Muller ya yi ban kwana da Bayern bayan kaka 25 a ƙungiyar

Thomas Mueller

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Thomas Muller ya yi ban kwana da Bayern Munich, bayan tashi wasan da ta doke Borussia Moenchengladbach 2-0 a Bundesliga ranar Asabar.

Mai shekara 37, ya yi kaka 25 a Bayern, wadda ya fara tun daga makarantar matasa, ya kuma lashe Bundesliga 13 da Champions League biyu a ƙungiyar.

Shi ne wasan karshe da Bayern ta buga a gida a bana, hakan ya sa Mueller ya yi ban kwana da magoya bayan ƙungiyar.

Cikin ban kwana da Bayern ta yi da Muller, an yi wa Allianz Arena ado da fulawoyi da kafa allon da ke ɗauke da hoton ɗan wasan da dukkan kofunan da ya lashe.

Muller, tsohon ɗan ƙwallon tawagar Jamus, ya buga wasa 750 a Bayern Munich.

Wasan karshe da ya rage a gaban Bayern Munich a Bundesliga a bana, shi ne za ta je Hoffenheim ranar Asabar 17 ga watan Mayu.

Bayern wadda ta lashe Bundesliga na 34 jimilla a makon jiya, ta fara cin ƙwallo ta hannun Harry Kane a minti na 31, kuma na 25 kenan a Bundesliga.

Daf da za a tashi daga karawar ce Bayern ta kara na biyu a raga ta hannun Michael Olise, hakan ya sa ta haɗa maki ukun da take bukata.

Harry Kane na daf da zama na farko da ya lashe takalmin zinare a yawan cin ƙwallaye kaka biyu a jere da ya fara buga gasar Bundesliga a tarihi.