Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaƙe-yaƙen 2024 da suka haɗa kan masu hamayya da kuma ƙirƙiro sabbin maƙiya
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Security correspondent
- Lokacin karatu: Minti 7
Shekarar 2024 ta kasance shekara mafi yawan faruwar al'amura tun lokacin da na fara ɗauko rahoton harkokin tsaro a duniya ga kafar BBC a 2001 bayan harin ranar 11 ga watan Satumba.
A shekarar ne aka hamɓarar da tsohon shugabna Syria, Bashar al-Asad, sojojin Koriya ta Kudu suka shiga yi wa Rasha yaki. Makamai masu linzami mallakar Burtaniya da Amurka sun sauka a Rasha, Ita ma Iran ta tallafa da nata makaman masu linzami zuwa Rasha. Haka kuma a shekarar na an ga yadda Isra'ila bisa goyon bayan Amurka ta yi luguden wuta a Gaza da Lebanon sannan sojoji Houthi na Yemen na ruwan makamai masu linzami zuwa Isra'ila.
Bari mu yi duba kan waɗannan yaƙe-yaƙe masu sarƙaƙaƙiya da ke tilasta yin tambayar cewa shin ko yaƙe-yaƙen na da alaƙa ne?
Ukraine da Rasha: Yaƙi a tsakiyar Turai
Kafar watsa labarai ta Lurid ta rawaito cewa sojojin Koriya ta Arewa tsakanin dubu 10 zuwa 120,000 waɗanda ba su da ƙwarewar yaƙi sun je filin daga a Ukraine kuma sun kwashi kashinsu a hannu. Sai dai ana ganin ɗaukin da suka kai wa Rasha alama ce da ke nuna yadda yaƙin ya fantsama.
Wata alamar da ke nuna fnatsamar yaƙin ita ce yadda ƙasashen Turai suka bai wa Ukraine makamai masu linzami da ke cin dogon zango domin harba wa Rasha, wani abu da ya tayar da hankalin Rashar har ta yi barazanar mayar da martani.
Sai dai ƴan Ukraine suna nuna damuwa dangane da tallafin da Rasha ke samu da suka ce ya fi wanda suke samu daga Turai.
"E, muna samun tallafin makamai da horo daga ƙawayenmu na Turai kuma muna godiya da hakan, to amma irin taimkaon da Rasha ke samu daga Iran da Koriya ta Arewa ba za ka haɗa shi da wanda muke samu ba. Dole ne mu samu tallafi fiye da nasu daga Turai idan dai ana son mu yi nasara." In ji wakilin BBC a Ukraine, Vitaly Shevchenko.
To sai dai tun farkon fara wannan yaƙi, yammacin duniya ba ta tsaya kallo ba. Amurka da NATO da tarayyar Turai suna tallafa wa Ukraine da soji da kuma kuɗade waɗanda su ne suka taimaka mata hana dakarun Rasha yin kataɓus - kafin yanzu.
Gabas ta Tsakiya
Sarƙaƙaƙiyar da ke cikin yaƙin da ake a Gabas ta Tsakiya ya mayar da wanda ake yi a Turai kamar wasan yara.
Sai dai wani abu da ya kamata a sani shi ne rikicin bai shafi rayuwar al'ummomin Dubai da Saudiyya da ma Misra inda suke tafiyar da rayuwarsu yadda ya kamata. Sannan duk da cewa ƙasashe kamar Iran da Iraq sun fuskanci rikicin amma wasu al'ummun nasu a wasu wuraren na tafiyar da rayuwarsu kamar yadda suka saba.
Syria: Ƙarƙashin sabuwar gwamnati
Babu dai wanda ya yi hasashen abin da ya faru a Syria zai faru a ƙasa da makonni biyu, inda ƴantawaye suka fatattaki shugaba mai ci, Bashar al-Asad.
Abin da ya faru dai ya fi ƙarfin mutanen Syria wani abu da ke nuna akwai hannun ƙasashen waje.
Ɗaya daga cikin illolin da harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila ya yi a Syria, shi ne martanin Isra'ila ya janyo ya ɗaiɗaita ƙawayen Iran a yankin. Saboda a 2015 lokacin da ƴantawaye suka nemi hamɓarar da gwamnatin Assad, Iran da Rasha da hezbollah sun daƙile yunƙurin.
To amma a wannan karo rasha tana fama da Ukraine, ita kuma Hezbollah ta ji jiki daga hare-haren Isra'ila sannan Iran ta samu matsala tun bayan kutsawa da jiragen yaƙin Isra'ila suka yi wa sararin samaniyyarta.
Hakan na nufin ƙawayen Assad na fuskantar barazana saboda haka ba za su iya kai masa ɗauki ba, wani abu da ya bai wa Turkiyya wadda ke goyon bayan ƴantawayen, ta ga dama kuma ta yi amfani da damar.
Rikicin Gaza da ke ci gaba
Yanzu watanni 15 ke nan da fara wannan rikici kuma an lalata mafi yawancin yankunan Gaza. Fiye da mutum miliyan daya daga cikin mutum miliyan 2.4 na Gaza na gudun hijra.
Alƙaluma daga ma'aikatar lafiyar da Hamas ke iko da ita sun nuna kawo yanzu an kashe Falasɗinawa fiye da 44,000 tun fara yaƙin.
Isra'ila na cewa harin da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan oktoban 2023 ya yi sanadin mutuwar ƴan Isra'ila fiye da 1000 sannan sun yi garkuwa da mutum 250.
Ƙokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na samu cikas duk da irin ƙoƙarin da Qatar da Misra da Amurka ke yi. Ita dai Isra'ila ta sha alwashin ganin bayan ƙungiyar Hamas.
