Rikici huɗu da suka sa ake yi wa Wike kallon mutum mai taƙaddama

Lokacin karatu: Minti 5

Kusan za a iya cewa a baya-bayan nan idan aka cire sunan Shugaba Tinubu wanda ke bakin al'ummar ƙasar sakamakon tsare-tsarensa, mutum na biyu wanda ake ta tattaunawa a kansa sannan da wuya gari ya waye babu labarinsa a jaridu, shi ne Barrister Nyesom Wike.

Nyesom Wike shi ne ministan babban birnin na Najeriya, Abuja a yanzu haka bayan da shugaba Tinubu ya naɗa shi sakamakon rawar da ya taka a nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zaɓen 2023, duk kuwa da cewa shi Wiken ɗan jam'iyyar PDP mai hamayya ne.

Nyesom wanda tsohon gwamnan jihar River ne ka iya zama mutum mafi janyo taƙaddama a daidai wannan lokaci wani abu da ya sa masu hamayya da shi da masu sharhi ke ganin cewa yana yin hakan ne saboda irin karɓuwar da ya samu a wurin shugaban.

Ga wasu rikice-rikice guda uku da Nyesom Wike ya zama shi ne a cikinsu tsundum.

Taƙaddamar haraji kan gidaje da filaye

A makon da ya ne ministan na Abuja, Nyesom Wike ya bai wa masu gidaje da filaye a Abuja da yawansu ya kai 4,794 wa'adin mako biyu da ko su biya haraji ko kuma su fuskanci tsattsauran hukunci.

Ministan ya ce sabon tsarin zai shafi masu filaye da gidaje da ke zaune a tsakiyar Abuja da aka nemi su biya naira miliyan biyar tare da sauran kuɗaɗen da ake bin su bashi a baya.

Sai kuma masu kadarori a Maitama da Asokoro da Wuse II da Guzape, su kuma za su biya harajin naira miliyan uku, yayin da masu filayen da ke Wuse II da Garki I da Garki II an dora mu su biyan naira miliyan biyu.

Kafin nan dai sai da ministan ya amince da ƙwace filayen wasu ɗaiɗaikun mutane a unguwar masu kuɗi ta Maitama da ke Abuja saboda rashin sabunta takardun mallakar filaye na tsawon shekaru.

Filayen da ministan ya ƙwace takardunsu sun haɗa da fili mallakin gidauniyar tsohon shugaban ƙasar, Muhamamdu Buhari wadda aka ce ana bin su bashin sama da naira biliyan ɗaya.

Ministan ya kuma ƙwace takardun mallakar wasu gine-gine bisa irin waɗannan dalilan da suka haɗa da sakatariyar jam'iyyar PDP da ya sa aka kulle suna tsaka da taro.

Hakan ne ya sa sanata mai wakiltar Abuja, Sanata Ireti Kingibe ta fara tanka wa ministan inda ta bayyana abin da ministan yake yi da abin da ya saɓa ƙa'idar doka da oda.

Rikicin shugabancin PDP

Nyeson Wike shi ne mutumin ɗaya tilo da kusan kowa ya buɗe baki zai magana kan rikicin da jam'iyyar PDP ke fuskanta, sunansa zai kama.

Rikici na baya-bayan nan shi ne wanda ya ɓarke tsakaninsa da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde wanda a baya tsohon abokinsa a wata ƙungiyar gwamnonin PDP da suka yi wa laƙani da G5 wadda ta taka rawa wajen kayar da jam'iyyar PDP a 2023.

Wike ya zargi Seyi Makinde da kitsa duk wani rikicin da jam'iyyar PDP ke ciki, inda ya ce suna ƙoƙarin sauya yarjejeniyar da aka yi ta zaman lafiya wadda ta amince da hukuncin kotun ƙoli na bar wa Senator Samuel Anyanwu maimakon Ude-Okoye.

Ana tsaka da wannan ne kuma ministan na Abuja ya bada umarnin kulle hedikwatar jam'iyyar PDP da ke Abuja suna gab da fara taron jam'iyya na majalisar zartarwa karo 99, abin da ya tilasta ƴaƴan jam'iyyar komawa tsohon ofishin PDP da ake kira Legacy House.

Tun farko dai sai da Nyesom Wike ya fara kwaso ta da Atiku Abubakar wanda ya lashe zaɓen cikin gida na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 da kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da ya ce sun ci amanarsa.

Ƴaƴan jam'iyyar PDP da dama na zargin shugaba Tinubu da amfani da ministan na Abuja wajen gadar da rashin zaman lafiya a jam'iyyar.

Rikicin jihar Rivers

Rikici tsakanin Nyesom Wike da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ne ya janyo har aka saka wa jihar dokar taɓaci kuma aka naɗa gwamnan riƙon ƙwarya har na tsawon watanni shida.

Rikicin siyasa ne dai ya ƙi, ya ƙi cinyewa a tsakanin Siminalayi Fubara da tsohon ubangidansa, ministan Abuja Nyesom Wike tun a shekarar 2023, inda suka fara rigima a kan jan ragamar jihar, lamarin da ya sa siyasar jihar ta ɗauki zafi, har ta zama abar kallo.

Lamarin ya ɗauki sabon salo ne lokacin da za a yi zaɓen ƙananan hukumon jihar, a 2024 inda ɓangaren Wike suka ce ba za a yi zaɓen ba, shi kuma ɓangaren gwamna Fubara suka ce babu gudu, ba ja da baya sai an yi, inda aka yi zaɓen, jam'iyyar APP wadda ake tunanin gwamna Fubara ya goyawa baya, ta lashe kujera 22 daga cikin ƙananan hukumomin jihar guda 23.

Ana tunanin gwamnan ya tsayar da ƴantakara ne a APP kasancewar tun a lokacin da aka gudanar da zaɓen shugabannin PDP na jihar Rivers an samu ɓaraka, inda tsagin Wike na PDP ya samu nasara a kan tsagin Fubara.

Haka kuma rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar, inda mafiya yawan majalisar, su 27 suke tare da da Wike, sauran kuma guda uku suke tare da gwamna.

A lokacin ne ƴanmajalisar na hannun damar Wike suka sanar da komawa APC, inda sauran ukun na gefen Fubara suka sanar da cewa guda 27 sun rasa kujerarsu, lamarin da aka je kotu har aka kotun ƙoli, wadda ta dawo musu da kujerarsu, sannan ta soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Rikicin Wike da Gwamnan Bayelsa

Tun bayan saka dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Riverssai rikicin kuma ya yi naso zuwa jihar Bayelsa mai maƙwabtaka.

A wannan karon ma, ministan Abuja kuma tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike, shi ne kan gaba a rikicin, wanda wani magoyin bayansa George Turnah ya nemi shirya gangamin nuna goyon baya ga ministan da kuma Shugaba Tinubu na jam'iyyar APC a jihar ta Bayelsa.

Sai dai tuni wata babbar kotun Bayelsa ta haramta yin taron bayan antoni janar na gwamnatin jihar ya kai ƙarar Mista Turnah da Wike, yana mai cewa hakan "zai iya tayar da fitina".

Rahotonni na cewa magoya bayan Wike na ci gaba da shirin gudanar da taron, lamarin da ya sa shugabancin jam'iyyar PDP na jihar suka shirya nasu taron makamancin na su Nyeso Wike a farfajiya ɗaya.