Me ya sa wasu kiristoci ba sa bikin Kirsimeti?

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da al'ummar Kirista suka gudanar da shagulguan bukukuwan kirsimeti a tsakiyar makon nan, wasu kiristocin kan kaurace wa bukukuwan a kowace shekara.

Mabiya addinin Kiristan kan gudanar da bukukuwan ne domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu, da Kiristoci suka yi imanin cewa an haife shi ne domin ya ceci duniya daga ɓarna.

To sai dai yayin da kowane Kirista ya yi imani da wanzuwar Yesu Almasihu a matsayin wannan babban ginshiƙi ko madogarar addininsa, akwai saɓani mai ƙarfin dangane da haƙiƙanin ranar da aka haife shi.

Babu wasu tsofaffin littattafan tarihi da suka bayyana cewa an haife shi ranar 25 ga watan Disamba, duka ijma'i ne kawai la'akari da tsofaffin bukukuwan mutane da.

Wannan shi ne babban dalilin da ya sa wasu Kiristoci ba sa bukukuwan Kirsimeti, saɓanin mabiya ɗariƙar Katolika da wasu daga dama cikin mabiya Protestants, da suka ɗauki ranar da muhimmanci a addininsu.

Yayin da wasu coci-coci suka ɗauki ranar da muhimmanci wajen gudanar da bukukuwa, wasu kuwa ba sa gudanar da bukukuwan.

Farfesa Edin Sued Abumanssur, ƙwararren masanin ilimin zamantakewa a Jami'ar Pontifical Catholic da ke São Paulo ya ce akwai saɓani tsakanin mabiya ɗariƙar Evangelican, kan bukukuwan na Kirsimeti.

''A wasu garuruwan suna gudanar da bukukuwan Kirsimeti, yayin da a wasu garuruwan kuwa ba sa gudanarwa'', kamar yadda ya shaida wa sashen Brasil na BBC.

"Waɗanda ba sa bukukuwan, suna cewa asali ranar, hutu ce ga mabiyar addinin Pagan, don haka suke ganin ranar ta samo asali ne daga addinin Pagan, to amma addinin Kiristanci ya rungumi wasu ranakun hutun addinin Pagan'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

'Abu muhimmi shi ne ceton Yesu'

Farfesa Abumanssur ya ce wasu kuma na cewa babu tabbaci game haƙiƙanin ranar da aka haifi Yesi Almasihu, don haka ba su ga dalilin ware ranar 25 ga watan Disamba domin gudanar da biki domin tunawa da wani abu muhimmi na tarihi ba

Ya ƙara da cewa ''abu muhimmi shi ne mutuwa da ceton Yesu''.

A taƙaice ba a bayyana rana ko lokacin da aka haifi Yesu, kai tsaye ko ishara da hakan ba, a cikin manyan littan addinin Kirista biyu, Luke da Matthew da suka yi bayanin haihuwarsa.

Mabiya cocin Jehovah Witnesses sun yi bayanin wannan matsala a littattafan cocinsu.

A cikin litattafan sun bayyana dalilinsu na rashin gudanar da bukukuwan kirsimeti da cewa babu shi a cikin surorin littafin Bible.

"Yesu ya umarce mu da tunawa da mutuwarsa, ba ranar haihuwarsa ba,'' kamar yadda suka rubuta cikin littattafan cocin nasu.

Suna masu ambata nassi daga littafinsu da ake ciki ake tunanin Yesu ya umarci almajiransa su riƙa maimaita al'adar "don tunawa da ni."

Mabiya wannan ɗarika sun yi imanin cewa bukukuwan kirsimeti sun samo asali daga al'adun da ibadun addinin Pagan.

''Kan wannan dalilin ne muka yi imanin cewa ba Ubangiji ne ya halasta Kirsimeti ba,'' kamar yadda yake cikin littattafn nasu.

Masanin falsafa mai suna Cleberson Dias, da ya wallafa litattafan na cocin Jehovah Witnesses, wanda ke da digiri na uku a fannin ilimin kimiyyar addinai ya shaida wa Sashen Brasil na BBC cewa wannan dalili - na kasancewar bikin ba daga addinin Kirista ya samo asali ba - ya sa mabiya Cocin Jehovah Witnesses "ke kallonsa a matsayin laifi", duk kuwa da tsawon lokacin da aka ɗauka ana gudanar da shi.

"Babu wani dalili da ya nuna cewa an haifi Yesu ranar 25 ga watan Disamba, ba a ambata ranar haihuwarsa a cikin littafin Bible ba,'' a cewar cocin.

''Sahabbai da tabi'an Yesu na farko ba su yi bikin Kirsimati ba. kamar yadda littafin Barsa Encyclopedia ya bayyana.

"Bishop Liberius na Roma ne ya fara ɓullo da bikin Kirsimeti a hukumance a shekara ta 354," fiye da shekara 200 bayan mutuwar sahabin Yesu na ƙarshe.

A cikin wata muƙala da wani Fasto mai suna Adventist Carlos Hein ya wallafa a 2013, ya ambato cewa Ellen G. White ta rubuta cewa Ubangiji ya ɓoye "ranar haihuwar Yesu" saboda kada ranar "ta sami wata daraja maɗaukakiya da za a danganta da shi a matsayinsa na mai ceton duniya."

Ellen G. White ta kuma soki yadda ake gudanar da bikin da cewa "Bai kamata mutane su riƙa matsa wa kansu lamba ba wajen sayen kyaututtukan Kirsimeti da na sabuwar shekara. Ba laifi ga ƙananan kyatuttukan da ake bai wa ƙananan yara, amma bai kamata mutane su riƙa kashe kuɗaɗensu wajen kyaututtuka masu tsada'', in ji ta.