Yadda Tinubu ya zame a Eagles Square a ƙoƙarinsa na hawa mota

Tinubu

Asalin hoton, Tinubu/X

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu "yana cikin ƙoshin lafiya bayan faɗuwa da ya yi kafin jami'an da ke tare da shi su tallafo shi" sakamakon zamewa lokacin hawa mota, akmar yadda jami'an gwamnati suka ce.

Bola Tinubu mai shekaru 72, dai na ƙoƙarin hawa mota ƙirar a-kori-kura wadda za ta zagaya da shi a dandalin Eagles Square inda ake taron ranar dimokaraɗiyya, sai ya zame.

Mataimakin Shugaba Tinubu na musamman kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya ce " ƴar ƙaramar zamiya ce. Kuma dandanan (Tinubu) ya miƙe ya ci gaba da zagaya dandalin da ake bikin. Babu wata matsala."

Daga bisani an ci gaba da fareti inda shugaban ya tsaya a cikin motar yana gaisawa da jama'a.

Atiku ya jajanta wa Tinubu

Mutumin da shugaba Tinubun ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da "zamewar" da ya yi.

"Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyar lau."

A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Ƴan Najeriya na tattauna batun a soshiyal midiya

Tuni dai ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta ke ta tattauna batun tare da mayar da martani kamar haka:

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Larabar nan, 12 ga watan Yuni ce ranar da 'yan Najeriya ke murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya a kasar, da aka fi sani da June 12.

Wannan rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ne aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, wanda ake kallo a matsayin mafi tsarki, ko da yake a zahiri ya bar baya da ƙura.

Tsohuwar gwamnatin ƙasar ta shugaba Muhammadu Buhari ce ta sauya ranar, daga 29 ga watan Mayu, ranar da aka fara gudanar da mulkin farar hula zuwa 12 ga watan Yuni, ranar da aka gudanar da zaben na 1993.

Albarkacin wannan rana gwamnati ta ayyana Larabar nan a matsayin ranar hutu, don gudanar da bukukuwa, kana shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar wa yan kasar jawabi na musamman.