Yan wasan da United za ta tsawaita zamansu a Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta shirya tsawaita zaman wasu yan wasanta da suka hada da Marcus Rahsford na Ingila.
Kungiyar ta Old Trafford na kuma kan tattaunawa da David de Gea, wanda kwantiraginsa ke karewa a karshen kakar da ake ciki.
A makon da ya gabata, koci Erik ten Hag yace United za ta duba yiwuwar tsawaita zaman Rashford da Luke Shaw, da Diogo Dalot da kuma Fred.
Duka yan wasan hudu na da damar barin kungiyar a watan Yuni idan ba a kulla sabuwar yarjejeniya da su ba.
Sai dai yarjejeniyar De Gea ta dan fi tsauri a kan ta saura, don dama yana kan kwantiragin da yake karbar fam dubu 375 a duk mako tun daga 2019.
Tun a lokacin ne ya zama golan mafi tsada a duniya.
Sai dai ga alama da wahala Man United ta bai wa mai tsaron ragar dan shekaru 32 kwantiragi mai tsawo a wannan karon.
Kuma idan har aka kai 1 ga watan Janairu ba bu wata matsaya tsakanin United da De Gea, to kuwa golan, wanda ya zama mutum na 11 da ya buga wa kungiyar wasanni 500 a tarihi, zai iya kama gabansa zuwa wata kungiya daban.











