Ba bu wani dan wasa da ya kama kafar Pele- Oliseh

Pele

Asalin hoton, OTHER

Tsohon kyaftin din Super Eagles Sunday Oliseh, ya ce daga Lionel Messi har Cristiano Ronaldo, babu wanda ya yi abunda za a kira shi dan wasan da ba a taba irinsa ba a duniya.

A maimakon haka Oliseh ya ce yana da yakinin cewa tun daga Diego Maradona har Messi da Ronaldo, babu wanda ya kamo Pele a matsayin shahararren dan kwallo da duniya ta taba gani.

Baya ga lashe kofin duniya sau uku a zamaninsa, Pele na Brazil ya zamo allon kwaikwayo ga matasan yan kwallon da suka yi nasara a wannan zamani.

Oliseh

Asalin hoton, OTHER

Da aka tambaye shi ko wa yake gani a matsayin dan kwallon da ba bu irinsa a duniya? Oliseh bai bata lokaci ba ya kada baki yace '' sunan shi Pele.''

'' Shi ne dan wasan da duniya ba ta taba ganin irinsa ba har yanzu. Ba zai yiwu ka lashe kofin duniya ba har sau uku, a ce ga wani yana gasa da kai.''

''Na san wasu musamman matasa, ba za su ji dadin zabi na ba, amma ire-ire na da muka girme su mun san ko wane ne shi.'' In ji Oliseh.

To amma dan wasan gaban PSG Lionel Messi, ya nuna kansa a matsayin daya daga cikin shahararrun yan kwallo a duniya, bayan da ya taimaka wa kasarsa Argentina lashe kofin duniya na 2022 a Qatar.