Al'ummar Birtaniya na kaɗa ƙuri'a a babban zaɓen ƙasar

An bude rumfunan zaɓe a babban zaben Birtaniya,, inda miliyoyin masu kaɗa ƙuri'a ke shirin zabar 'yan majalisa, da kuma sabon Firaiminista.
Dole ne masu zaɓe su gabatar da katinsu na shaida kafin kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓe.
Za a rumfe rumfunan ne da karfe 10 na dare agogon ƙasar da kuma na Najeriya, inda a lokacin ne kuma ake sa ran sakin sakamakon farko.
BBC ba ta da damar kawo muku rahotannin yaƙin neman zaɓe ko na siyasa da suka danganci zaɓen yayin da ake gudanar da shi, to amma za mu rika kawo muku bayanai daga rumfunan zaɓen da kuma yadda abubuwa ke gudana.
Wannan dai shi ne karon farko da al’ummar Birtaniya za su nuna wata shaida kafin su zaɓi wanda suke so.
Da dama daga cikin ƴan ƙasar sun kaɗa kuri’un su ta akwatun gidan waya.
Zaɓen zai kasance wani babban ci gaba a ƙasar.
Babu dai wata jam’iyya da ta taba cin zabe a kasar sau biyar a jere, wanda hakan shi ne tsagwaran gaskiya, da ke ci gaba da zama barazana ga Rishi Sunak.
Haka kuma babban ƙalubale ne ga shi ma ɗan takara Labour Sir Keir Starmer, kasancewar jam’iyyar sa shekarunta 19 rabon ta da ta ci zaɓe.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, PA Media











