Matsalolin da ke janyo rufe gidajen mai a Najeriya

Asalin hoton, OTHER
A Najeriya, ƙungiyar dillalan mai da iskar gas ta arewacin ƙasar, wato Arewa Oil and Gas Marketers Association, ta ce wasu manyan matsaloli ne suke janyo ake gani ana ƙaurace wa depo-depo da kuma rufe wasu daga cikin gidajen man ƙasar.
Cikin wata hira da BBC, shugaban ƙungiyar Bashir Ahmad Dan-mallam, ya ce ba wai kaya ba ne babu dalilai ne kusan guda uku.
Ya ce,“ Wadannan dalilai na da alaƙa da kawo man, wato tun daga siyansa da kuɗin motar da ake biya idan an ɗauko man zuwa inda ake so a kai shi ga kuma kuɗin lodi, to idan aka zo aka lissafa sai a ga a kan yadda ya kamata a sayar da shi babu riba kwata-kwata.“
Bashir Dan-mallam, ya ce wannan ne dalilin da ya sa wasu masu gidajen ke rufewa wasu kuma ke ɗan ƙara kuɗin man.
Ya ce, "Baya ga wannan matsala, akwai kuma batun kuɗin da kamfanin NNPCL ya bayar masu yawa domin a yi gyaran hanya, to amma masu wannan aiki ba sa yi, idan an taɓa su sai su ce ai damuna ce, to rashin gyara hanyar na janyo idan ka ɗauko mai sai ka shafe kwanaki masu yawa kafin manka ya isa inda ake so saboda rashin kyawun hanya."
Shugaban ƙungiyar dillalan mai da iskar gas ta arewacin Najeriyar, ya ce matsala ta uku kuma ita ce, "Yadda kuɗaɗen al’umma suke a wajen hukumar Petroleum Equlization Fund, wadda akwai biliyoyin kuɗaɗen mutane a hannunta don juyawa wasu kuma bankuna ne suka karɓa, to kuɗaɗen na nan a hannu."
Ya ce, to waɗannan su ne matsalolin da ya sa a yanzu wasu masu gidajen mai ko su sayar da man da tsada ya koma naira 700, ko kuma a rufe gidajen man ta yadda za a fara ganin layukan motoci a gidajen mai kuma.
Bashir Dan-mallam, ya ce a yanzu haka akwai mai a depo-depo din da ke Legas da Warri da Kalaba da kuma Fatakwal, kawo man ne ke da wahala.
Shugaban ƙungiyar dillalan man, ya ce, "Idan har ana so abubuwa su daidaita dole a ɗauki matakai kamar, amfani da batun cire VAT a tabbata ana aiki da shi, sannan maganar NIMASA da NPA da suke karɓar kuɗaɗen da ake ba su da dala, su dawo su rinƙa karɓa da naira don dala hauhawa take yi, sannan kuma abu na ƙarshe ministan ayyuka ya tabbata an gyara hanyar da ake bi wajen shigo da man."
Ya ce, idan har gwamnati ta jajirce a kan waɗannan matakai to mai zai yi sauki, amma idan har aka samu akasin haka to farashin mai sai yadda hali ya yiwu.











