Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya yi saura ga jam'iyyar PDP bayan Wike da Makinde sun sanya zare?
Da alama jam'iyyar hamayya ta PDP na ƙara tsunduma cikin rikicin da ka iya yi mata illa a shirinta na tunkarar zaɓe mai zuwa a 2027, inda ƴaƴan jam'iyyar guda biyu Nyesom Wike, ministan babban birnin Najeriya da Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo suka sanya zare.
Nyesom WIke dai ya zargi Seyi Makinde da "lalata jam'iyyar" inda ya ce bai mutunta duk wasu yarjeniyoyin aka yi ba dangane da yadda za a warware taƙaddamar da jam'iyyar ke fama da ita a tsawon lokaci.
Nyesom Wike da Seyi Makinde sun kasance abokan tafiya a jam'iyyar PDP gabanin zaɓen 2023 lokacin da suka ja daga suka kafa ƙungiyar gwamnoni biyar da ake kira "G5" a lokacin Wike na gwamnan jihar Rivers, kuma suka yaƙi- ɗantakarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar tare da goyon bayan Bola Tinubu na jam'iyyar APC.
Kalaman Nyesom Wike
Ministan na Abuja, Nyesom Wike ya zargi gwamnan na jihar Oyo, Seyi Makinde da cewa shi ne ke kitsa duk wasu matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta a halin yanzu.
A ranar Lahadin nan ne ministan na Abuja, Nyesom Wike ya fitar da wata sanarwa mai taken "Rikicin PDP: Matsayata" inda ministan ya tsaya kai da fata kan wasu batutuwa da ya ce su ne asalin matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta.
"Sanata Samuel Anyanwu ne halastaccen sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa kamar yadda kotun ƙoli ta hukunta, dole ne lauyan jam'iyyar ya janye duk wasu batutuwan da suka jiɓanci jihar Rivers, da shari'a kan dokar taɓaci kuma dole ne kowa ya martaba yarjejeniyoyin da aka cimma:. In ji Nyesom.
Sai dai Wike ya kokwanta cewa " na sha mamaki yadda Seyi Makinde ya haɗa baki da Peter Mbah na Enugu suka kitsa taron shugabannin jihohin kudu maso Gabas inda suka cimma matsayar cewa idan dai ba a amince da Ude-Okoye ba a matsayin sakataren jam'iyyar PDP ba to za su bar jam'iyyar. Ni kuma na yi hira da ƴan jaridu cewa abin da suka cimma a Enugu ba zai yi tasiri ba."
Daga ƙarshe ministan na Abuja ya ce "ba zan bar wannan rashin adalcin ya ci gaba ba. Zan yi gwagwarmayar tabbatar da sauya wannan al'amari."
Me hakan ke nufi ga jam'iyyar PDP?
Malam Kabiru Sufi wanda masanin kimiyyar siyasa ne kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a, CAS Kano ya ce wannan rikici ne ba sabo ba sai dai kuma wannan ɗin ka iya ƙara tsunduma jam'iyyar cikin rikici.
"Za a iya cewa har yanzu jam'iyyar PDP ita ce ke biye wa jam'iyya mai mulki ta APC, to amma wannan rikicin ka iya sauko da jam'iyyar daga matsayin nata.
"Wannan ƙari ne a kan burin wasu ƴan jam'iyyar da ke shirin ficewa daga jam'iyyar domin yin haɗaka. Sannan akwai waɗanda za su jira har a yi zaɓen cikin gida kuma idan ba su yi nasara ba za su fice daga cikinta.
Saboda haka dole ne a warware wannan rikici tsakanin Wike da gwamnoni da ke zargin juna da shirin lalata jam'iyyar." In ji Malam Kabiru Sufi.
Asalin rikicin
An daɗe ana kai ruwa rana dangane da wane ne halastaccen sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa tsakanin Samuel Anyanwu da Udeh-Okoye.
Taƙaddamar da ke neman tarwatsa jam'iyyar ta tankarar da kotuna da dama ciki har da kotun ƙolin ƙasar.
Shi dai Samuel Anyanwu, ya sauka daga muƙamin ne domin tsayawa takara a zaɓen gwamnan jihar Enugu na ranar 11 ga watan Nuwamban 2023 ƙarƙashin jam'iyyar PDP to amma bai samu nasara ba bayan da sanata Hope Uzodinma na APC ya kayar da shi.
Sai dai Anyanwu bai miƙa takardar sauka daga kujerar sakataren jam'iyyar ba.
A wannan yanayin ne wata babbar kotu a Enugu a watan Oktoban 2023 ta bayar da umarnin maye gurbin Mista Anyanwu da Mista Ude-Okoye.
Bayan saɓata juyata a kotuna da dama, daga ƙarshe kotun ƙoli a ranar 21 ga watan Maris ta rushe hukunce-hukuncen bisa rashin ikon yin hakunci kan batun, wani abu da ya bai wa dukkannin ɓangarorin tunanin su ne suke da nasara.
Nyesom Wike na goyon bayan sanata Samuel Anyanwu, inda su kuma gwamnoni da jaga-jigan jam'iyyar PDP a kudu maso Gabas ke tare da Ude-Okoye.