Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan yadda ake alhinin rasuwar Fafaroma Francis
Lokacin karatu: Minti 2
Fafaroma Francis, na farko daga nahiyar Amurka ta kudu ya rasu a ranar Litinin, sa'ilin da ake bikin Easter yana da shekara 88.
Ya rasu ne a gidansa na Casa Santa Marta da ke Vatican bayan fama da cutar sanyin haƙarƙari wadda ta shafi huhunsa na hagu da dama.
Haka nan fafaroman ya yi fama da sauran wasu cututtuka.
Rasuwarsa ta kawo ƙarshen shekara 12 da ya kwashe kan muƙamin, inda aka shaide shi da ƙoƙarin kawo sauyi a cocin.
An san shi da ƙoƙarin neman ƴanci ga mutanen da aka tauye wa hakki, da ƙoƙarin samar da haɗin kai tsakanin al'umma.