Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Sun kashe majinyata da ke kwance a gadon asibiti' - BBC ta ji abin da ya faru a Suweida
- Marubuci, Jon Donnison
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, in Suweida City, Syria
- Lokacin karatu: Minti 3
An zargi dakarun gwamnatin Syria da yin kisan kiyashi a wani asibiti yayin rikicin kabilancin da ya ɓarke sama da mako guda da ya wuce.
BBC ta ziyarci Babban Asibitin Kasa na Suweida, inda ma'aikatan asibitin suka yi ikirarin an kashe marasa lafiya a kan gadajensu.
Gargadi: Wannan labarin na kunshe da bayanan tashin hankali
Warin ya buge ni kafin komai.
A filin ajiye motoci na babban asibitin birnin Suweida, gomman gawarwakin da suka fara zagwanyewa ne aka jera a cikin ledojin nannaɗe gawa.
Wasu a bude suke, kuma ana ganin alamun rauni a jikin mutanen da aka kashe a nan.
Inda nake takawa na da santsi saboda jini da ya yi faca-faca.
A cikin zafin rana, ɗoyin na ƙara ƙamari.
"Kisan kiyashi ne," kamar yadda Dr Wissam Massoud, wani likita a asibitin ya faɗa min.
"Sojojin sun zo nan suna cewa suna son kawo kwanciyar hankali, amma sun kashe mutane da dama, daga masu karancin shekaru zuwa tsofaffi sosai."
Cikin makon nan, Dr Massoud ya aiko min wani bidiyo da ya ce ya nuna yanayin wani hari da gwamnatin ta kai.
A cikin bidiyon, wata mata ce ta zagaya tana nuna harabar asibitin. Kwance a kasa cikin asibitin gawarwakin mutanen da suka mutu ne aka naɗe da zanin gado.
Kowa a nan, likitoci da ma'aiktan jinya, da kuma yan sa-kai na faɗin abu daya.
Cewa ranar Laraba da ta wuce, dakarun Syria ne da ke harin yan addinin Druze suka shigo asibitin tare da yin kashe-kashen.
Kiness Abu Motab, wani ma'aikacin sa-kai a asibitin ya yi tambaya a kan mutanen: "Mene ne laifinsu? Kawai saboda daga kabila mara rinjaye suke a kasar da ke dimokuraɗiyya?"
"Masu laifi ne. Miyagun mutane. Ba mu yarda da su ba gaba daya," Osama Malak, wanda malamin Turanci ne ya fada min a wajen kofar asibitin.
"Sun harbi yaro dan shekara takwas da ke da nakasa a kai," ya kara.
"A dokar kasa da kasa, ya kamata a kare asibitoci. Amma sai suka kawo mana hari a cikin asibitocin ma.
"Sun shiga asibitin. Suka fara harbin kowa. Sun harbe marasa lafiya a kan gadajensu yayin da suke bacci."
Dukkanin bangarorin da ke rikicin na zargin juna da aikata laifuka.
An zargi mayakan Bedouin da na Druze, da kuma sojojin Syria da kashe fararen hula.
Babu cikakken bayani game da abin da ya faru a asibitin. Wasu na kiyasin mutanen da aka kashe a Larabar da ta wuce sun zarce 300, amma ba a tabbatar da hakan ba.
A daren Talata Ma'aikatar tsaron Syria ta ce tana sane da rahotannin "wuce ka'ida" da mutane masu sanye da kayan soji suka yi a birnin Suweida da ke da rinjayen mabiya Druze.
Cikin makon nan, Ministan kai daukin gaggawa a lokacin bala'o'i ya fada min cewa za a bincika dukkanin zarge-zargen miyagun laifuka da ake zargin dukkanin bangarorin da aikatawa.
An takaita shiga garin Suweida sosai, wato samun shaidar ta hanayr gani da ido na da matukar wahala.
Garin na karkashin wani takunkumi a yanzu, dakarun gwamnatin Syria na kayyade wadanda za su shiga ko su fita.
Domin shiga, sai da muka wuce shingaye da dama.
Da kuma muka shiga garin, mun wuce shaguna da gine-ginen da aka kona, da kuma motocin da tankoki suka take.
Da alamun an yi kazamin yaki tsakanin mayakan Druze da na Bedouin.
A wannan matakin ne gwamnatin Syria ta shigo ta yi kokarin ganin an tsagaita wuta.
Duk da cewa dakarun gwamnatin Syria sun samu iko da kauyukan Druze da dama a yankin Suweida, birnin Suweida, wanda ke da mutane 70,000, na karkashin ikon yan Druze.
Kafin mu tafi, mun samu Hala al-Khatib zaune a benci da gwaggonta.
Fuskar Hala ta yi jina-jina. Kamar ta rasa ido daya.
Ta fada mana cewa yan bindiga sun shigo sun harbe ta a kai yayin da take boye a gida.
Hala ba ta san makomarta ba tukunna, to amma iyayenta sun mutu.