Har kawo yanzu dai babu wata makoma da aka fitar dangane da Gaza bayan yaƙin haka kuma ba a fayyace wane ne zai jagoranci zirin Gaza ba bayan kwashe shekaru 18 Hamas na iko da yankin.
Rikicin na Gaza ne dai ya haifar da sauran rikice-rikicen wasu ƙasashen a Gabas ta Tsakiya kamar Lebanon da Yemen da Iran da Syria.
Iran da ƴan kanzaginta
kasar Iran na goyon bayan ƙungiyoyin sojin sa-kai da dama a yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar ba su kuɗaɗe da makamai da kuma horo. Dakarun Iran ɗin na Quds Force, wani ɓangare na dakarun juyin-juya hali na ƙasar Iran,IRGC ne ke aiwatar da tsari.
To sai dai ta hanyar amfani da jami'an sirri na hukumar leƙen asirinta, Mossad, da dakarunta , Isra'ila ta gurgunta Hezbollah bayan kashe mata jagorori da lalata tsarin sadarwarta da kuma rumbunanta na makamai. Isra'ilar ta kuma kashe dubban jama'a a lokacin hare-haren tsakanin Lebanon da Israi'la na ɗan wani lokaci kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Nuwamba.
Isra'ila tana yaƙi da Hamas a Gaza da Hezbollah a Lebanon sannan kuma ta sha harba makamai masu linzami ga Iran da Yemen da Syria da Iraq.
Amurka dai na ci gaba da bai wa Isra'ila tallafin soji kamar na'urar THAAD mai garkuwa ga makamai masu linzami.
Israi'ila ta samu galaba a kan ƙungiyoyi da Iran ke marawa baya kamar Hezbollah da hamas da Houthis da sauransu.
Baya ga tallafa wa ƙungiyoyi ƴankanzaginta da makamai, Iran tana aike da makamai masu linzami ga Rasha domin yakar Ukraine. Akwai rahotannin da ke nuna cewa Rasha tana bai wa mayaƙan Houthi bayanan sirri da ta tattara daga tauroronta na ɗan'adam ta hanyar Iran domin taimaka musu kai hari kan jirageb ruwan ƙasashen yammaci da ke safara a tsakanin tekun India zuwa Maliya.
Afirka: Sabon gandun da Rasha ta sabu
Duk da cewa Rasha ta rasa babbar ƙawarta Syria amma har yanzu tana tare da shugaban Libya, Khalifa Haftar da ke Benghazi sannan tana kafa sansani ga dakarunta a Sudan da sauran ƙasashen Sahel.
Yanzu dakarun Rashar da a baya ake kiran su da Wagner inda suka koma "Afrika Korps" sun yi nasarar maye gurbin dakarun ƙasar Faransa da na sauran ƙasashen yammaci a ƙasashen Sahel da tsoffin ƙasashe renon Faransa kamar Mali, Burkina Faso da Nijar da Afirka ta Tsakiya.
Koriya ta Arewa: Abokiyar ƙawancen Rasha
Koriya ta Kudu na cikin damuwa saboda tsoron alaƙar abokiyar hamayyarta Koriya ta Arewa da Rasha. Seoul na tsaron yiwuwar samun wasu fasahohin yaƙi daga Rasha da Koriya ta Arewa za ta iya samu biyo bayan dakarunta da ta aike da su Ukraine domin tallafa wa Rashar.
Duk wadannan sun riga sun ƙara girman tankiyar da ke tsakanin ƙasashen Koriyar guda biyu - ƙasashen biyu dai masu maƙwabtaka ba su ayyana a hukumance cewa sun ƙarƙare yaƙin da ke tsakaninsu tun 1953.
Taiwan da China
Har yanzu wannan bai zama rikici na fili ba amma kuma wani abu ne mai ban tsoro.
A daidai lokacin ƙasashen yammacin suka kwashe kusan shekaru 20 suna yaki a Iraq da Afghanistan, China kuwa a asirce kuma cikin dabara tana mamaye wuraren da ke Kudancin China inda take ikirarin mallakarta ne.
Babbar damuwar ita ce Taiwan. China tana sha nanata cewa za ta sake komar da Taiwan zuwa cikin ƙasarta duk da cewa China ba ta taɓa mulkar Taiwan din ba tun da jam'iyyar Communist Party ta hau karagar mulki a 1949.
Shugaba Xi Jinping ya bayyana a fili cewa hakan abu ne mai yiwuwa "ta hanyar ƙarfin tuwo" kafin cikar jam'iyyar Communist Party shekara 100 a 2049.
Taiwan ba ta son ta zamo ƙarƙashin China.
Mene ne abu na gaba?
Akwai ƙudirin da gwamnatin Trump mai shigowa ke yi na samar da zaman lafiya a Ukraine. To sai dai da alama ba abu ne da zai yiwu cikin sauƙi ba domin Rasha na da nata tsarin.
Dangane kuma da Gabas ta Tsakiya, Iran da Israel da alama ba su kammala cimma burinsu ba. Akwai alamun da ke nuna cewa Donald Trump wanda ya ba da umarnin kashe Qasem Sulaimani na Iran a 2020 ka iya haɗa kai da Isra'ila domin kai wa shirin Iran na nukiliya hari.
Ita kuwa Syria, ana hasashen cewa za ta iya faɗawa rikicin basasa. Ita kuma Turai ka iya taka wa Turkiyya birki wajen kai wa mayaƙan Kurdawa hari a Syria.
Netanyahu ya kafe cewa sojojinsa ba za su bar Gaza ba, inda ita kuma sharaɗin Hamas kenan idan dai ana son cimma batun tsagaita wuta.