Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Salah ba ya son barin Liverpool, Man Utd na son sayar da Onana
Ɗanwasan gaba na Masar Mohamed Salah mai shekara 33 na son ya ci gaba da taka leda a Liverpool har zuwa kakar baɗi da yarjejeniyarsa za ta kawo ƙarshe, idan har bai samu yadda yake so ba a Saudiyya da ake zawarcinsa. (Football Insider)
Arsenal da Liverpool da Manchester City da Newcastle da Brighton da Brentford, na hamayya kan ɗanwasan baya na Jamus da Eintracht Frankfurt Nnamdi Collins (Teamtalk)
Ɗanwasan tsakiya na Manchester United da Brazil Casemiro, mai shekara 34, na son ci gaba da murza leda a Turai idan har kwangilar shi ta kawo ƙarshe a Old Trafford a wannan bazara. (Sun)
Manchester United na son sayar da golan Kamaru Andre Onana, mai shekara 29 a wannan bazara. (Talksport)
Sai dai Onana na son dawo da ganiyarsa domin zama zaɓin farko a tsaron ragar Manchester United idan ya dawo daga Trabzonspor da ya tafi a matsayin aro. (Guardian)
Arsenal da Liverpool da Manchester United na sa ido kan matashin ɗanwasan tsakiya na Ajax Sean Steur. (Teamtalk)
Manchester United har yanzu ba ta fara tattaunawa ba da ɗanwasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20. (Sun)
Ƙungiyar Orlando City ta Amurka ta yi wa Antoine Griezmann tayin yarjejeniyar shekara uku kuma zai tattauna da ƙungiyarsa Atletico Madrid kafin amincewa da tayin. (Fabrizio Romano)
Darajar Victor Osimhen ta lunka tun bayan da ɗanwasan gaban na Najeriya ya koma Galatasaray daga Napoli, a cewar maitaimakin shugaban gasar Lig din Turkiya Abdullah Kavukcu. (Goal)