Bournemouth ta ragargaji Forest a Premier Leagye

Bournemouth

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Bournemouth ta ci gaba da sa ƙwazo a wasannin Premier League a bana, domin ganin ta je gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa.

Ƙungiyar ta Vitality ta doke Nottingham Forest 5-0 ranar Asabar a karawar mako na 23, tun kan nan ta yi wasa 11 ba a doke ta ba.

Bournemouth ta ci ƙwallo ta hannun Kluivert, shi kuwa Ouattara uku rigis ya zura a raga da kuma Semenyo da ya ci na biyar.

Bournemouth ta buga wasan da kwarin gwiwa, wadda ta doke Newcastle United 4-1 a makon jiya.

Ƙwallon da Kluivert ya ci shi ne na 11 kuma na biyu a gida, kenan suna ta kokarin ganin sun samu gurbin shiga gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa.

Da wannan sakamakon Bournemouth tana da maki 40 tana ta shidan teburin Premier League.

Bournemouth za ta karɓi bakuncin Liverpool ranar Asabar 1 Fabrairu daga nan ta je Everton, domin fafatawa da Everton a Goodison Park a FA Cup.