela da hannu a safarar miyagun ƙwayoyi da kuma zama haramtaccen shugaba, yayin da Maduro ya zargi Amurka da yi mashi barazana.
Ga abubuwan da muka sani kawo yanzu.
Me muka sani a kan harin?
Babu cikakken bayani kan wajen da aka kama Maduro. Trump bai bayar da cikakken bayani ba game da yadda aka kama shugaban Venezuela, ko kuma wajen da ake tsare da shi.
Kafar CBS ta ce dakarun yaƙi da ta'addanci na Amurka da ake kira Delta Force ne suka kama shugaba Maduro.
Trump zai yi taron manema labarai a gidansa Mar-a-Lago, kuma ana sa ran samun ƙarin bayani game da yadda harin ya gudana, a lokacin taron.
Sanata Mike Lee na jam'iyyar Republican, wanda ya zanta da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya ce Maduro zai fuskanci shari'a a Amurka kan zargin aikata manyan laifuka.
"Rubio ba ya tunanin za a ci gaba da wani harin soji a kan Venezuela a yanzu tunda Maduro yana a hannun Amurka,'' in ji Lee.
Da misalin ƙarfe 2 na dare aka ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Caracas, yayin da hayaƙi da wuta suka turnuƙe birnin.
An ga bidiyon yadda abubuwan suka fashe da uyadda jirgi mai saukar Ungulu, amma kawo yanzu ba a iya tantance sahihancin bidiyon ba.
Rahotanni sun ce daga wuraren da aka kai harin harda filin jirgin saman soji na La Carlota da ke a tsakiyar babban birnin da kuma wata barikin soji a Fuerte Tiuna.
An kuma ɗauke lantarki a wuraren da ke maƙwabtaka da wajen da aka kai harin.
Ba a kuma tantance ko an samu asarar rai ba kawo yanzu.
Gwamnatin Venezuela ta ce an kai wasu hare-haren a jihohin Miranda da Aragua da kuma La Guaira.
Mene ne martani Venezuela?
Mataimakin shugaban Venezuela Delcy Rodríguez ta ce gwamnati ba ta san wajen da Maduro da matarsa suke ba, amma ta buƙaci a gaggauta ba su tabbacin cewa suna nan a raye.
Mnistan tsaron ƙasar, Vladimir Padrino López ya yi iƙirarin cewa hare-haren sun shafi wuraren da fararen hula suke, kuma gwamnati tana tattara bayanan waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata.
Ya ƙara da cewa Venezuela za ta yi "turjiya" ga duk wani yunƙurin jibge dakarun ƙasar waje a cikin ƙasar ta.
A cikin wata sanarwa, gwamnatin Venezuela ta yi Allah wadai da ƙarfin soji da Amurka ta yi amfani da shi a kan ƙasar, a barikin soji da kuma yankin fararen hula.
Ta kuma zargi Amurka da zama barazana ga zaman lafiyan duniya, inda ta bayyana harin a matsayin wani yunƙuri na ƙwace muhimman albarkatun Venevuela, musamman mai da ma'adinai.
Me Donald Trump ya ce?
Jim kaɗan bayan harin, fadar White House ta ƙi yarda ta yi tsokaci a kai.
Amma Trump ya wallafa a shafin sada zumuntarsa na Truth Socila cewa Amurka ce ta kai harin.
"Amurka ta yi nasarar kai manyan hare-hare a Venevuela, kuma shugaban ƙasar, Nicolas Maduro, wanda aka kama tare da matarsa an ɗauke su daga ƙasar,'' in ji Trump.
"An gudanar da wannan aiki ne tare da jami'an tsaron Amurka da sauran hukumomin tabbatar da doka. Za mu bayar da cikakken bayani nan gaba."
A wata hira da New York Times, an ji shugaban Amurka cikin wani saƙon murya na daƙiƙa 50 yana cewa an gudanar da aikin cikin ''ƙwarewa da basira''.
Asked what he envisioned for
Da aka tambaye shi game da manufarsa kan Venezuela, sa ya ce: "Za ku sani da ƙarfe 11.''
Wane ne Maduro kuma me ya sa aka kama shi?
Nicolás Maduro ya yi suna ne a ƙarƙashin shugabancin tsohon shugaban Venevuela mai tsattsauran ra'ayi Hugo Chávez da jam'iyyarsa ta United Socialist Party of Venezuela (PSUV). Maduro ya gaji Chávez a matsayin shugaban ƙasa a 2013.
A 2024, aka sanar da shugaba Maduro a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban kasa, duk da cewa ƙidddigar da ƴan adawa suka tattara ta nuna ɗan takararsu, Edmundo González ne ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye.
Sun raba gari da Trump bayan kwararar ɗaruruwan baƙi ƴan Venezuela cikin Amurka, da kuma matakin fadar White House na yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi musamman fentanyl da hodar iblis.
Trump ya ayyana ƙungiyoyin Venezuela biyu masu hada-hadar ƙwayoyi, Tren de Aragua da Cartel de los Soles a matsayin ƙungiyoyin ta'addanci na ƙasashen waje kuma ya yi zargin cewa Maduro ne shugaban ɗaya daga cikin su.
Amurka ta sanya ladar $50m (£37m) ga duk wanda ya bayar da bayani kan yadda za a kamo Maduro.
Maduro ya musanta zama shugaban ƙungiyar safarar ƙwayoyi, kuma ya zargi Amurka da fakewa da yaƙinta da safarar ƙwayoyi domin hamɓarar da shi da kuma samun damar kwasar albarkatun mai da Venevuela ke da su.
A watannin nan, dakarun Amurka sun kuma ƙaddamar da gomman hare-hare kan jiragen ruwa da take zargin suna shigar da miyagun ƙwayoyi cikin Amurka. An kashe mutane fiye da 100 a hare-haren.
Me sauran ƙasashe ke cewa?
Labarin harin ya janyo martanin gaggawa daga tsofaffin abokan ɗasawar Venezuela.
Rasha ta zargi Amurka da aikata ''laifin kutse cikin wata ƙasa, kuma abin damuwa da Alla-wadai''.
Jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce: "Abin da ya fi muhimmanci shi ne a gano yadda maƙiyi ke neman kawo hari kan ƙasa ko kan shugabanni ko gwamnati ko jama'a. Dole mutum ya tashi tsaye domin turjiya ga maƙiya.''
Shugaban Colombia Gustavo Petro ya kira harin a matsayin wani "harin Amurka kan ƴancin ƙasa" yayin da shugaban Cuba, Miguel Diaz-Canel ya bayyana harin a matsayin "babban laifi".
Ita kuma ma'aikatar harkokin wajen Sifaniya ta yi kiran a kiyaye tanadin dokar ƙasa da ƙasa kan duk wani mataki da za a ɗauka, yayin da Jamus da Italiya suka ce suna bibiyar abin da ke faruwa.