Yadda sabon nau'in cutar Korona ya fara yaɗuwa a duniya

Asalin hoton, Getty
- Marubuci, Michelle Roberts
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan sashen lafiya na BBC
- Lokacin karatu: Minti 3
Mutane sun fara kamuwa da wani sabon nau'in cutar Korona da ake ganin cikin ƙanƙanin lokaci zai iya zama nau'in da ya fi yawa a duniya, a cewar masana kimiyya.
Nau'in cutar ya fara ɓulla ne a Jamus cikin watan Yuni.
Nau'in da aka yi wa laƙabi da XEC ya bayyana a Birtaniya da Amurka da Denmark da wasu ƙasashe da dama, in ji masu amfani da dandalin X, wanda aka fi sani da Twitter.
Sauye-sauyen da ke tattare da kwayoyin hallitar wannan nau'in na iya taimaka wa cutar ta yi matuƙar yaɗuwa a wannan kakar, kodayake ya kamata alluran rigakafi su taimaka wajen hana cutar yin tsanani idan har an kamu da ita, in ji masana.
Ga waɗanda suke da yiwuwar kamuwa da cutar korona mai tsanani, hukumar NHS na bayar da allurar ƙara ƙarfin rigakafinta kyauta.
An sake inganta alluran rigakafin domin su iya yaƙar sabbin nau'ukan cutar da suka ɓullo amma ban da nau'in XEC wanda ya samo asali daga nau'in Omicron.
Farfesa Francois Balloux, daraktan cibiyar binciken kwayoyin halitta a Kwalejin Jami'ar Landan ya shaida wa BBC cewa duk da cewa nau'in XEC na da "ƙananan hanyoyi ta fannin yaɗuwa" fiye da sauran nau'ukan Covid na baya-bayan nan, ya kamata alluran rigakafin su bayar da kariya.
Ya ce yana yiwuwa nau'in XEC ya zama nau'i mafi muni a lokacin hunturu.
'Samun ƙarin ƙarfi'
Daraktan cibiyar bincike ta Scripps, a California, Eric Topol ya ce nau'in XEC "yanzu ya fara".
"Kuma hakan zai ɗauki makonni da yawa, ko watanni ma, kafin ƙara ƙarfi kuma ya fara haifar da barazana," kamar yadda ya shiada wa jaridar LA Times.
"Tabbas XEC yana ƙara ƙarfi. Wannan ya tabbatar da shi a matsayin sabon nau'i na gaba. Amma zai ɗauki ƴan watanni kafin ya kai mataki mai muni."
Mene ne alamominsa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana tsammanin alamoninsa ba su bambanta da na mura ba kamar na nau'ukan da aka sani a baya:
- Matsanancin zafin jiki
- Ciwon jiki
- Gajiya
- Tari ko ciwon makogwaro
Yawancin mutane sukan samu sauƙi a cikin ƴan makonni da kamuwa da cutar korona amma yana iya ɗaukar lokaci mai tsawo kafin a gama murmurewa.
An samu yaɗuwar XEC a Denmark da Jamus, kamar yadda manazarcin bayanan cutar korona Mike Honey ya wallafa a dandalin X.
Akwai ƙarancin gwaje-gwaje na yau da kullum fiye da da, hakan ya sa da wahala a san asalin adadin waɗanda ke kamuwa da cutar korona a yanzu.
Hukumar Kula da Lafiya ta Burtaniya ta ce ba wani abin mamaki ba ne a ga cewa ƙwayoyin cuta suna sauyawa.
Mutanen da suka cancanci samun ƙarin alluran rigakafi na kyauta a Birtaniya sun haɗa da:
- Waɗanda ke da sama da shekaru 64 da haihuwa
- Waɗanda ke zama a gidajen kula da tsofaffi
- Waɗanda suka haura watanni shida kuma ke cikin haɗarin rashin lafiya
- Ma'aikatan hukumar NHS, da ma'aikatan gidajen kula da tsofaffi
Za a fara babban aikin rigakafin mura da Korona a watan Oktoba, kodayake wasu na iya samun allurar kafin wannan lokacin.
Dr Gayatri Amirthalingam, mataimakin darakta a hukumar kula da lafiya ta Burtaniya, ya ce: "Ba abin mamaki ba ne a ga ƙwayoyin cuta suna sauyawa. Hukumar kula da lafiya ta Birtaniya na ci gaba da sanya ido kan duk bayanan da ake samu da suka shafi nau'ukan cutar korona masu ɓullowa a cikin Birtaniya da ma duniya baki ɗaya, za kuma mu ci gaba da wallafa bayanan mu akai- akai.
"Allurar rigakafi ne ke bayar da mafi kyawun kariya daga rashin lafiya mai tsanani da ya jiɓanci korona, kuma muna kira ga waɗanda hukumar NHS ta tuntuba da su zo don karɓar rigakafinsu na wannan kakar."











