Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Al'adar hawan kaho na fuskantar barazana a Faransa
Wasan hawan kaho wanda aka shigar daga Sifaniya a karni na 19 har yanzu yana da farin-jini sosai a yawancin sassan kasar ta Faransa.
Yanzu dai a karon farko shawarar haramta wasan wanda ake kira ‘’corrida‘‘ ta kai ga zauren majalisar dokokin kasar – wanda hakan wata alama ce da ke nuna nasara ga masu rajin kare hakkin dabbobi.
Duk da haka bukatar wadda hadakar jam’iyyu masu ra’ayin kawo sauyi ta Nupes ta gabatar na da gagarumin aiki a gaba na samun karbuwa.
Ita dai gwamnati a hukumance tana adawa da haramcin yayin da su kuwa ‘yan majalisar dokokin da ke goyon bayan wasan suka yi alkawarin kawar da maganar tattaunawa kan batun daga majalisar.
Duk da cewa da dama daga cikin ‘yan jam’iyyar Shugaba Emmanuel Macron su da kansu suna son a haramta to amma kuma fadar gwamnatin kasar, Élysée Palace na dari-darin hanawa.
Saboda gwamnatin na fargabar matakin zai kara haddasa sabani tsakanin birane da kauyuka da kuma tsakanin Paris da yankuna.
Aymeric Caron, tsohon mai gabatar da shirin talabijin wanda ya kirkiro jam’iyyar masu kare hakkin dabbobi kuma ya ci kujerar majalisar dokokin kasar a shekarar nan shi ne ya rubuta kudurin dokar neman haramcin.
Kudurin dokar ya kunshi cewa kamar yadda wani kwamitin majalisar kan dabbobi ya rubuta, wasan hawan kaho domin nishadi wanda hakan ke kaiwa ga rauni da ma mutuwar dabbobin ya saba ta ko’ina da akidar kare hakkin dabbobi da jin dadinsu.
Haka kuma masu goyon bayan haramcin sun nuna cewa sama da kashi 80 cikin dari na Faransawa na sona kawo karshen wasan wanda ke kaiwa ga mutuwar dabobobin.
Suka ce hatta a garuruwan da ake yin wasan masu son a hana sun kai kashi 61 cikin dari.
Dokar 1951 ce ta bayar da damar wasan na Corridas, wadda kuma ta ware yankuna daga batun dokar kasa ta hana azabtar da dabbobi.
Hakan na nufin ke nan a yankuna inda ake da damar ci gaba da al’adar wasan musamman ma yankunan Nîmes zuwa Bayonne – akwai damar wasan ya ci gaba.
To amma daya daga cikin dalilan da ake bayarwa na neman haramtawar shi ne cewa wasan na hawan kaho irin na Sifaniya ba tsohuwar al’ada ba ce ta Faransa sam-sam, domin a cewarsu an bullo da shi ne a 1853 domin jin dadin matar Sarkin Sarakuna Napoleon III, Eugénie, wadda ‘yar Sifaniya ce.
Masu kare al’adar wasan a Faransa sun yi wasan domin kara nuna yadda yake a karshen makon da ya gabata a yawancin yankuna 45 da wasan ya yi fice.
Maganar da suke yi ita ce cewa wasan al’ada ce ta mutanen karkara kuma hana ta tamkar take hakkin al’ada ne da kuma barazana ga ayyukan wasu.
A wajensu Aymeric Caron, na zaman irin mutanen birni ne masu al’ada ta daban da kauye, wanda kuma suke ki.
Haka kuma masu goyon bayan wasan sun nuna yadda za a ce al’ummar da ke kin noma kamfani da samar da nama mai yawa, amma kuma ba za ta iya boye kinta ga mutuwar shanun hawan kaho ba a fili, wadanda kuma aka kiwa ta su a cikin ‘yanci ba.
Masu adawa da wasan dai sun yi karfi a yanzu sabanin a baya inda bukatar tasu to majalisa ba ta iya kaiwa.
Hadakar da ke da mambobi 131 na amfani da ranar ‘yan hamayya a majalisar ta gabatar da kudurorin doka da dama ciki har da na neman hana wasan hawan kahoton.
Wannan yunkuri na ‘yan hamayya na da damar samun nasara kasancewar jam’iyyar Shugaba Macron ta Renaissance da magoya bayanta ba su da rinjaye a majalisa.
Sai dai kuma kan dukkanin jam’iyyun ya rabu dangane da kudurin.
Ita dai wannan al’ada ta wasan hawan kaho aba ce da aka hana yankin arewa maso gabas na Sifaniyar wato Catalonia.
Haka ma kuma a wasu jihohin Mexico da kasashe da dama a Latin Amurka, amma kuma har yanzu ba a haramta shi ba a wasu wuraren a Sifaniya da Portugal da
Colombia da Ecuador da kuma Bolivia.