Hotunan yadda ake alhinin rasuwar Fafaroma Francis

Lokacin karatu: Minti 2

Fafaroma Francis, na farko daga nahiyar Amurka ta kudu ya rasu a ranar Litinin, sa'ilin da ake bikin Easter yana da shekara 88.

Wata mata na zubar da hawaye yayin da mabiya ɗariƙar Katolika ke taruwa a cocin Redeemer Church da ke birnin Bangkok na ƙasar Thailand a yau Litinin bayan samun labarin rasuwar Fafaroma Francis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata na zubar da hawaye yayin da mabiya ɗariƙar Katolika ke taruwa a cocin Redeemer Church da ke birnin Bangkok na ƙasar Thailand a yau Litinin bayan samun labarin rasuwar Fafaroma Francis

Ya rasu ne a gidansa na Casa Santa Marta da ke Vatican bayan fama da cutar sanyin haƙarƙari wadda ta shafi huhunsa na hagu da dama.

Haka nan fafaroman ya yi fama da sauran wasu cututtuka.

Wata hadimar coci na yi wa Fafaroma addu'a a cocin St Patrick da ke birnin New York na ƙasar Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata hadimar coci na yi wa Fafaroma addu'a a cocin St Patrick da ke birnin New York na ƙasar Amurka.

Rasuwarsa ta kawo ƙarshen shekara 12 da ya kwashe kan muƙamin, inda aka shaide shi da ƙoƙarin kawo sauyi a cocin.

Malaman addinin kirista na ci gaba da addu'o'i a dandalin St Peter da ke Vatican bayan ɓullar labarin rasuwar Fafaroma Francis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Malaman addinin kirista na ci gaba da addu'o'i a dandalin St Peter da ke Vatican bayan ɓullar labarin rasuwar Fafaroma Francis

An san shi da ƙoƙarin neman ƴanci ga mutanen da aka tauye wa hakki, da ƙoƙarin samar da haɗin kai tsakanin al'umma.

Wani mutum riƙe da fure tsaye a dandalin St Peter da ke Vatican yana alhinin rasuwar Fafaroma Francis a yau Litinin 21 ga watan Afurilun 2025

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum riƙe da fure tsaye a dandalin St Peter da ke Vatican yana alhinin rasuwar Fafaroma Francis a yau Litinin 21 ga watan Afurilun 2025
A birnin Manilla na ƙasar Philippines an ajiye hoton Fafaroma Francis a dandamalin cocin Minor Basilica yayin da mutane ke zuwa suna masa addu'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A birnin Manilla na ƙasar Philippines an ajiye hoton Fafaroma Francis a dandamalin cocin Minor Basilica yayin da mutane ke zuwa suna masa addu'a